← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 78

Sashe 32

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a babu wata É—awainiya" ta yi maganar tana fita waje.
Ta so tambayar Nana me ya kawo ta Nijar, ga tsohon ciki, kuma ta ce ba ta da kowa, amma ta kasa saboda wani irin kwarjini da Nanan ta yi mata.
Tun da ta bawa Nana abincin safe, da rana ta bata fura Nana take amai. Har sai da Hajara ta ji babu daÉ—i, ta yi zaton ko Abincinta ne ya saka Nana amai.
A sanyaye ta ce "Ko Abincin nawa ne ya saka ki amai?"

Nana ta yi murmushi ta ce "A'a kar ki damu, dama haka nake fama tun farkon cikin, ni na riga na saba ma"

"Kayya ai ba a sabo da wahala, kin yi amai ya kusa goma, ko Asibiti zamu je?"

"A'a zan daina in sha Allah"

Gaba É—aya Hajara ta damu, ganin yanayin da Nana take ciki.

Nana ta ce "Ba ki taɓa haihuwa ba ne? In dai mutum ya haihu ya san irin wannan larurar ta ciki ai"

Hajara ta ce "Ina fa? Watanmu takwas da aure, ban haihu ba".
Nana ta yi murmushi ta ce "Allah ya kawo mai albarka"
"To ai ni duk na tsorata ne, wannan aman ya yi yawa"
"Ai ni na riga na saba ma, ba ya damuna yanzu" haka suka ɗan din ga taɓa hira.

Mijin Hajara bai dawo ba sai isa'i, Nana na ɗaki tana shafa'i da wuturi. Ya ce wa Hajara "Ina baƙuwarmu?"

"Tana nan sai dai ba ta da lafiya"

"Me ya same ta?"

"Wallahi tun da na ba ta Abinci take amai, haryanzu jikina duk ya yi sanyi"

Ya ce "Subhanallah, kuma bai tsaya ba?"

"Tana dai ta yi"

Nana ta idar ta yi addu'a, sannan ta fito, ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa yana yi mata ya jiki.
Ta ce "Jiki Alhamdillah"

Ya ce "Baiwar Allah ba a samu gidan haya ba, duk inda na tambaya, sai masu tsada, kuma babu lallai a bayar, mussaman idan aka san ke kaÉ—ai za ki zauna, kuma zaman ki ke kaÉ—ai babu Namiji babu tsaro ko kaÉ—an.
Amma na kuma bayar da cigiya ko za a samu wani, wanda yake da mutane a ciki sai a kama"

Nana ta jinjina kai ta ce "Na saku É—awainiya, Allah ya saka da alkhairi"

Ya ce "Ba komai" ya kalli Hajara ya ce "Bari na je na dawo, ko za ku yi hira kar na takura muku"

Nana ta ce "A'a ba komai, ka zauna ni sai na koma É—aki"

Ya ce "A'a dama zan fitan"

Hajara ta raka shi soro, ta tsaya can su na hira Nana tana jiyo dariyar su. Sayyid ya faÉ—o mata a rai. Yana daga cikin manyan ni'imomi da nasarorin rayuwa, mutum ya auri wanda yake son sa, ya kuma dace da shi. Ta yi musu addu'a da fatan samun dauwamammen zaman lafiya da kuma zuriya ta gari masu albarka.
Hajara ta dawo, ta zauna su ka ci gaba da ɗan taɓa hira da Nana.
Ta cewa Nana "Ko sunanki ban sani ba"
"Nana Asma'u, amma Nana ake ce mini"
Ta ce "Allah sarki, amma ki na da aure ne?"
Nana ta yi murmushi, ta ce "Kin yi mamakin yadda na taho inda ban san kowa ba ga tsohon ciki ko? Na san wataƙila, kina tunanin ina na samo ciki ne?"

Hajara ta ce "Laaa a'a wallahi"

Nana ta ce "Ai babu damuwa idan ma kin yi tunanin haka, ɗabi'ar zuciya ce. Matar aure ce ni, ko a yanzu haka ka ma ina da igiyoyin aure uku a kaina, wani dalili ne ya kawo ni ƙasar nan, kuma in sha Allah da na kammala, zan koma gida"

"Allah sarki, Allah ya tabattar da alkhairi, ya sanya a samu abin da aka zo nema"

Nana ta amsa da "Amin na gode sosai"

*****

Su na zaune sun tattara hankalinsu a kan likitan, cikin matsananciyar girmamawa Likitan ya gaishe su.

"Ya ya jikin Imam?"

Ya amsa da "Jikinsa Alhamdillah, yana samun sauƙi sosai da sosai"

"Ba yana samun sauƙi muke son ji ba, mene ne sakamakon binciken ku da aka gudanar?"

Likitan ya ce "Eh sakamakon gwaje-gwaje, ya nuna babu abin da aka yi masa na cutarwa a jikinsa, gaba É—aya babu wani abu na cutarwa a tare da shi"

"Shi kuma matsalar zuciyar fa?"

"Wannan yana da nasaba da hawan jini da yake da shi tuntuni, wataƙila ya daɗe ba a kan magani ba. Shi yasa ya shafi zuciyarsa. Sai dai matsala ɗaya"

Cikin damuwa dattijon ya ce "Wace matsalar?"

"Ƙwaƙwalwarsa, mun kasa gano abin da yake faruwa da ƙwaƙwalwarsa, haryanzu bai samu nutsuwar da zamu tattauna da shi ba, yana buƙatar kulawa ta musamman a bangaren ƙwaƙwalwa"

Sultan ya dafe goshinsa, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, idanunsa suka yi jawur. Ya ɗago ya kalli Likitan ya ce "Ko gida za a mayar da shi, a saka duk abin da ake buƙata na kula da shi a ɗakin, ya zamana yana kusa da ni, hankalina ba ya kwanciya, yana nan ina can"

Abduou ya ce "A'a Sultan, idan aka mayar da shi gida, za a iya gane halin da yake ciki, wanda ba ma fatan hakan, dole a ci gaba da toshe duk wata kafa da za a san halin da yake ciki, har zuwa lokacin da zai warware. Kuma za a ci gaba da matsa yaran can, har sai ya yi mana bayanin abin da suka yi masa a Nigeria. Kuma Asibitin nan akwai tsaro babu wanda ya san yana nan. A kula da shi har zuwa lokacin da za a yi tafiyar"

Sultan ya yi ajiyar zuciya cike da gamsuwa, ya miƙe tsaye ya ce "Mu je na gan shi"

Su ka miƙe gaba ɗaya, Likitan yana gaba su na biye da shi a baya.
Cikin sauri suka ƙarasa gaban gadon. Idanunsa a rufe yana bacci.
Sultan ya ƙarasa gaban gadon, fuskarsa ɗauke da damuwa.
Ya din ga dudduba jikinsa, tamkar yana son gano wani abin. Ya kalli Likitan ya ce "Kun tabattar a jikinsa babu wani abu na illa ko cutarwa a tattare da shi?"

"Babu ranka ya daɗe, lafiya kalau yake, ba a yi masa komai ba, sai wannan matsalar ta ƙwaƙwalwarsa. Ba na tunanin an tafi da shi Nigeria ne dan a cutar da shi, akwai dai wani abu...

"Ya isa ba kai ke hurumin zartar da wannan hukuncin ba, sai abin da bincike ya tabattar"
Babu shiri likitan ya ja bakinsa ya tsuke.

Sultan ya É—ago hannun Imam na hagu, ya kalli yatsunsa ya ga yatsunsa biyu sanye da zobuna, ya É—ago hannun damansa, ya ga babu azurfa É—aya sai É—aya. Cikin tashin hankali ya ce "Abduou. Babu zoben Imam guda É—aya" Cikin sauri Abdou ya ce "Wanne daga ciki?" Ya É—ago wa Abdou hannun Imam.
A rikice Abduou ya kama hannunsa ya duba, ya kalli Sultan ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga abin da nake gaya maka ko? Kai ne ka ke ƙoƙarin kare yaron can, ka ke cewa a bi shi a sannu ba ka tunanin zai iya cutar da shi, to ga shi nan ai ga irinta nan, tabbas ya san inda zoben nan yake, dole a matsa shi a fito da shi. Dalilin da ya sanya su ka sace shi kenan ma, su ka bar ƙasar nan da shi, su ka kai Nigeria. Zoben suke so su sace"
Sultan ya dafe kansa, ya rasa abin da yake yi masa daÉ—i.
"Sultan wannan ma wani sabon sirri ne, da yake buƙatar duk tsanani a rufa shi, a ci gaba da addu'a, amma dole a nemo zoben nan, idan ba haka ba zai fita daga sahun Imams"
Sultan ya sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya yana kallon yadda yake bacci a kan gadon.

****
Sai da Nana ta shafe kwanaki huɗu a gidan Hajara, ba a samu inda za ta zauna ba. Nana ma abin daya dame ta, sai ɗawaniya suke faman yi da ita, ga shi tana tsoron kar su ƙosa da ita, dan babu mai jurewa yau da kullum sai Ubangijin da ya halicci bawa.
Ranar kwana na huÉ—u da yamma mai gidan ya dawo, Hajara ta kira Nana.

Bayan sun sake gaisawa ya ce "Malama Nana, wallahi ba a samu gida ba, sai dai ina tafe a hanya wata shawara ta faÉ—o mini. Akwai wata 'yar uwar Babana a can wata unguwa, itakaÉ—ai take zaune a gidanta, kuma akwai É—akuna a gida, kuma ba mazauniya ba ce, tana fita sana'iinta. Sai dai fa mace mafaÉ—aciya, tana da yawan faÉ—a, ba wuya ta hasala. Ban sani ba ko za ki iya zama da ita?"

Cikin farin ciki Nana ta ce "Zan iya zama da ita, in dai ta amince"

"A'a dai ki yi tunani, mafaÉ—aciya ce sosai, idan kin amince zan tafi na je na same ta a daren nan, na yi mata bayani"

Nana ta ce "Wallahi kar ka damu, zan iya zama da ita"

Ya ce "To Allah ya sa, zan ne yi mata magana, idan ya so ko kuÉ—in hayar ne ita sai a bata" Nana ta yi ta masa godiya tana murna.

Har Nana ta yi bacci bai dawo ba, sai washegari da safe, bayan ta karya,  Hajara ta cewa Nana ta shirya, za su tafi can gidan matar.
Nana ta yi wanka ta shirya, suka fita suka hau abin hawa.
Hajara ta ce "Nana kamar kar ki tafi, kwana biyun nan har na saba da ke"

Nana ta yi murmushi ta ce "Nima haka, sai dai har Abada ba zan taɓa daina yi muku godiya da fatan Alkhairi, ba dan ba ƙaramin jihadi ku ka yi ba, ne ceton rayuwata"

"Ba komai, mu ma bamu san ta inda Allah zai taimake mu ba".

Sun yi tafiya mai É—an nisa, kafin su je unguwar da matar take.
Mijin Hajara ya sallami mai abin hawan, ya É—auki kayan Nana su ka shiga layin gidan.

A tsakar gida suka tarar da matar, ta cake É—auri tana ta lissafin kuÉ—i. Ta amsa musu sallamar tana yi musu maraba.
Suka shiga É—aya daga cikin É—akunanta. Ta kawo musu ruwa da lemo ta ajiye.
Cikin girmamawa Nana ta gaida matar.

Ta kalli mijin Hajara ta ce "Wannan ce yarinyar?"

Ya ce "Eh Nene"
Chapter 32 · 0% Book details