Sashe 34
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na san yanzu da da ba É—aya ba ne ba, amma ko yaya É—an abin da ki ke da shi idan ya samu, ko abinci ko kuÉ—i, ki din ga bayar da sadaka, da nufin Ubangiji Allah ya kawo muku É—auki,ya sassauta muku wannan yanayin da ku ka tsinci kan ku a ciki"
Fadila ta jinjina kai ta ce "In sha Allah"
"Tun kwanank da kawunki, ya zo ya duba mijinki, ya kira ni yake mitar, kun tare ku na maganin Asibiti, kun ƙi mayar da hankali ku yi na gargajiya. Na ce masa mijin naki ne ɗan aƙida, kuma ke na haifa ba shi ba, balle na yi masa dole. Amma nima hankalina ya fara karkata ga a yi na hausan, mijinki mutumin kirki ne, ba zan manta halaccinsa a gare mu ba, dan haka na bayar da kuɗi a yi saukar Alqur'ani, da fatan Ubangiji Allah ya yaye masa koma mene ne, tun da shi Alqur'ani waraka ne. Ki yawaita karanta masa, ko ki kunna ya saurara, ko ki din ga busa wa a abincinsa ko abin shan sa.
Ba mu san a inda za a dace ba, wannan abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, na Asibitin ba wani haske da ake gani, idan hagu ta ƙi ai sai a koma dama ko?"
Fadila ta ce "Haka ne Umma, in sha Allah, zan yi duk abin da ki ka ce, kuma addu'a mu na yin ta sosai, ina yi masa. Sai dai kin san lamarin Ubangiji ba a yi masa dole, duk addu'arka sai lokacin yankewar abu ya yi tukuna".
Umma ta ce "Haka ne, amma hakan ba ya nufin a sare, a ce an haƙura gaba ɗaya ba za a yi ba" Sosai Fadila take jin daɗin rarrashi da nasihar da Umma take yi mata a duk lokacin da ta zo gidan.
Ko da su Hajiya Sa'a suka je gidan Alhaji Fatuhu, Alhaji Zailani yana gidan. Yana sashen Alhaji Fatuhu tare.
Alhaji Zailani ya din ga kallon Jamila, yana ganin kamar ya santa, amma ya manta a inda ya san fuskarta.
Suka gaisa Hajiya Sa'a ta kalli Fatuhu ta ce "Yaya ya jikin naka?"
Ya jinjina kai ya ce "Alhamdillah"
"Ka na samun sauƙi, ko dai haryanzu babu afuwa?"
Ya yi murmushi ya ce "Da sauƙi" Daga haka suka koma hira da ita da Alhaji Zailani, tamkar ba dubiya su ka zo ba, bar sai da abin ya ba wa Jamila mamaki. Sun jima sannan su ka shiga suka gaisa da matansa suka tafi.
Su na tafe a hanya Jamila ta ce "Mummy, mara lafiyar nan shi ne wanda É—an sa ya mutu kwanaki ko? Yaran da Nana take koyarwa a makaranta"
"Eh shi ne"
"Allah sarki, to shi wannan Alhaji Zailanin, ko shi ne a can quaters ɗin bayan makarantar nan na ƙofar famfo?"
Hajiya Sa'a ta kalle ta ta ce "Ya aka yi ki ka san shi?"
"A'a na tambaya ne dai kawai, kenan shi ma Nana ta yi aiki a gidansa, yana da 'ya Shukura ko?" Hajiya Sa'a ta jinjina kai tana kallon Jamila.
"To ai da Nanan gidanmu zai aura, ba a yi ba, aka yi aurenta da wannan Buzun, lokaci É—aya kawai ya fito ya ce wai zai aure ta"
Shiru Hajiya Sa'a ta yi tana kallon Jamila, ta san abu ne mawuyaci a ce haka kurum Alhaji Zailani ya ce zai auri yarinyar da ta fito daga gida kamar na su Nana, da ƙyar idan ba ya san sirrin da ke tattare da Nanan ba. A take gabanta ya faɗi, dan kuwa ko me za a yi ba za ta taɓa barin Alhaji Zailani ya riga ta amfani da jinin Nana ba"
Jamila ta ce "Mummy ya na ji kin yi shiru ne?"
Ta girgiza kai ta ce "Babu komai Jamila, dole mu nemo Nana ne duk inda ta shiga"
Jamila ta ce "Saboda me?"
"Saboda ƙungiya, za ta iya neman ki kawo jinin mafi kusanci da ke, a kowane lokaci!
Ayshercool
08081012143
64
Jamila a ranta ta ce "Ni kuwa zan ga abin da ya ture wa Buzu naɗi, zan ga abin da zai faru idan na bijirewa buƙatar ƙungiyar"
Jamila ta numfasa ta ce "Mummy, dan Allah tambayar ki zan yi"
"Ina jin ki"
"Wai dan Allah, ya aka yi ki ka shiga ƙungiyar nan?"
Hajiya Sa'a ta kalli Jamila, sannan ta mayar da hankalinta kan tuƙin da take yi tana murmushi. Ta ce "Dogon labari ne Jamila, amma me yasa ki ka tambaye ni?"
"Ina son na ji tarihin gwagwarmayar ki ne, ko nima zan daure na yi koyi da jarumtar ki, haryanzu wasu lokutan zuciyata tana rawa ne a kan lamarin"
"Ai na ga alama kam. Jamila na sha gaya miki, muddin ki na son cimma abin da ki ke buri a rayuwa, babu ruwanki da kowa kan ki kawai za ki din ga dubawa.
Na tashi a gidanmu bamu da komai, babata da babar Fatuhu, su ne ƙanana a matan gidan, kamar dai yanayin rayuwar gidanku, a haife ka, ba a damu da ɗawainiyarka ba.
Manyan yayyenmu babu ruwansu da mu, saboda iyayen su mata sun cusa musu aƙidar ƙin iyayenmu. Babanmu ya mutu shi ma saboda bai bar komai ba, babu wanda ya damu da mu.
Yayyenmu iyayensu kadai suke taimako da ƙannen su, mu kuma namu iyayen ke ta fafutuka da wahala.
Fatuhu ya yi ta faÉ—i tashi da rayuwarsa, da ta mahaifiyarsa, sai dai yana tunawa da ni.
Zailani tsohon saurayina ne, da rashin abin yi ya hana mu yin aure da shi.
Ya shiga makaranta, bisa tallafin karatu, a can ya samo mana wannan ƙungiyar.
Shi kuma lokacin Fatuhu ya fara zuwa kasuwa, ni kuma na riga na yi aure.
Zailani ya gaza jan Fatuhu ƙungiya, saboda mutum ne mai tsantseni da ra'ayin riƙau. Ni kuma har a lokacin mijin da nake aure, ba shi da komai ba na samun irin rayuwar da nake so. Sannu a hankali na ci gaba da hulɗa da Zailani ya kai ni ƙungiya, ya zamana ba na rasa kuɗin kashewa dai.
Fatuhu kuma ya ja Zailani kasuwa, suke kasuwanci tare, sai dai duk da tasirn ƙungiya, Zailani ya kasa tara abin da Fatuhu yake da shi.
Kin san waye mutum na farko da na fara bayarwa?"
Jamila ta girgiza kai alamar a'a.
"Babban yayanmu, da iyayensu su ka mayar da mu saniyar ware a gida"
Jamila ta jinjina kai a É—an tsorace ta ce "Sai kuma ki ka ba da wa?"
Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta ce "Zan ƙarasa miki nan gaba kaɗan, yanzu bari mu ƙarasa gida, akwai abin da nake son yi"
Jamila ta jinjina kai tana satar kallon Hajiya Sa'a.
Hajiya Sa'a ta ajiye Jamila, sannan ta ja motar ta tafi. Tana tafe ta kira layin Alhaji Zailani.
Sai da ta kusa katsewa, sannan ya É—aga tare da yin sallama.
Ta ce "Ai na zata ba ka É—aga ba ne"
Ya ce "A'a ina tuƙi ne? Lafiya?"
"Ƙalau, tambayarka abu zan yi"
Ya ce "Ok, ina jin ki"
"Ashe kwanaki da aure zaka yi?"
Ya ce "Yaushe?"
"Kwanakin baya mana, za ka auri wata yarinya Nana"
Kamar tana gabansa ya tsuke fuska ya ce "Waye ya gaya miki"
"A'a ba sai ka ji wanda ya gaya mini ba, zancen Duniya ba ya ɓuya ai, sai dai ka sani na san da abin da ka ke nema, ni ma shi nake farauta"
"Sa'a ban fahimci abin da ki ke nufi ba fa, ki yi mini bayani gwari-gwari "
"Za ka fahimta ne, ka je ka nutsu ka yi nazari" ta kashe wayar ta ajiye ta ci gaba da tuƙinta.
*****
Yana zaune a takure a gurin, ya yi shiru tamkar mai jiran tsammannin wani abun, aka buɗe ƙofar ɗakin da yake . Wasu tiƙa-tiƙan murɗaɗɗun maza suka shigo. Ba su yi wata-wata ba, suka yi sama da shi, suka fito da shi daga gurin da yake zaune.
Wani É—akin aka sake kai shi, sai dai yana shiga ya yi turus, ganin mutumin da yake zaune a cikin É—akin.
Ƙartin suka juya suka fice, suka bar shi daga shi sai mutum biyu a ɗakin.
"Bismillah ka zauna mana" cike da tsoro ya ƙarasa ya zauna yana rarraba ido, ya sunkuyar da kansa.
"Mahmudu, É—agowa za ka yi ka kalle ni ai"
Ya É—aga kai ya saci kallon mutumin, ya mayar da kansa ya sunkuyar.
"Na san wannan zaman takurar ya ishe ka zuwa yanzu, kasancewarka mutum da ya saba da 'yanci a baya.
Ina son ka buÉ—e kunne ka saurare ni da kyau, tambayoyi nake son na yi maka, muddin ka gaya mini gaskiya ka bani amsa, zaka iya samun sassauci, ko ma na yi umarnin a sake ka, ka yi tafiyarka gaba É—aya"
Ya jinjina kai ba tare da ya É—ago ba.
Mutumin ya sauke rawnain fuskarsa ya ce "Na san an yi maka wannan tambayoyin an kum a baya, yanzu ma zan sake jaddada maka su, me yasa ka sace Imam ka kai shi Nigeria, da ka kai shi kuma me ka yi masa?"
Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya girgiza kai ya ce "Ban sace shi ba, kuma ban yi masa komai na cutarwa a Nigeria ba"
"To me yasa ka tafi da shi Nigeria ba ka sanar da kowa ba?"
Mahmudu ya ce "Wannan wani sirri ne da ba zan iya tona shi ba, ko da za ku salwantar da rayuwata, wani abu wanda daga ni sai shi Imam"
Abduou ya jinjina kai ya ce "Da amincewar sa ku ka tafi Nigeria kenan?"
"A'a hasalima bai san komai ba, ba wani da zaɓi ne da ya rage, sai abin da na aikata ɗin"
"Mahmudu, na fuskanci zama da maɗaukin kanwa ya sanya maka farin kai. Rayuwa da Imam ya sanya ka koyi baƙin taurin kai irin nasa. Amma ka snai, kama da wane ba ta wane, kuma ina fatan ka san da tun da aka ɗaukko shi daga Nigeria har yau ba ya hayyacinsa, bai yi magana da kowa ba?"
Mahmudu ya girgiza kai ya ce "A'a ranka ya daÉ—e. Rashin gane kowansa ba shi da nasaba da zuwansa Nigeria"
"Saboda me?"
"A can É—in ma ba gane kowan yake yi ba"