← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 78

Sashe 8

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ta É—an yi shiru ta ce "Kuma haka ne, yanzu zuwa gobe in Allah ya kaimu, zan samo dillalai su saya"

Cikin sauri Nana ta ce "A'a Ummi, ba na son ci gaba da zama a unguwar nan, ban san me za su yi mana ba. Idan da hali a nemo su yau kawai. Su saya gobe in Allah ya kaimu mu tafi"

"To shikenan, bari na fita na gani"

*****

Yana zaune a cikin office ɗin sa, ya ɗora ƙafafuwansa a kan tebur, yana juyi, ya din ga kiran lambar cike da fatan a ɗauka. Har ya yanke tsammani, kawai ya ji ta ɗauka, sai dai ta yi shiru.

Da sauri ya sauke ƙafafuwansa ya ce "Hello" ta yi shiru ba ta amsa ba.

"Hello ki na ji na?"

"Eh" ta amsa a raunane.

"To ba za ki yi mini magana ba?"

"Ba cewa ka yi ba ka gane ni ba, ranar da na kira ka?" Ya ɗan yi guntun murmushi ya ce "Ki yi haƙuri, sai daga baya na ɗauki muryar ne. Ya ki ke ina fatan kina lafiya?"

"Ai baka damu da ina lafiya ba, tun da ka sake ni baka ƙara nema na ba, saboda ka yi aure matarka ta haihu, dama ni haushina ka ke ji, ba na haihuwa"
"A'a Yusra, kar mu fara haka da ke. Kin san ko bayan mun rabu, na yi ta neman lambarki, amma ba ta shiga har na haƙura. Ya jikin ki?"

"Da sauƙi, amma ni ba mahaukaciya ba ce"

Sagir ya ce "Ai dama ban ce ba"

"Lokacin da muna tare ai ka ce" ya yi murmushi ya ce "Wannan ba ya wuce ba? Amma Mami ba ta san kin kira ni ba ko?"

"Eh, ina gidan Mummy Zahra, da wata na haÉ—u sunanta Nana, ita ma ta san irin rashin lafiyata. Ita ma tana yi"

Ya ce "Haba dai?"

"Wallahi. Ita ta din ga ba ni shawara, ita ce ma ta ce na kira ka fa, na ma zata ba zaka ɗauka ba, ka ɗauka amma ka nuna ba ka gane ni ba" dariya ya yi ya sakankance sosai, yana sauraren Yusra. A yanayin surutun da take yi, ya fuskanci jikinta da saura, ba ta warke ba, amma ya tattara hankalinsa yana sauraren ta. Hirar ta din ga tuna masa da yadda suka zuba soyayya a baya kafin aure. Yana kallon kiran Shukura amma ya ƙi ɗagawa ya ba wa Yusra lokacin sa.

"Ki na ji na"

"Eh"

"Yanzu ina gurin aiki, kuma lokacin salla ya yi, zan sake kiran ki, in sha Allah"

"Tom sai anjima"

"To 'yar farata, bye-bye"

Kamar tana gabansa ta saki murmushi, cike da sanyin jiki, saboda ta yi kewar jin sunan.

Shi ma murmushin ya yi, yana tuna wasu abubuwa da suka wuce.

Ya kira Shukura, sai da ta kusa katsewa sannan ta É—aga. "Madam ya aka yi ne?"

"Ina ta kiran ka, kana waya, har da rejecting kirana"

"Sarkin ƙorafi, kin san da wa nake wayar ne?"

"Ai ba sai ka gaya mini ba, na san 'yan matanka ne"

"Ni ba da 'yan mata nake waya ba. Ya aka yi?"

Shukura ta ce "Ba komai"

"Madam Shukura, bakomai É—in ki, na nufin akwai komai. Yanzu dai a yi mini afuwa da ni da 'yan matan nawa."

"Ni shikenan kawai" ta kashe wayar. Ya girgiza kansa tare da É—an lumshe idonsa.

****

A ranar dillalai, suka saye wardrobe da mudubin Nana, da sauran kayan da take ganin za su zame musu shirgi.
Ta tattare musu kayan su cikin bagcco, duk wani kayan amfaninsu ta tattare. Da safe ƙarfe goma, ita da Ummi suka je suka samo taxi. Har fargaba take yi kar mijin Ummi ya yi ƙorafi a kan yawon da take yi saboda ita. Duk da ba mazauni ba ne. Suka yi cinikin a nawa zai kai su Garko cikin ƙauyen Buda.
Aka É—aure katifa a saman taxi, aka loda kayan su a ciki.
Ummi ta shiga gaban motar, ita da babbar 'yar ta Islam.
Nana kuma suka shiga bayan motar, tare da Sayyid.
Ya kwanta a jikin Nana ya yi shiru, ita kuma ta riƙe hannunsa tana matsa masa a hankali cike da kulawa.

Awa É—aya da rabi, suka isa har cikin garin Buda. Sai dai shigar su garin ke da wuya, Nana ta fara jin sanyi yana ratsa ta.
Addu'a ta din ga yi, a kan Ubangiji Allah ya rufa mata asiri, ya kawo musu ɗauki, ya shiga tsakaninsu da su Ƙaisar.

"Ma vie" ta ji ya yi magana.

"Na'am Sayyid" Sai kuma ya yi shiru, bai sake cewa komai ba. Yara suka firfito suka tatstsaya bayan ganin mota ta tsaya a ƙofar gidan Uwani.

Uwani da kanta ta fito tana tafa hannu, tana "Maraba da mutan birni. Ina yayar tawa take?" Nana ta buÉ—e motar ta fito tana murmushi.

Ummi ta sallami mai motar, Uwani ta ce "Ina mai gidan?"

Nana ta buÉ—e taxi É—in, ya fito a hankali, kansa rufe da mayafi.

Uwani bakinta fal magana, amma ta haɗiye ta yi musu maraba, zuwa cikin gidan. Babban gida ne mai ɗauke da ɓangarori. Ta kai su sashen ta, aka yi shimfiɗa Sayyid ya zauna ya jingina da bango.
Abin da dai ba ya ƙauna, ya sake tararwa a garin, kallo. Ba ya son a zura masa ido, amma ya lura da yadda ake ta kallon sa.

Uwani ta karrama su da ruwan pure water, da abinci shinkafa da wake.

Ummi ta ce "Kafin cin abinci, Uwani a ina za su zauna, a gyara musu?"

Sai da Uwani ta sake yi wa Ummi ta tas, tamkar ita ce Baban, sannan ta kalli Nana ta ce "Yayata, kin ga cikin gidan nan, akwai É—akuna, idan ma ba zaku zauna a nan ba, nan baya tafiyar babu nisa, akwai gida da É—akuna biyu da tsakar gida. Babu kowa a gidan idan za ku zauna".

Nana ta ce "Gara su zauna a inda babu kowa"

Ummi ta ce "Maimakon ku zauna a cikin mutane, yadda ko wani abin ne, a taimaka muku"

Nana ta ce "Akwai dalili gara mu zauna inda babu kowan" Nana kuwa ta yi hakan ne, domin samun rufin asiri na larurar da suke fama daga ita har Sayyid. Ga uwa uba takura da Sayyid ba ya so.

Uwani ta saka yara, su ka je su ka share gidan tas, aka wanke.

Nana ta ce "Sayyid, bari mu je da Ummi, a gyara gidan, sai mu zo mu tafi da kai" Ya saka hannu ya riƙe nata, tare da girgiza mata kai alamar a'a.

"Mu tafi tare za ka iya tafiya?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

"To ta so" Ya yinƙura a hankali ya tashi tsaye.

Uwani ta ce "Nana, ku bar shi a nan mana, tun da ba shi da lafiya, ke ku je, ku gyara gidan"

Nana ta ce "Ai ba zai zauna ba, ya ce bin mu zai yi"

"Ikon Allah, ni da bita zai-zai, to Allah ya taimaka" Nana ta yi murmushi kawai, tare da jin nauyin abin da Sayyid É—in ya yi.

Sauran yaran gidan Uwani, suka bi su Nana, su taya su shirya kaya. Wanda galibi Nana ba ta ma san su ba, saboda ba zuwa garin suke yi ba, domin ita rabonta da garin ma, har ta manta.
Gidan ƙasa ne tsura, da zunzurutun turɓaya Ɗaki ɗaya ne gyararrre, sai aka yi masa siminti, da plasta, aka shafa farar ƙasa, da ƙofar langa-langa. Sai wani ɗakin kuma, si kuma ko rufi babu, sai banɗaki.
Duk lalacewar gidan su Nana ya fi nan nesa ba kusa ba, Ummi jarumta kawai take yi, zuciyarta a cunkushe babu daÉ—i, biyo bayan tuna cewar a nan Nana za ta rayu. Sai dai ta ga tsantsar tawakkalli a fuskar Nana. Su ka gyara É—akin aka shimfiÉ—a leda, sai katifar su. Sai kuma tarin kayan su, na girki sai na sakawa a cikin bagco.
Uwani ta aiko musu da Abinci. Da la'asar bayan Ummi ta yi salla, ta ba wa Nana kuÉ—in barkononta da aka sayar, ta yi ta mata nasiha da kwantar mata da hankali, sannan ta yi musu sallama.
ÆŠan gidan Uwani ya É—auke ta a kan babur, ya tafi da ita.

Nana ta ƙarasa gaban Sayyid, da ya zuba mata idanu tamkar bai taɓa ganinta ba.

Ta riƙo hannayen sa ta ce "Sayyid, duk da ban san wace irin rayuwa ka yi a baya ba. Amma wadda muka yi, mun yi ta ƙarƙashin kulawar su Habu, ba mu taɓa neman abu mun rasa ba. Amma Allah shi ne abin godiya. Wannan yanayin da muke ciki, ba zai dauwama ba in sha Allah. Ina fatan Allah ya baka lafiya, ya kuma baka haƙuri da juriyar a yanayin da muka tsinci kanmu a ciki".

Ya sanya tafukan hannayen sa biyu, a fuskarta laɓɓansa na rawa, amma magana ta gagara.

Ta girgiza masa kai tana murmushi, ta ce "Ruhinka yana cikin jikina, kar ka damu kanka lallai sai ka yi magana. A jikina ina jin abin da ka ke son faɗa" ɗan guntun murmushi ya yi, duk da yadda yake matuƙar son ya furta wani abu.

Da daddare Uwani ta aiko musu da tuwon dawa, da miyar karkashi, ta sha daddawar kalwa har É—aurin yajin daddawa.
Ta san ba lallai ya iya ci ba, ta ba wa yaran da suka kawo kuÉ—i, ta ce su sayo mata buredi da shayi, na gurin masu sayarwa, da kuma maganin sauro, saboda azabar sauron da ke É—akin.
Sai dai ya ƙi shan shayin, buredi kawai ya ci ya kwanta. Nana jikinta na rawa ta ci tuwon, saboda yadda ranta ya biya, amma ƙarshe amai har ta hancinta sai da ta yi shi.

Kan su kwanta, ta kunna maganin sauro, ta gyara masa shimfiÉ—a ya kwanta. Ita ma ta hau katifar ta tofa masa Addu'a, sannan ta kwanta a kusa da shi, tana yi masa fifita.
Chapter 8 · 0% Book details