Sashe 36
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fadila ce zaune a kusa da Alhaji Fatuhu, gefenta kuma jaririnta ya yi wayo, yana ta bacci.
Ta miƙa masa lemon da ta haɗa masa a kofi, ta zuba masa ido, yana sha a hankali.
A ranta take faÉ—in "Ubangiji Allah ka bawa wannan bawa naka lafiya, albarkacin ayoyin Alkur'ani'
Ta kalle shi tsaf, ya yi rama ta ban mamaki, dan ma yanzu ya ɗan ciko, ba kamar da ba" ya shanye ya miƙa mata kofin, ta karɓa ta ajiye a gefe. Ta matsa kusa da shi tana ɗan ƙara gyara masa filulluka.
Ya ce "Na gode sosai, Allah ya yi miki albarka, ya raya miki Muhsin"
Ta ce "Amin Daddy"
"Da lafiyata ƙalau, da mun yi sauri, nan da wata wata taran, ki kuma haifo mana wani" Murmushi ta yi ta ce "Allah ya baka lafiya ya tashi kafaɗunka" ya amsa da Amin yana riƙe hannunta cikin nasa da ya yamuste kamar na tsoho.
Hajiya Suwaiba ta ce ta shigo É—akin, Fadila ta É—an zabura ta ja da baya.
Hajiyar ta ja tsaki ta ce "A hakan ma da kake wani abin ka ke ƙoƙarin yi, ai sai ku rufe ƙofa kar yara su faɗo, a lalata mini tarbiyyar yara"
Fadila ta ce "Haba Hajiya, abu na ba shi ya riƙe hannuna, and laifi ne dan ya riƙe hannuna wani abin ki ka ga na yi?"
"Kar ki yi mini rashin kunya dai? Idan ma yin ku ke, ku ƙarata ku da Allah"
Ran Fadila ya yi mummunan ɓaci, ta yinƙura da niyyar, ta ɗauki ɗan ta ta bar ɗakin, amma ya riƙe hannunta, ya hana ta tafiya. Hajiya Suwaiba ta gama bala'inta ta tafi ta bar su.
Idan ya ce Suwaiba ba ta ƙoƙari a kan rashin lafiyarsa ya yi ƙarya, tana iyakar ƙoƙarinta amma wasu lokutan tana da saurin ƙosawa gashi haryanzu azababben kishi na ɗawainiya da ita.
****
Gidan Maijidda kuwa, Iliyasu bai taɓa tsammanin,  Maijidda na da taurin kai haka ba. Gaba ɗaya ta tarkata shi ta yi watsi da shi. Iyakarta da shi, ta girka Abinci ta ba shi, idan buƙatarsa ta tashi, ya yi kiɗansa ya yi rawarsa. Gaba ɗaya ta sanya damuwa a ranta, ta rame sosai da sosai, dan ko Abincin kirki ba ta iya ci, kusan kullum cikin kuka take, ko ta zauna ta yi shiru. Ga shi ya lura 'yan uwanta sun fara gajiya da sinturin kai ƙararta da yake yi, ba yau ba gobe.
"Anya ka na ganin haka rayuwar Imam za ta ci gaba, duk lokacin da ya farka sai ihu da fizge-fizge, sai dai a yi ta yi masa allurar da zai yi bacci? Idan aka bar shi a haka rayuwarsa fa ta nakasa kenan har abada"
Sultan ya ce "Abdou, ni kaina ala'amarin nan yana damuna, na rasa yadda zan yi. A ɓangaren ƙwaƙwalwar ma, babu wani gamsashshen bayanin abin da ya faru da shi. Ta ɓangarenka ma babu wani nagartaccen bayani daga bakin shi yaron, balle mu ji ko wani abin ɗin aka yi masa".
"Sultan, ka ƙi bayar da dama a sanya 'yan doka, su maguza yaron nan, ya faɗi gaskiya ko ya ƙi Allah"
Sultan ya girgiza kai ya ce "A'a, duk ranar da Imam ya samu lafiya, muddin ya ji labarin an cuzguna masa, zai yi fushi, kuma zai ji babu daɗi kai ka san irin alaƙar da take a tsakaninsu."
"Amma yanzu ai yanzu a kan gaɓar bincike a ke Sultan. Amma tun da haka ka ce Shikenan, za a ci gaba da bin komai sannu a hankali"
Sultan ya amsa da "Yauwwa"
BAYAN WATA ÆŠAYA
Sabo turken wawa, rashin ganin Ƙaisar da Nana ta daina yi, ya sanya ta din ga tunanin ko wani abin ne ya faru da shi.
Sai dai yau kwatsam cikin barcinta, ta ganta a cikin Librarynsa. Sai dai ta gurin ƙwalam babu litatafai babu kayan rubutunsa sai mudubin da yake nuna mata abubuwa a cikinsa.
Ta waiwaya ta lelleƙa, amma babu Ƙaisar babu alamunsa.
Wani littafi guda ɗaya tal, ta hango a kan teburin rubutun Ƙaisar, ta ƙarasa ta nufi teburin ta ɗauki littafin.
Bangon littafin na fatar wata dabba ne. Dan har da gashi-gashi a jiki. Yanayin bangon littafin ya sanya ta yi tunanin, ko mene ne a rubuce a littafin ba yanzu ya faru ba, ya kwana biyu da faruwa. Littafin ba wanda ta karanta tarihin su Lanti ne a ciki ba, wani ne daban.
Hoton wata alƙarya ce, da ke tsakanin duwatsu, da aka rarake aka samar da katafariyar daula.
Ta buÉ—e littafin shafin farko, ta fara karantawa.
"Tushiya..." Shi ne abin da ke rubuce a shafin farko na littafin.
"Ka sani,har abada da ɗan Gari a kan ci gari. Kuma ba a cimma buri da tausayi ko jin ƙai. Wannan mataki na farko kawai ka cimma, na sharar fagen cimma nasararka.
Ka na buƙatar sanya wa mutane tsoronka, da shakkarka domin cimma burinka, kuma hakan ba zai taɓa yiwuwa ba sai ka zubar da jini, duk wanda ya biyo ta hanyarka ka datse rayuwarsa, kar ka damu da adadin rayukan da za a rasa, ka zubar da jini ba ƙaƙƙautawa har sai mutane sun fara jin fitsari a duk lokacin da aka ambaci sunanka.
Ka kame mutanen gefen alƙaryar nan, ka mayar da su bayi, matansu ka mayar da su naka, mazansu su zama bayinka, ka yi amfani da ƙarfinsu da fikirarsu ka gina alƙaryar da babu wani mahaluki da zai iya ɗaga maka yatsa, kar ka gushe kana aikata hakan, har sai buƙata ta biya.
Zaka kasance cikin sanyawar albarkar Aljanu, za su baka dukkanin goyon bayan da ka ke buƙata kar ka saurarwa kowa"
Cikin damuwa mutumin ya kalli mai maganar ya ce "Ka sanya ni na kashe mahaifina da hannuna, yanzu ga wani abin ka sake zuwar mini da shi, kar ka manta ina da 'yan uwa maza, ba za su zuba mini ido, duk na yi wannan ba, na É—auki abin da ba nawa ba, alhalin su na gaba da ni ba"
Ji ta yi mudubin gurin yana wata irin ƙara tamkar zai tsage, a take ta ajiye littafin ta nufi mudubin tana kallonsa.
Wata irin wuta ta gani tana ci a cikin mudubin. Wutar mai matuƙar ban tsoro saboda yadda take ci. Wani mashi ta gani a soke a jikin wani ƙwarangwal, ɗaya gefen mashin an yi rubutu a jikin wani abu mai kama da takarda. Ta ƙara matsawa domin karanta mene ne a jikin takardar amma ta ga mudubin yana hayaƙi yana baƙi yana washewa.
A kusa da wutar ta ga wani abu mai kama da mutum, a lulluɓe da wani mayafi yana zuba wani abu a cikin wutar wanda yake ƙara sanya wutar ƙara balbala.
Imam... ta iya gani a rubuce a jikin abin, mai kama da takarda, a gaban Imam ɗin akwai wani sunan, sai dai ba ta iya karanta sunan ba. A jikin wutar ta ga taswirar fuskar Sayyid yana jijjiga jikinsa na ƙonewa yana kururuwa yana kiran sunanta.
Wata irin zabura ta yi ta kuma tunkarar mudubin gadan-gadan, mudubin ya yi wata irin tsawa ta ja da baya ta faɗi ƙasa.
A gigice Nana ta farka, ta haɗa uban gumi ta yi sharkaf, ga wata irin ƙullewa da cikinta ya yi haɗi da mararta. Ta yinƙura da ƙyar ta tashi ta tafi banɗaki, a zatonta fitsari take ji, ko kuma bayan gida, amma ta ji ba bayan gida take ji ba, ta fitsarin amma still mararta kamar an saka wani abu an ɗaure mata. Ta yi alawala ta koma ɗakinta.
A zaune take salla saboda yanayin girma da nauyin da cikin ya yi. Ta kasa tuna abin da ta gani, sai iya wutar nan da wannan tsawar da mudubin ya yi su kawai take iya tunawa.
"Allahumma ajirni mina narr"
Ta maimaita da tuno yadda ta ga wutar nan. Ta ji sam mafarkin nan bai yi mata daÉ—i ba, ko mene ne babu Alkhairi a tattare da shi sam.
Sai da gari ya waye, sannan ta samu afuwa daga wannan ɗaurewar da mararta ta yi da bayanta. Jikinta babu daɗi, haka nan take lallaɓawa ta daure kar Nene ta fuskanci wani abu.
Nana ta dama kunu da kanta, ta tashi tana tafe da kyar, Nene ta ce "Nana wai cikin nan naki wata nawa ne?"
Ta É—an yi shiru ta ce "Ina ga bakwai ne"
"Anya kuwa Nana, kalli yadda ya cure guri ɗaya ya yi ƙasa sosai a ce cikin nan na watanni bakwai ne kawai? Amma ban sani ba ko biyu ne. Yakamata ma mu je Asibiti a duba ki, ni wallahi na ma manta shaf ana zuwa awo. Ko danmu lokacinmu ba awon ake yi ba oho" Nana dai ta yi murmushi kawai tana jin yadda ɗan yake ta motsi yana danno ta.
Da ba rufe cikakken sati, mijin Hajara bai zo gidan ba, dama yana fargabar kar Nana ta kasa zama da Nene, saboda faÉ—anta, kuma cikin ikon Allah ya ga lafiya kalau suke zaune. Dan haka ya rage zuwa sosai.
Tun da Nana ta je gidan, Neme ba ta barin ta ta fita, saboda ta ce mata tana da aure, kuma tana yawan gaya mata, ba a son mace mai ciki ta din ga yawo jama'a su na kallonta, saboda baki da ido.
Ma'aikatan Nene duk sun saba da Nana, duk a tunaninsu 'yar uwatta ce, sai dai sukan tambayi Nana, ya aka yi hausarta ba irin tasu ba.
Wasu lokutan sai Nene ta cewa Nana ta zauna a É—aki kar ta fito, dan haka babu inda Nana ta sani a garin.
Nana ta kwana huÉ—u, tana fama da wannan ciwon a tsaitsaye.
Sai dai na yau ya fi na kullum, dan sam ba ta yi bacci ba, kuma ba ta gaya wa Nene ba.
Da safe kan Nene ta fito, Nana ta yi shara ta wanke banÉ—aki, ta É—ora abin karin kumallo.
Ta kuwa sha faÉ—a a gurin Nenen, sai dai ita ko a jikinta.
Sun gama karyawa, Nene ta shiga É—aki, ta ji Nana na kiran sunanta, cikin mawuyacin hali.
Nene ta fito da sauri ta ce "Nana lafiya?"
"Nene yoyon fitsari nake yi, ba na iya riƙe fitsari" gaban Nene ya faɗi ta ce "Kamar yaya?"