Sashe 40
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nana, masu iya magana suka ce mugu shi ya san makwantar mugu. Ni na yi harkar bori da bayar da magani, ni baƙin aljani ma na gada daga gurin mahaifina. Ya azabtar da ni ya hana ni aure, na ƙi bayar da magani ya shanye mini ƙafafuwa, na daina al'ada na fara hauka tuburan. Sai da na bayar da magani, bayan wasu shekaru, na daina al'ada na fara hauka tuburan. Sai da na bayar da magani, bayan wasu shekaru, na gaji na ce zan ajiye, saboda kullum cikin larura nake, ga shi ya sanya na saka a yi ta zubar masa da jini. Ya sake burkita ni, ya hana ni aure, na koma ciwon hauka yau na kuturce gobe na daina gani, anjima na kasa tafiya. Ya buɗe mini ido nake ganinsu muraran a siffofi na ban tsoro, nake jin maganganun su a cikin kunnuwana. Ya ɗauke ni ya kai ni can wata uwa duniya ya yasar da ni, na yi ta gararamba sannan ya gaji ya dawo da ni. Ko ya saka na yi ta zubar da jini babu ƙaƙƙautawa.
Duk inda muka je neman magani, sai a ce sai dai na haƙura na ci gaba da bayar da magani.
Da ƙyar wani mai magani ya raba ni da shi, ta hanyar yin amfani da wani aljanin. Ya kafa sharuɗɗa sai da aka yi masa yanka, da sauran abubuwa dai na sharuɗɗa sannan Allah ya raba ni da shi. Bayan mun rabun ma, da ƙyar na samu na yi aure, shi ma dai kusan kullum cikin rigima da miji, na zo babu haihuwa, sai rigima sai dai ya dage ya ƙi rabuwa da ni. Sai daga baya Allah ya bani haihuwar ɗa namiji, daga nan ban sake haihuwa ba. Yarona yana can ƙasarku Nigeria. Mijina kuma Allah ya yi masa rasuwa, ni kuma na ci gaba da sabgogina ban sake wani auren ba, duk da wasu lokutan haryanzu abubuwan na taɓa ni."
Nana tana Libraryn Ƙaisar, daga can nesa take jiyo maganar Nene.
Kai tsaye gurin mudubin nan ta nufa, cike da fatan ta sake ganin ko fuskar Sayyid ne, amma ta tarar da mudubin wayam, sai ma baƙi ƙirin da ya yi.
Ta daÉ—e a tsaye ta zura wa mudubin idanun amma babu alamar wani abu zai bayyana a mudubin ta gani.
Ta hango littafin da ta fara karantawa a yashe a ƙasa, inda ta yasar da shi, hakan ya tabattar mata da Ƙaisar ba ya cikin ɗakin karatun nasa na wani lokaci.
Ta sanya hannu ta É—auki littafin, ta nutsu ta ci gaba da karantawa.
"Idan ka bari tsoro ya É—arsu a cikin zuciyarka, to tabbas ba za ka iya cimma abin da ka ke hari ba. Tun da kawar da mahaifinka bai yi maka wahala ba, wannan ma ba zai gagare ka ba, ka kashe su É—aya bayan É—aya, ka yi mulki cike da izza ka tara sojoji da runduna da za ta razana duniya".
Ire-iren waÉ—annan kalamai na ziga da kambamawa, ya sanya matashin saurayin jin kansa na daÉ—a kumbura, tare da ji a ransa zai aikata komai domin cimma burinsa.
Ana tsaka da jimamin mutuwar shugaba a garin, ya ci gaba da tattara sojojin sa na ƙarƙashin ƙasa, da shirya hanyoyin da zai bi gurin kawar da dukkanin wanda ka iya kawo masa tangarɗa.
Ganin babu abin da ake yi a farkon littafin, ban da tsagwaron zalunci, zubar da jini da rashin tausayi ko imani, tsananin ƙiyayya da kisan kai a tsakanin 'yan uwa, duk don kowa yana kwaɗayin ɗarewa gadon mulki.
Ga bautarwa ta fitar hankali ga na ƙasa ba tare da afuwa ko sassauci ba, sai Nana ta ji gaba ɗaya littafin ya ishe ta, ba ya yi mata daɗin karantawa, har ma gara na tarihin Buda a kan wannan.
A hankali ta buɗe idonta, da ya yi mata nauyi, ta ga gari ya yi haske, ta shafa gefenta ta ji babu Muhsin, kawai ta yi zaton ko Nene ce ta goya shi, dan idan Nene na nan, tsakaninta da Muhsin shayarwa ne kawai, ita take yi masa komai kamar ita ta haife shi. Tana ɗaga kai ta ga wannan mahaukaciyar, riƙe da Muhsin a hannunta, gefenta ga wannan ƙwarangwal ɗin baƙi ƙirin da shi kamar an gasa shi da wuta.
Ihu Nana ta saka a cike da matuƙar razana, ba wai dan ta ga ƙwarangwal ɗin ba, sai ganin ɗan ta a hannun mahaukaciya ga aljani a bayanta yana ta lasar jinin jikin mahaifar da ke ɗauke da zaren cibi.
Ayshercool
08081012143
66
Nece ce ta fito hankali a tashe, ta shiga É—akin da Nana take ciki, ta tarar da Ashura a tsaye rungume da jaririn Nana.
A matuƙar fusace ta ƙarasa ta karɓe Muhsin, ta ajiye shi a kan katifa, ta ce "Uban me ya shigo da ke ki ka ɗauke shi?"
Cikin tsoro ta girgiza kai ta ce "Babu komai"
"Uban me ki ka yi masa?"
"Wallahi ban yi masa komai ba"
Nene ta shaƙe ta, ta ce "Ki gaya mini me ki ka yi masa?"
Cikin kuka ta ce "Wallahi ba abin da na yi masa"
"To me yasa ki ka shigo?"
"Wallahi son shi kawai nake yi"
"ÆŠan ki ne da za ki ce son shi ki ke yi, wani abin za ki yi masa kenan" cikin kuka ta ce "A'a Nene"
Nene ta ce "Wallahi na sake ganinki a gidan nan, sai na yi miki shegen duka, babu ke babu jaririn nan"
Nana ta saka hannu ta ture Nene, ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri ki daina dukanta, ai ta ce babu abin da ta yi masa"
Nene ta ce "Ba dan kin farka ba fa? idan ta yi masa wani abin, ni ina banÉ—aki ke ki na bacci fa?"
Nana ta ce "In sha Allah babu abin da za ta yi masa. Zo mu je na raka ki gida"
Nene ta ce "Nana ki rabu da ita ta tafi gidan"
Nana ta ce "Nene zan raka ta, ni duk inda na ga mai irin larurar nan, tausayi yake bani"
Nene ta ce "Can ta matse muku ke da ita, ku je can ku ƙarata, ni dai na sake ganinta a gidan nan, ta taɓa yaron nan, sai na yi mata shegen duka da itace"
Nana ta kama hannun Ashura da ke ta rarraba ido, suka fita daga gidan.
*****
Hajiya Sa'a ta tattara hankalinta a kan Abba da yake zaune a gabanta a bedroom É—in ta.
"Magana nake yi maka, ka É—ago ka kalle ni, mene ne a tsakaninka da yarinyar nan Jamila?"
Ya ce "Ba komai"
"To ka buÉ—e kunnenka da kyau ka saurare ni, na sanya katanga a tsakaninka da ita, babu kai babu ita, kar ka kuskura na ji wata magana a tsakaninka da ita, kuma matar aure na samo maka ita, zan baka lambarta ka kira ta ku gaisa. Ka je ku gana, kuma nan kurkusa za a yi komai a gama. Ka fita daga harkar Jamila, ka fita daga harkar ta na gaya maka na kuma nanata maka, idan ba haka ba daga kai har ita ba za ku ji daÉ—in abin da zai biyo baya"
Ya jinjina kai jiki a sanyaye ya ce "To in sha Allah zan kiyaye"
"Tashi ka bani guri" ya yinƙura ya tashi jiki a sanyaye, ya fice daga ɗakin, zuciyarsa na wani irin zafi. Bai taɓa zaton za ta nuna adawarta da maganar haka ba, ganin yadda take da Jamila.
Ko da ya tafi É—akinsa, kiran Jamila ya shigo wayarsa, jiki a sanyaye ya É—aga wayar ya ce "Hello Jamila"
"Jamila kuma, yau ba ƙanwartaka?"
"Afuwan a yi mini afuwa"
Cikin damuwa Jamila ta ce "Yaya lafiya kuwa?"
"Lafiya ƙalau, ina fatan kin je gida lafiya, ba ki bari na dawo na mayar da ke ba"
"Ina sauri ne, kuma ba na son wahalar da kai gaba É—aya. Ko dai Mummy ta yi maka magana a kan ka daina kula ni ne?"
Da sauri ya ce "A'a ai kin san ba za ta hana ba ko kaÉ—an"
Jamila ta ce "To shikenan, amma dan Allah in anjima ka zo na ganka"
Ya yi murmushi ya ce "Ni ki ke son gani?"
"Eh mana, ko na haƙura?"
"Ina ni na isa, ina yin sallar isha'i za ki ganni a bar ƙaunar Abba"
"To abin ƙaunar ƙanwarsa, sai ka zo" ya sauke wayar yana murmushi, sai dai yana sauke wayar ya ɗan yi shiru cikin damuwa, bayan tuna abin da Mummyn ta gaya masa na kashedi.
****
Muhsin ɗin Nana tamkar ana hura shi, saboda girma ya cika ya yi fam. Ga shi fafur Nana ta ƙi bari a yi masa aski, ta cewa Nene babansa ma ba ya aski, dan haka a bar masa sumarsa.
Nene ta fara jinginar da shi, a tsakanin fululluka tana koya masa zama.
Nene ta ce "Nana bari na hanzarta na fita, ki kula da yaron nan dan Allah, ban da shiririta, ko ki ƙyale shi yana kuka ki yi masa banza"
Nana ta ce "To Nene ki goya abinki ki tafi da shi mana, tun da kullum ba na yi muku abin arziki"
"Kya dai ji da shi, ni dai na gaya miki, kuma wallahi mahaukaciyar can ta shigo, ki ka ɗauki yaron nan ki ka bata, sai na ɓata muku rai daga ke har ita"
Nana ta ce "Ni dai ba wannan ba, Nene so nake na fara bin ki gurin sana'ar nan, zaman gidan nan yana damuna, ba akin fari babu na baƙi"
Nene ta ce "Nima na yi wannan tunanin Nana, amma bai kamata a ce kina matar aure mu din ga fita bakin titi babu iznin mijinki ba, kin san halin maza wasu ba kirki ne da su ba, mussaman ke ga ƙuruciya ma. Sam ba mutuncinki ba ne ba, dama jira nake yi Muhsin ya ƙara ƙwari, na nema miki ko gurin ɗinki ne ko makamancin haka, ki din ga zuwa sannan mu ga ta ina za mu fara laluben mijinki, amma tun da Muhsin ya yi ƙwari, mu fara lalubawa zaman haka ba zai yiwu ba, motsi ya fi laɓewa ai"