← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 78

Sashe 21

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aka din ga samun ci gaba a garin Buda, wasu suka din ga barin garin su na tafiya fatauci, wasu kuma tashin hankalin Aljanun da ya addabi garin ne ya sanya suka bar garin, ciki har da wasu daga cikin zuriyar Lanti.
A can Bauchi aka haifi Maijidda, har ta girma, an saka mata rana saura watanni uku aurenta, su ka zo Buda, a nan suka haɗu da Isa, ya ƙallafa rai a kanta.
Yayar kakarta ta ce sai an warware wancan baikon da aka yi da na can garin Bauchi, an yi da Isa, saboda ƙara danƙon zumunci, kuma hakan zai sanya su din ga kawo musu ziyara a kai a kai, da ƙara samun zaman lafiya a tsakanin zuriyar maharba da ta wanzamai.
Aka mayar wa da wancan na Bauchi kuÉ—insa, ita kuma ta auri Isa.
Gidansa na Kano, inda yake harkokin kasuwancinsa, nan ya tafi da ita. Ya ajiye ta a gidansa da suke tare da matarsa babar Gaddafi.
Ya ɗora wa Maijidda son duniya, kamar a kanta ya taɓa aure. Ba uwargidansa ba, hatta 'yan uwansa sai da suka fara jin haushin Maijidda saboda ba ya ɓoye son da yake yi mata, ga ta yarinya ƙarama amma su na ganin kamar ta mallake shi, dan shekarunta goma sha shida a lokacin.
Kasancewar daga zuriyar Sarkin Aska Maijidda take, ta auri ɗan zuriyar Sarkin Baka, sai Aljanun da suka yi wa sarkin Aska hidima, suka shiga cikin lamarin auren, su ka fara haddasa musu matsala. Haka kurum sai ta ji ta tsani Isa, ba ta ƙaunar ganinsa ga yawan rashin lafiya. Kishiya da facaloli suka sako ta a gaba, ga jarabar dangin miji.
Ana haka ya samu matsala da uwargidansa, da ta haifa masa Gaddafi da Ummi, ya sake ta. Nan ma aka ce Maijidda ce sila.
Ya auri Rabi, suka zama ita da Maijidda. Yayarsa Atine ta ƙara haɗe kai da Rabi, su na cizguna mata.
Maijidda ke riƙon su Gaddafi, tana iya kokarinta amma kullum cewa ake yi tana azabtar da su. Kasancewar Gaddafi ya fi Ummi wayo, ya tsani Maijidda cewa yake saboda ita aka saki babar su, kamar yadda Yaya Atine take faɗa. Ita kuma Ummi tana matuƙar ƙaunar Maijidda.
Nan ma Rabi ta saka Maijidda a gaba, da kishi da ƙage kala-kala.
Bayan haihuwar Imran sai da ya shekara uku da rabi, ta haifi Nana. A lokacin Isa ji yake kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba sai a kan Nana. Ya saka mata suna Asma'u, sunan kakarsa da ta riƙe shi take bala'in son sa. Hatta hakika biyu ya yi wa Nana, Ummi ma da ya saka mata sunan mahaifiyarsa bai yi mata abin da yake yi wa Nana ba.
Isa kofur ne na 'yan sanda, abokan aikinsa suka yi masa ƙage, aka kore shi daga aiki har da prison. Ya koma harkar fawa, ya fara samun rufin asiri, harka ta buɗe masa yana samun rufin asiri sosai , sai dai kasancewar sa mutum ne da ba shi da sirri, duk samun sa sai ya bayar da labari, abokansa suka jefe shi sana'ar ta fita daga ransa ya daina zuwa ko ina, sai zaman gida.
Tun da Allah ya sanya aka haifi Nana Ƙaisar ya ganta ya rikice, tamkar Lanti ta yi kaki ta ajiye saboda kamanin su. Ga irin tauraronta ɗaya da Lanti. Gaba ɗaya Ƙaisar ya tattara hankalinsa a kan Nana Asma'u yana ganin, ya samu uwar gijiya a zuriyar Lanti. Giyaz na fuskantar abin da ke shirin faruwa, ya fara ƙoƙarin raba Ƙaisar da Nana. Dan kullum yana tattare da ita. Wasu lokutan ya zungure ta tayi ta kuka. Manyan bokaye da ƙungiyon Asiri na zawarcin son yin aiki da Ƙaisar, saboda tarin baiwa da kuma ilimi da binciken ƙwaƙwaf da yake yi. Wanda za su aiki da shi ne, ya din ga taimaka musu, su kuma su din ga yi masa hidima, amma fafur ya ƙi. Saboda ba ya son duk wata alaƙa da jini.
Ƙaisar ya yi tafiya zuwa wata ƙasa, ganawa da wani tsohon Aljani, a kan wani rubutu da yake yi, ya dawo ya tarar an saki Babar Nana, ita kuma Nana ta daina magana, ta daina tafiya ga Baba ya ƙwace ta, ya hana Maijidda ita. Ya fuskanci aikin mahaifinsa ne Giyaz. Ya je ya same shi yake tambayar sa me yasa ya yi wa Nana haka.
Giyaz ya ce "Ka sani ba zan taɓa sake yadda, ka zama bawan bil'adama ba, da ka sake zama bawan bil'adama gara na kashe ta ko na kashe ka, kowa ma ya huta."
Ƙaisar ya san Giyaz ba ya magana biyu, idan ya faɗi magana sai ya aikata.
Dan haka Ƙaisar ya fara ƙoƙarin kare Nana, ya yi amfani da jakar da ya saka Lanti ta haɗa, ta yi amfani da ita gurin kashe Sarkin Aska. Ya ƙara yi mata aiki, da saiwoyi da wasu hatimai, ya yi wa Giyaz tarko da ita.
Cikin matsananciyar sa'a, Giyaz ya faɗa tarkon Ƙaisar, saboda ya san muddin ya bar Giyaz, zai iya nakasta Nana nakasa ta har abada, ko ma ya kashe ta, kamar yadda ya furta.
Ya É—auki Giyaz, ya kai shi can nesa ya sadaukarwa wani boka shi, bisa musayar da za su yi, zai ba shi wani abu mai muhimmanci. Wanda ya yi hakan domin nesan ta shi da Nana da zuriyar Lanti.

Duk da abin da ya yi ya dawo ya dame shi, yana matuƙar ƙaunar mahaifinsa, duk da saɓanin da suka samu, amma babu yadda iya, hakan ne kawai zai sanya ya nisanta shi da Nana.
Sauran 'yan uwan Ƙaisar da tuntuni suke jin haushinsa, suka yo caaa a kan Ƙaisar, har suka nemi hallaka shi, saboda abin da ya yi wa mahaifinsu, amma sun san ko sun hallaka shi, idan Giyaz ya kuɓuta suma sai ya kashe su.
Ɗan uwan Giyaz Duna, ya yi ta ƙoƙari gurin ganin ya kuɓutar da Giyaz, amma abu ya gagara.
Nan suka din ga kai wa Nana hari, da yinƙurin hallaka ta.
Maijidda kuwa bayan mutuwar aurenta, tana gama idda, Iliyasu tsohon saurayinta ya sake dawowa ya aure ta. Ko da Baban Nana ya samu labari, sai ya ce tana sane, ta ƙi zama da shi, saboda ta koma ta auri Iliyasu, dama son zama da shi take yi ba.
Nana ta ga garari tun da ƙuruciya, babu cikakkiyar kulawa, kuma tun ba ta fi shekara uku ba take ganin Ƙaisar, da ma sauran 'yan uwansa da suke ta kokarin azabtar da ita.
Maijidda ta so karɓar ko Nana ce, saboda rashin cikakkiyar lafiya, amma Isa ya hana fafur, ita ma can mijinta ko yaya ta motsa tana son ganin 'ya'yanta, sai ya hau bala'i wai za ta gurin tsohon mijinta.
Tun Nana na ƙarama, take nuna alamun rashin lafiya, amma babu wanda ya kula. Ta kan wuni tana bacci tun safe, har dare babu wanda zai damu. Wasu lokutan ta daina magana ma ko tafiya gaba ɗaya. Idan kuma ta warware ta din ga fitinar da ta fi ƙarfin shekarunta nesa ba kusa ba.
Ta kan ga Ƙaisar a zahiri, ko kuma a cikin bacci. Babu wanda ya damu da ta ci Abinci ko ba ta ci ba, mussaman da Baba ya daina sana'ar komai, sai dai Imran ya nema ya bata. Idan ta fita Ƙaisar ya kan zo a suffar mutum, ya ba ta abinci. Allah ya sanya masa matsananciyar ƙaunarta. Ya fara bayyana a jikinta ne, tun wani duka da Mama ta yi mata, bayan faɗa ya haɗa ta da Jamila.
Sai da ta kwana biyu a sanƙame, tun daga nan suka gane halin da take ciki. Da ranta ya ɓaci sai hankalinta ya gushe. Ƙaisar ya sha ɗauke Nana, a neme ta a rasa kwana ɗaya ko biyu ya je ya ajiye ta gurin sa.
Baba ya yi ƙoƙarin nema wa Nana magani, amma abu ya gagara. Labari ya iske Maijidda halin da Nana ne ciki, bayan da su Adda Saude suka zo ganin su Nana. Rabi ta haɗa tuggu a gurin Baba, ya ce kar su sake zuwar masa gida, kuma ba zai bayar da Nana ba. Wahala ta saka Imrana fara sace-sace saboda su ci Abinci, Rabi ta saka Baba ya kore shi daga gidan. Haka Nana ta tashi a cikin wahala, ga wanda bil'adama suke yi mata, ga wadda Ƙaisar yake yi mata da sunan kulawa.

Ji ta yi tamkar an sanya hannu an shaƙe ta, a dole ta saki littafin ta ja da baya tana tari.

Ta ɗaga kai ta kalli Ƙaisar, bai ce mata komai ba, ya ɗauki littafinsa ya juya ya tafi. Yana barin gurin Haula ta zagayo ta dafa Nana. Ta ɗaga kai ta kalle ta ta ce "Ƙawata, kwana biyu. Hadiminki ya ƙi saurarata balle na sanya ran zai karɓi buƙata ta, ki yi wani abu a kai dan Allah"

Nana ta ce "Haula, gaba É—aya jinsinku ba abin yadda ba ne, ki rabu da ni da wannan maganar ta ku"

"Shikenan, na rabu da ke, amma kin yi ganganci abin da ki ka yi wa dattijo, Allah kaɗai ya san me zai yi miki idan ya gama jinya. Kuma har Ƙaisar ki ka janyowa shi ma ba zai bar shi ba"

"Duk hukuncin da ya yi wa Ƙaisar yayi daidai, ɗa na gari ba zai taɓa yi wa babansa abin da ya yi wa nasa mahaifin ba"

Haula ta ce "Kash! Nana kar ki zama butulu mana. Sai dai ina fatan kin fuskanci jakar gurin Sarkin baka da ya baki, wace jakar ce"

Nana ba ta ba wa Haula amsa ba, Sayyid ya tashe ta.

"Ma vie" yayi maganar yana matsawa jikinta sosai. Jiki a sanyaye ta amsa masa. Ya ce "Lafiya dai?"

"Mmm"

"Ko Ƙaisar ɗin ne?"

"A'a"

"To me yasa ki ka tsorata? Mene ne ya baki tsoro?"

"Bakomai"

"es-tu sûr? (Kin tabatta?)"

Ta ce "Eh. Haryanzu hannunka lafiya ƙalau ko?"

"Eh, amma akwai abin da ya tsorata ki, gaya mini mene ne?"

Ji ta yi tamkar ta gaya masa, dan a wannan karon ba ta manta abin da Giyaz ya gaya mata ba, a kan idan ya warke zai sake waiwayar su.

"Ma viee"

"Sayyid" ta amsa a hankali.
Chapter 21 · 0% Book details