← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 78

Sashe 20

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ƙarya ka ke yi Ƙaisar. Ɗana ba zai zama bawa ga gajiyayyun halittu kamar bil'adama ba, ka sani yadda suke yi mana kallon halittu maƙaryata, haka su ma ba su da cika alƙawari. Ka tuna kai makaranci ne, manazarci kuma marubuci. Ka karanta litattafai da ni kaina ban san adadinsu ba. A ɗakin karatun ka akwai litattafan da aka rubuta dubbanin shekaru kafin zuwanka Duniya. Ka yi yawace-yawace a Duniya domin neman abubuwan rubutawa, kuma ina da tabbacin ka karanta tarin kashedin da magabantanmu suka yi mana a kan bil'adama. Dan haka ba zan bari iliminka da soyayyar da nake yi maka, su ƙare a kan yi wa biladama hidima ba, ba ma su su yi maka ba. Sai dai ka zaɓa, zama da mu ko kuma hidima ga bil'adama!"

Ayshercool
08081012143
59

Ƙaisar ya ce "Haƙiƙa kai Babana ne, ka so ni mai sonka ma ya so ni. Kuma na san ni ne ruhi mafi soyuwa a gare ku. Ka tallafawa burikana da bani damarmaki a matsayina na ɗanka. Sai dai ka tuna, na kawo girman da zan iya yankewa rayuwata hukunci. Kamar yadda ka faɗa; na karanta kashedin da aka yi mana a litattafan magabata, na yi yawon neman labarai a duniya, amma babu inda na ga an ci riba da tashin hankali da yaƙar juna. Kuma Aljani bai taɓa nasara a kan bil'adama ba, komai tasirin cutarwar da ya yi masa.
Na yi abota da bil'adama, na karanci wasu abubuwa masu muhimmanci dangane da zamantakewar su. Kuma ina son na yi amfani da ilimina na sanin magunguna, na sanar da wasusn su, domin samun waraka daga wasu cututtukan da mu ne muke haddasa musu su.
Dan haka ina mai baka haƙuri, na riga na yi alƙawari ba zan iya warwarewa ba. Sannan ba a banza zan yi wa zuriyar sarkin baka wannan aiki ba. Kamar yadda na gaya maka, sun sadaukar mini da duk wani mai irin tauraron Lanti, domin gudanar da burina na son yaɗuwar ilimin bayar da magani"

Cike da ƙunar rai Giyaz ya numfasa ya ce "Shikenan, ka yi abin da ka ke so, amma ka je, na sallama ka daga cikin zuriyaramu, kar ka sake danganta kanka da mu" daga haka Giyaz ya ɓace.

Lanti ta damu da mutuwar kakanta, sai dai ba a rufa sati ba, 'yar ta ma mai larurar shan Inna ta mutu. Ta shiga tashin hankali sosai da sosai, tamkar za ta zauce.

Hankalin Sarkin Aska kuwa ya yi mummunan tashi, bayan da Duna ya sanar da shi cewar, da Uban duƙusa aka yi wa Lanti girka. Kuma cutar da Uban duƙusa ka iya kawo fitina da tashin hankali a tsakanin su kan su Aljanun. Duk da zafin bil'adama da Giyaz yake ji a kan abin da suka yi wa mahaifinsa, amma ba zai lamunci kowane Aljani ya taɓa masa ɗa ba.
Sarkin Aska ya ji baƙin ciki ba kaɗan ba,  da abin da Duna ya gaya masa, bayan tabattar da cewa ya samu abokiyar hamayya a garin.

Ƙaisar ya fara bawa Lanti magunguna, ta fara aikin bayar da magani a garin. Babu nasiha da rarrashin da ahalin Ƙaisar ba su yi masa ba, a kan ya janye daga harkar taimakon biladama, amma fafur ya ƙi ya ce ba zai daina ba. Akwai kyakykywar fahimta a tsakanin Lanti da kuma Ƙaisar.
Lanti ta kuma samun juna biyu, ta haihu sai dai É—an da ta haifa, ba ta haife shi da irin taurarinta ba.
Aka shiga zazzafan takun saƙa, a tsakanin Lanti da Sarkin Aska, dan mutane suna tururuwar karɓar magani a gurinta. Domin ita ba ta tsauwwala wa mutane, kuma ba ta neman su kawo wani abu da ya fi ƙarfinsu. Duk da Giyaz ya sallama Ƙaisar, amma hakan bai bayar da damar, 'yan uwansa su iya cutar da shi ba.
A lokacin sai zuriyar Jaddul Jinn wasu suka goyi bayan zaman lafiya, kamar yadda Ƙaisar ya yi, wasu kuma suka zauna a kan bakar su na lallai sai an ci gaba da cutar da bil'adama da duk wanda ya fito daga wannan tushe na Buda.
Sarkin Aska ya ci gaba da jan Aljanu, yana sadaukar musu da jini, yana amfani da su ta hanyar tsafi, da kuma alwashin taimaka musu a duk lokacin da suke buƙatar hakan.
Cike da baƙin ciki, Giyaz ya zura wa Ƙaisar ido, babu yadda ya iya da shi.
Ganin abin da Sarkin Aska yake ci gaba da yi, duk a ƙoƙarin sa na mamaye garin a ci gaba da tsoron sa, ya sanya Lanti ta ƙara zage damtse a kan harkar bayar da magani da laƙantar hanyoyin da za ta kawo ƙarshen Sarkin Aska.

A haka ta haifi yara biyar maza, duk babu mai irin tauraronta, gaba ɗaya abin ya damu Ƙaisar, ganin babu wanda zai iya gadar ayyukan Lanti.
Sai dai a jininsin mutane ma, 'yan uwan Sarkin Aska ba sa ƙaunar abin da yake aikatawa na zaluntar mutane.
Wata jakar fatar damusa, Ƙaisar ya sanya Lanti ta fara haɗawa, wadda da ita take burin kawo ƙarshen Sarkin Aska, saboda babu irin mugun hari da yinƙurin da Sarkin Aska ba ya yi, dan ya kashe ta.
Sai da ta shekara biyar, tana aikin jakar nan, tare da jiƙata da magunguna daban-daban. Ban da zanen hatimai kala-kala da yake cikin jakar.
Ta haɗa kai da ɗan uwan Sarkin Aska, baya nan ya je ya ajiye masa jakar a ƙasan abin kwanciyar sa. Kuma ƙaisar ya ɓatar da sahun sa, ta yadda babu wanda ya gane a cikin aljanun da suke yi masa hidima. Tun da ya kwana a kan jakar, Aljanun da suke yi masa aiki, suka watse suka bar shi, ya kamu da matsananciyar rashin lafiya da sai da ta yi ajalinsa. Yana mutuwa kuma aljanun suka fantsama kan 'ya'yansa da jikokinsa, sai dai aka rasa wanda zai gaje shi gurin ci gaba da aikin zaluntar al'ummar da yake yi. Sosai mutanen gari suka yi murna da mutuwar sa. Babban ɗan sa da suke bokancin tare ma, cewa ya yi ba zai iya ba.
Ƙin samun wanda zai gaje shi, ya sanya aljanun fara sanya wa iyalansa cututtuka. Wasu kuturta wasu suka makance, har da waɗanda suka haukace. Aka din ga ɗauki ba daɗi da Lanti, a kan sai ta warkar da su. Ƙaisar ya gargaɗe ta a kan babu ruwanta ta rabu da su.
Lanti ta shafe shekaru Ashirin da bakwai, tana aiki tare da Ƙaisar tana harkokinta na bori da bayar da magani, haka zalika ita ma ta yi wa mutane da dama girka, masu sha'awar harkar bori. Akwai bikin 'yan bori da ake gudanarwa da nuna bajinta duk shekara, wanda a nan ake yi wa masu so girka, ake bikin bajekolin abubuwan ban mamaki, na gidaje daban-daban.
Maharba su yi na su, wanzamai, 'yan bori da dai sauran su.
Domin bayan mutuwar Sarkin Aska an É—an samu zaman lafiya, tun da dama shi yake assasa duk wata fitina da rashin zaman lafiya. Sai dai aljanu ba su fasa cutar da su da razana su ba, duk da Lanti tana iya kokarinta. Sai dai ita ma bayan wannan shekarun ta koma ga Allah.
Sai dai kan ta mutu, a cikin jikokinta an samu guda É—aya da take da irin tauraronta.
Dan haka bayan mutuwar Lanti, aka ci gaba da ba ta kashi tsakanin mutanen garin, da Aljanun da sarkin Aska ya yi aiki da su, har ma da waÉ—anda ba 'yan asalin garin ba ne.
Sai dai babu yadda Ƙaisar zai yi, a lokacin jikar Lanti ba ta kai lokacin da za ta iya bayar da magani ba. Kuma har a lokacin ba a fasa yi masa magiyar ya rabu da bil'adama ba. Gaba ɗaya ya nesan ta kansa da Ahalinsu.

Bayan jikar Lanti ta fara tasawa, Ƙaisar ya fara bijiro mata, domin yin gadon kakarta, sai ta kasa ɗauka sai ma taɓin hankali da ta samu, duk da ta ɗan taɓa bayar da maganin amma ba sosai ba. A hakan ita ma ta yi aure ta hayayyafa.
A cikin 'ya'yanta aka samu wadda ta gaje ta, duk da ba irin tauraronta ɗaya da Lanti ba. A lokacin Musulunci ya shigo cikin mutane, duk da bai yi ƙarfi a garin Buda ba.
Asma'u ta bayar da magani ita ma, ta yi aiki tare da Ƙaisar, sai dai ba ta da ƙarfin zuciya da juriya irin ta Lanti. Gaba ɗaya ita ma ba wani daɗin aiki ya ji da ita ba. Ko yaya ya buɗe mata ido ta ga abu, sai ta kwanta ta hau jinya. Daga baya ma ta watsar ta tattara komatsan borin ta ajiya, ta ce ta tuba ta daina.
Ganin ba a samun masu irin tauraron Lanti, ya sanya Ƙaisar fara sarewa, da haƙura da batun bayar da magani ta hanyar bil'adama. Sai dai yana iya yin sa gurin bawa zuriyar su Lanti kariya, daga cutarwar zuriyarsu.
Duk abin da yake faruwa, Giyaz yana ankare da Ƙaisar, kuma yana murnar yadda ɗan sa ba zai ci gaba da zama bawa ga bil'adama ba.
Chapter 20 · 0% Book details