← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 78

Sashe 67

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na ce miki yarinyar nan ta daina shigowa, bana jin daÉ—in jikina idan na ganta, ina kyautata zaton ma ba mutum ba ce ba"

Asal ta tuntsure da dariya ta ce "Mutum ce fa, dan dai kawai ba ka son hayaniya ne, kuma ba hankali ta cika ba. Amma ai Abincinta yana yi maka daÉ—i, shi ka ke ci fa, kuma idan ba ita ta yi ba baka ci"

Ya numfasa ya ce "Ni dai kar ki É—aukko abin da zai zame mana matsala"
Ta karairaye murya ta ce "Imam ba zan taɓa kawo abin da zai cutar da mu ba, ka kwantar da hankalinka za ka daina ji, ka san ita ba ƙabilarmu ba ce, ba kuma 'yar ƙasarmu ba ce ba, shi yasa ka ke jin haka, amma ka kwantar da hankalinka"

Ya jinjina mata kai kawai bai ce komai ba, ya san ba za ta taɓa fuskantar halin da yake shiga ba.

*****
Yusra da Sagir su na zaune a falonsa, yana ta kallon agogon hannunsa, Shukura yake ta jira ta fito yana so ya haÉ—a su, ya yi musu nasiha, amma kusan awa guda da yi mata magana, amma shiru ba ta fito ba.
Ransa ya ɓaci da irin wannan wulaƙanci da take ta yi, ya rarrashe ta, ya ba ta haƙuri amma ta ƙi sauraren sa, sai wulaƙanci take yi masa yadda ranta ya ga dama. Ga shi yana tausayinta saboda tsohon ciki da yake jikinta, ga hawan jini, amma ko a jikinta tsakaninta da shi gaisuwa ce kawai, bayan wannan idan zai shekara yana magana, ba za ta kula shi ba, sai dai ya gaji ya tashi.
Yanzun ma har ya fusata zai je ya same ta, sai ga shi ta fito, fuskar nan babu annuri da alama ma fita za ta yi.
Ta zo ta nemi guri ta zauna, ta yi shiru ba ta ce komai ba.
Yusra ma ta kalle ta ta basar, ba ta kula ta ba.

"Mu na nan mu na ta jiran ki tun É—azu, amma baki fito ba"

Fuska a É—an tsuke ta ce "Shiryawa na tsaya yi ne"

"Ina za ki je ne?"

Ta kwaɓe fuska ta ce "Awo" Ta ba shi amsa a taƙaice.

Ya numfasa dan ba ya son biye mata, dan ya ga a kusa take, ko alamar ganin Yusra ba ta yi ba.

"Amm dama ba wani dalili ya sanya na tara ku a nan gaba É—aya ba, ina son in gabatar muku da juna, sannan kuma na yi muku nasiha a kan haÉ—in kai da zaman lafiya.
Shukura kamar yadda ki ka sani tun da farko, kafin na aure ki, na auri Yusra sai dai ƙaddara ta gifta mun rabu. Ke ma kuma Yusra na sanar da ke bayan rabuwarmu na auri Shukura.
Dan haka ina mai roƙonku a kan zaman lafiya da haƙuri da juna, domin na samu nutsuwa na yi muku adalci.
Yusra ga Shukura, Shukura ga 'yar uwakki Yusra"
Da ƙyar Yusra ta ce "Sannu"

Haushi ya kama Shukura, wai sanni sai ka ce wadda take ciwo, da ya san zai dawo da Yusra dan me zai sake ta ya aure ta.

Sagir ya ce "Shukura tana yi miki magana fa"

Shukura ta ce "Hankalina na yana kan tafiyata Asibiti ne, ba na jin daɗin jikina. Amarya ina yi miki barka da zuwa, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya" Ta ƙarasa maganar tare da miƙewa da ƙyar.

"Shukura ki tsaya mana mu gama sai ki tafi"

Cikin fushi ta ce "Na ce maka fa bani da lafiya, kwana na yi ba na jin daÉ—in jikina"
Sai kuma ya tuna takaicin abin da take yi masa ya sanya bai je ya ganta da daddare ba, ya wuce gurin Yusra.

Shukura kuwa tuni ta nufi ƙofa, ya bi bayanta yana "Ki tsaya na sauke ki a Asibitin"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ka koma gurin amaryarka, kar ka bar ta itakaÉ—ai"

Jiki a sanyaye ya kira sunanta, ta É—aga ido ta kalle shi. Idanunta sun yi jawur sun cika da hawaye.

Hannu ya sanya yana share mata hawayen da ya fara gangarowa kan kuncinta, ya ce "Dan Allah Shukura ki daina, ban dawo da Yusra dan na ɓata miki rai, ko na cutar da ke ba, wallahi kukan nan da ki ke yi da rashin walwalar ki yana damuna ba kaɗan ba, dan Allah ki daina"

Ta ce "Tom, bari na tafi kar na makara"

Ya ce "Bari na canzo kaya na zo na kai ki"

Ta ce "Kar ka damu, zan iya driving ai, yanzu zan dawo in sha Allah"

"To me za ki sayo mini idan kin tashi dawowa?"
Murmushin yaƙe ta yi ta ce "Me ka ke so?"

"Abin daɗi, sai kuma uwa uba ki ƙara yi mini murmushin nan dan Allah"

Murmushin ta sake yi tana taɓa jakarta.

Ya dafa cikinta ya ce "A dawo lafiya Allah ya tsare, ki kular mini da kan ku sosai. Dan Allah ki daina fushin nan da ni Shukura, kin ga yau zan dawo gurinki, kuma ina son zuwa inda ki ke amma yadda ki ke yi mini ne ba na jin daÉ—i, har fargabar zuwa inda ki ke nake yi. Dan Allah idan na zo kar ki haÉ—e mini rai dan Allah sweetheart"

"Tom"

"Tom É—in nan kuwa ta kai zuci?"

Shukura ta ce "Ta kai mana"

"Yauwwa babyna, ina jiranki, ki dawo da wuri dan Allah"

"To in sha Allah"

Ya buɗe mata motar, yana jin daɗin yadda ta sakar masa fuska, tsayawa ya yi janta da hira, yana tsaye a bakin ƙofar motar, ita kuma tana ciki a zaune. Abin mata da miji sai ga Shukura tana dariya, da haka suka yi sallama ta fita.
Yusra kuwa sai da haushi ya kama ta, yadda ya yi ficewarsa ya je ya shantake a gurin Shukura, kamar ma ya manta da wanzuwarta a gurin.

*****

Duk yadda Asal take É—okin Imam, gaba É—aya gani take kamar ba a cikin nutsuwarsa yake ba, kamar wani abu yana damunsa, babu yadda ba ta yi ba a kan ya gaya mata mene ne yake damunsa ba, amma ya ce mata shi babu abin da yake damunsa.

A hankali ta yi juyi a kan gadon, ta zuba masa ido yadda yake ta uban gumi, tare da yin haki, har sai da ta É—an tsorata. Sai dai ta ga ya yi juyi ya ci gaba da baccinsa.

Kwana biyu Nana ta daina yadda su haɗu, kamar yadda ya buƙata, sai dai yau da ta shiga ta tarar yana nan. Babu tsammani ya ga Nana, hakan ya sanya ya ɗan zabura, har sai da ta gani.
"Sayyid ina kwana" Shiru ya yi yana tunani, sai kuma ya maze bai motsa ba.
"Ban san laifin da na yi da ya sanya, ka nemi na daina zuwa inda ka ke ba, amma idan laifi na yi maka, ina neman afuwarka Sayyid"
Sannu a hankali kalmomin da ta yi amfani da su, suka din ga shigarsa ɗaya bayan ɗaya, yana jin kalaman na da wata fassara da yakamata ya sani, amma ya kasa gano fassarar, duk da yana jin yaren na hausa, kuma da shi ta yi maganar. Ƙamshin turaren sa da Asal take faɗa, yanzu ma shi yake ji yana tashi a jikinta.
Ta miƙe ta yi waje cikin sanyin jiki, kawai ya tashi ya yinƙura, ya bi bayanta. Sai dai ya tsaya a bakin ƙofa yana tunanin to idan ya bi bayanta ina zai je, ko kuma me zai ce mata?. Kawai ya koma da baya ya nemi guri ya zauna.

*****
Satin bikin Abba ya kama, Hajiya Sa'a duk ta yi busy, Jamila kuma ta rage zuwa gidan gaba É—aya.

Hajiya Sa'a tana ta jiran Abba za ta aike shi, amma shiru har sha É—aya na safe bai fito ba, haushi ya kama ta dan muraran yake adawa da auren nan da zai yi.
Bala'i take ta yi, tare da alwashin É—aukar mummunan mataki a kan Jamila. Dan a cewarta ita take ziga shi.

Ta shiga É—akinsa tana bala'i, kawai ta gan shi a kwance yana bacci.

"Abba wannan wane irin bacci ne har haka? Kai da muke da hidima a gaba, dan ka nuna mini ban isa ba, shi ne za ka nemi guri ka yi ta baccin asara" Sai dai ya yi shiru bai tashi ba.
Ta ƙarasa ta ɗala masa duka a ƙafafuwansa, amma shiru bai tashi ba.
A iya saninta, Abba ba shi da nauyin bacci, amma yau dai abin ya yi yawa. Ta jirkita shi, ga mamakinta kawai ta gan jini a hancinsa, da bakinsa ga fatarsa ta yamutse jikinsa ya yi fari ƙwal. Sai dai yanayin jikin nasa ya nuna akwai nutsuwa a tattare da shi.

Wani irin magigicin ihu Hajiya Sa'a ta yi, ta hau kururuwa tana jijjiga gawar Abba, tana kiran sunansa da wata irin murya ta tashin hankali, girgiza shi take yi tana ihu da kururuwa a kan gawar, amma Abba rai ya riga ya yi halinsa.
Hajiya Sa'a ta tashi da gudu ta nufi cikin gidan, tana ihu tana kururuwa tana "Wayyo Allah na shiga uku, dan Allah ku zo ku taya ni duba É—ana me ya samu Abba, dan Allah ku taimake ni kar Abba ya mutu ya bar ni na shiga uku na lalace"
Tuni mutanen da ke gidan, suka fito aka je aka dudduba aka tabattar da mutuwar Abba.
Ɗaya daga cikin ƙawayenta ta ce "Kuma ba guba ya sha ba, ko wani abu ko ba shi da lafiya?" Hajiya Sa'a babu baki sai kuka kawai da take yi.

Safiyya ta ja ta tayi waje da ita, ba su tsaya a ko ina ba sai bedroom É—in ta.

"Hajiya me ki ka fahimta game da gawar Abba?"

Cikin kuka da tashin hankali ta ce "Ni ban fahimci komai ba"

"Duk wanda muka bayar a ƙungiya, yana zubar da jini ne ta hancinsa da bakinsa, kuma fatarsu haka take komawa, wani ya bayar da Abba a ƙungiyar Asiri, ko tamu ko wata ƙungiyar".

Wani irin ihu Hajiya Sa'a ta zunduma, Safiyya ta toshe mata baki tana faÉ—in "Hajiya ki rufa mana asiri kar ki tona mana asiri a gano mu"
Chapter 67 · 0% Book details