← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 78

Sashe 49

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Ina sauran ma'aikatan gurin nan?" Ta ji wata murya ta daki kunnenta, da ba ta san mai ita ba.
Ta É—aga kai ta kalli matashiyar matar, doguwa fara jawur, mai kama da Al Hussain.
Kawai ta mayar da kanta ta ci gaba da aikin gabanta.

"Ke ba kya ji ina magana ne?"

Nana ta É—ago kai ta ce "Su na zuwa"

Nana na rufe bakinta, sai ga Adama ta shigo, ita da sauran ma'aikatan.

Wata irin rikicewa suka yi, suka hau tsuma su na gaida matar.

"Wace ce wannan? Da ba ta da mutunci ba ta da ɗa'a, nake magana tana bani amsa a wulaƙance" ta yi maganar tana nuna Nana.
Nana a ranta ta hau mamakin wane wulaƙancin ta yi mata, ita da ta zo guri babu sallama babu gabatar da kai, koma wace ce ba zai wuce ita ce mai gurin da ake faɗa ba. Nana a ranta ta ce "Koma wace ce ke, Allah ya fi ki" sai dai ba ta sake ɗaga kai ta kalle su ba, ta ci gaba da yankan kabejin hannunta.

Ayshercool
08081012143.
69

Adama ta risunar da kai ta ce  "Ki yi haƙuri ranki ya daɗe, mu ma haka muke ta fama da ita mu ma, amma ki yi haƙuri baƙuwa ce"

"Baƙuwa kuma ba ta iya magana ba, baƙuwa daga ina?"

Raliya ta ce "'yar Nigeria ce"

" 'yar Nigeria, waye ya saka Al-Husssain ɗaukar wata 'yar Nigeria, dama haka 'yan Nigerian ku ke, ba ku da mutunci ba ku san me ku ke yi ba?" Maganganun matar sun soki zuciyar Nana, tamkar ta mayar mata da martani ta ce "Ku a Nijar ba ku san muhimmancin sallama, da girmama na ƙasa da kai ba" Sai dai ta yi shiru ta ci gaba da aikin gabanta. Haka ya ƙara tunzura matar ta fita fuuuu tana bala'i tana sai Nana ta bar aiki a gurin.

Matar na barin gurin Raliya ta kalli Nana ta ce "Allah ya ƙara, idan kina cin ƙasa ai ki kiyayi ta shuri, yau kin taɓo abin da ya fi ƙarfinki, kin yi a bakin aikinki"

Babban abin da ya ɗaure musu kai, bai wuce yadda Nana ta ƙara yin burus, ta ci gaba da aikin gabanta.

Adama ta ce "Anya yarinyar nan ba mahaukaciya ba ce kuwa?"

ÆŠayar ta ce "Ko ta mayar da mu mahaukata ba. Amma idan haukan take ji, ai Hasna babarta ce"

Wata matashiyar mata ce ta shigo, sanye da uniform a jikinta. Ta yi sallama suka amsa.
Ta ce "Ina Nana?"

Nana ta ce "Ga ni"

"Ki zo ana neman ki a ofishin Al Hussain"

Ta ce "To gani nan" ta yi maganar tana ajiye wuƙar hannunta, ta wanke hannunta ta bi bayan matar.

Sai dai har matar ta yi gaba ta bar Nana, da ƙyar Nana take iya ɗaga ƙafafuwanta, saboda matsanancin nauyin da ta ji sun yi mata, ga sanyi da ya fara ratsa ta ta ko ina.

"Ya hayyu ya ƙayyum. Allah ka taimake ni, Ƙaisar kar ka yi mini haka mana"  Ta furta a hankali zuciyarta na bugawa.
Ta saka hannu ta tura ƙofar ofishin. A tsaye ta tarar da matar ɗazu, tana zazzaga masifa, Al Hussain yana zaune yana kallon ta.
Sai dai Nana ta yi turus, ganin Ƙaisar a zaune a jikin na'urar sanyaya guri, da ke cikin ɗakin.

"Nana ƙaraso mana" muryarsa ta dawo da Nana hayyacinta. A hankali ta ƙarasa ya ce ta zauna a kan kujera.

"Al Hussain ka na da lafiya kuwa? Yarinyar ta yi mini rashin mutunci, ka ce ta zauna a kan kujera?"

Ya ce "A'a Hasna, na fa san halinki, kuma a aikin da Nana ta yi da mu na É—an lokaci, ba ta da matsala sam. Nana meyafaru ne?"

Nana ta buÉ—e baki za ta yi magana, Hasna ta tari numfashinta ta ci gaba da masifa.
Al-Husssain ya daki tebur ya kalli Hasna, hakan ya sanya ta yin shiru tana harar Nana.
Nana ta ce "Ban san wace ce ba ne, ta yi haƙuri"

Hasna ta daki tebur ta ce "Ka gani ko, garin kwashe-kwashe ka kwaso mara mutunci, to wallahi sai ta bar gurin nan, tun da ba na ubanta ba ne"

Al-Husssain ya ce "Tsakani da Allah, Nana mutuniyar kirki ce mai girmama mutane, ba na tunanin za ta yi miki wani abu na rashin mutunci. Nana ki je ki ci gaba da aikinki" Ta jinjina masa ta kalli Hasna ta ce "Ki yi haƙuri, ban san wace ce ke ba, ba ki gaya mini ba, na zata a cikin abokan aikina ne kaw...

"Ke, na yi miki kama da wadda za ta zama abokiyar aikinki?. Za ta ci gaba da magana Nana ta tsare ta da ido, sai ta rikice gaba É—aya ta rasa abin da za ta ce.

Al-Husssain ya ce "Maza jeki ki ci gaba da aikinki"

Nana ta miƙe tsaye, kawai ta ji jiri ya ɗebe ta, ta yi saurin riƙe kujerar. Al Hussain ya miƙe da sauri ya ce "Ba ki da lafiya ne?"
A sanyaye ta ce "A'a jiri nake ji ne"

"Idan ba za ki iya aikin ba, ki je ki kwanta ki samu hutu"

Nana ta ce "A'a zan iya ma, in sha Allah"

Ta lallaɓa ta fita daga ofishin, sai dai tana jiyo Al Hussain yana ce mata, ki yi a hankali kin san mu na da baƙi, idan kuma ki ka ci gaba da hayayaga mutuncinki ne zai zube, wannan halin naki babu abin da zai janyo miki sai raini.

Gaba Nana ta yi, tana bin bango, sai dai sosai ta ji Duniyar na juya mata.
Ta lallaɓa ta koma ɗakinsu da ƙyar, sai dai a ɗakin ta din ga jin wani irin sauti mara daɗi, ga sanyi tana ji amma numfashinta tamkar zai ɗauke.
Ta buÉ—e tagogin É—akin, kasancewar saman bene ne, ta hango wasu irin manyan motoci a harabar gurin. NaÉ—in kan mutanen ya sanya ta tabattar da Buzaye ne, sai dai suna sanye cikin kaya na alfarma.
Nana ta zuba musu ido, tana son ganin fuskar ɗaya daga cikin mutanen da aka buɗewa wata danƙareriyar mota. Wanda haka kurum ta din ga jin kamar akwai wani abu mai matuƙar muhimmanci da yakamata ta sani game da mutumin, da ba ta san ko wane ne ba, duk da yanayin ƙirar jikinsa ba irin na Sayyid ba ne. Wata irin ƙara ta din ga ji cika mata kunne. Ta dafe kunnenta, ta durƙusa hawaye na bin fuskarta. Yanayin gaba ɗaya mara daɗi ne, rashin daɗin da ba za ta iya misaltawa ba sam.
Dariyar Giyaz ta din ga ji sama-sama, a hankali dariyar ta cika ilahirin É—akin.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil, wa hifzan min kulli shaiÉ—anin marid" shi ne abin da ta furta a hankali.

"Asmy" ta ji muryarsa cikin karkarwa, yayin da ƙarar iskar sahara take kaɗawa.

A galabaice ta ce "Sayyid"

"Ma vie"

Ta sake cewa "Na'am Sayyid, na fara sarewa, ina jin kamar ba zan yi nasara ba, ba zan ganka ba, na fara karaya." Ta yi maganar tana kuka.

"A'a kar ki karaya, kar ki yi mini haka, ina buƙatar ki dan Allah"

A hankali take sauke numfashi, idanunta a lumshe ƙirjinta ya yi nauyi kamar numfasihinta zai ɗauke.

*****

Daren da Jamila ba za ta taɓa mantawa da shi ba, ya sake maimaita kansa.
Daren da ta zama ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar asiri, daren da aka lalata rayuwarta a matsayin maraba da shiga ƙungiyar.
Chapter 49 · 0% Book details