← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 78

Sashe 27

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ikon Allah, na yi mamaki da na ji zuwa ta yi babu sanarwa, tare da mijin suka zo?"

Maijidda ta numfasa ta ce "A'a, matsala ma aka samu, ba a san inda mijin nata yake ba"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, garin yaya ina ya tafi?"

"Wallahi ban sani ba, na dai ce ta zauna a nan, kafin nu ga abin da Allah zai yi. Ashe rashin lafiya ya sha, yarinyar nan ba ta taɓa gaya mini ba. Ga babanta bai karɓe ta ba, ƙarshe ma sai Buda ta koma ta yi jinyarsa, kuma dai ma ya tafi ba a san inda yake ba"

Cikin jimami Saude ta ce "Kai subhanallah, abin nan bai yi daÉ—i ba, yanzu meya same ta haka?"

"Iska ne ya buge ta, na ba ta abinci ta karya, ta fara bacci kawai ta tashi wai mijin ne yake kiranta. Ashe haryanzu tana fama da wannan matsalar. Wallahi Adda na yi dana sanin biye wa Iliyasu na watsar da yaran nan." Ta yi maganar hawaye na cika mata ido.

"Ki yi haƙuri, amma yanzu ya ku ka yi da shi?"

"Hmm mu na nan muna ta bugawa, wai sai ta bar gidan nan, ni kuma Nana ba za ta bar gidan nan ba, sai dai mu tafi tare"

A É—an tsorace Adda ta ce "A'a Maijidda, idan da matsala, a kaita gidan Fati tun da tana da yalwar guri, ko gurin Yakumbo,kar ku samu matsala"

Ta girgiza kai ta ce "Ni na ke son kula da Nana da kaina. A cikin su ban san wanda zai ji ƙan wani ba, dukkaninsu su na buƙatata".

Nana ta farka tana ɗan yin miƙa, ta cewa Maijidda fitsari za ta yi, ta raka Nana banɗaki ta je ta yi fitsari, ta saka ta ta yi alwala ta koma ta kwanta.

Har zuwa yamma Adda na gidan, sai daf da magariba ta tafi, Nana kuma ta wartsake sai ciwon jiki da mararta da ke É—an murÉ—awa.

"Nana, ranar Litinin in sha Allah za mu je Asibiti, a fara yi miki awo, kuma zan duba gurin masu magungunan islamic É—in nan, mu je a duba ki" Nana dai ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Da sallar Isha'i, Baban su Walida ya dawo, tun da ya hangi Nana a ɗaki, ya turnuƙe fuska ya kalli Mai Jidda ya ce "Me na ce miki a game da yarinyar nan?"

"Baban Walida, ba a yi wa ɗa mugunta, dan Allah ka yi haƙuri ka bar Nana a gidan nan, ka ga 'yan uwanta ma duk ba su santa ba, ba su saba ba. Kuma ba a san me gobe za ta haifar ba. Wataƙila ita ce mai tallafar rayuwar ƙannen nata nan gaba."

"Ni ba nusari ne kamar ubanta ba, ni zan tallafi rayuwar 'ya'yana. Ba na buƙatar ko sisinta a kan yarana. Ta koma gidan mijinta ko gidan ubanta, idan ba haka ba sai dai ki zaɓa, ko ta bar mini gida, ko kuma auren ki."

Kafin ya rufe bakinsa ta tari numfashinsa ta ce "Na zaɓi 'ya ta, zan tafi tare da Nana, ko a daji ne na rayu da ita na kula da ita. Tun da ba dan wahala da bautarka da ta 'ya'yanka kawai Allah ya yi ni ba. Ba ka da kara Iliyasu. Nan har 'ya na riƙe maka na aurar da ita ban yi mata mugunta ba. Har 'ya'yan 'yan uwanka ka kawo mini na riƙe, ban taɓa muzguna musu ba, na riƙe maka, nawa 'ya'yan ne na banza kenan? Ƙiri-ƙiri ɗan da na durƙusa na haifa ya tsane ni, saboda yana ganin na kawo su Duniya amma ban damu da su ba. Su 'ya'yan da na riƙe maka haifar su na yi? Ko kuma dolena ne su, ni 'yar guda ɗaya ka gaza yi mini kara a kanta? To ka sani duka yau duka gobe shi ke sanya baƙin ba'auzine yin tawaye. Zan zube maka yaranka na ɗauki 'ya ta na tafi da ita, na kula da ita. Ka kwaɗa gidan ka cinye da kai da 'ya'yan naka"

Cikin matsanancin mamaki ya ce "Maijidda, ni ki ke gaya wa wannan maganganun?" Cikin ƙunar rai ta ce "Na faɗa ɗin, shekara nawa na rayu da baƙin cikin rashin ganin 'ya'yana, kullum na motsa zargina ka ke da tsohon mijina. Ƙaddarar haihuwar yaran nan biyu ta sanya ban aure ka da fari ba na fara auren sa, amma a kan dalilinku marasa tushe balle makama kun azabtar da ni da nesan ta ni da yarana. Wallahi wannan karon na zaɓi 'ya ta"

Kamar zubar wuta, haka Nana take jiyo cece kucen su. Dana sanin zuwa gidan ya cika mata zuciya. Tabbas ba za ta so mahaifiyarta ta kashe aurenta, da wannan gayyar 'ya'yan saboda ita kaÉ—ai ba, idan ta bari hakan ya faru ba ta yi musu adalci ba baki É—aya. Zurfin tunanin da ta tafi, bai bari ta gama jin yadda rigimar ta su ta kaya ba. A cikin daren bayan gari ya yi tsit, ta tashi ta haÉ—a kan kayanta cif.
Ta laluba jakunkunan yaran na makarantar boko, ta samu biro da takarda ta yi rubutu, ta ninke ta ajiye a kan katifar ta.
Da Asuba, Mama ta zo ta tashe ta, ta yi alawala ta yi sallar Asuba. Ganin yaran na ɗaya ɗakin su na salla, Mama ma tana bedroom ɗinta, tana salla, ya sanya ta lallaɓa ta ɗauki jakarta ta fice daga gidan.
Ta din ga zumbuɗa sauri, tamkar za ta tashi sama, ga faggon kaya. Tafiyar ƙafa ta ci sosai da sosai, har sai da gari ya yi haske, masu abin hawa suka fara fitowa, ta tari wani ta ce ya kai ta tasha. Yana kai ta tasha, ta yi sa'a an yi lodi saura gurin mutum biyu, tare da wata mata suka shiga tasha suka nufi babbar tashar Bauchi.
Daga babbar tashar Bauchi, ta hau wata motar, duk da zuciyarta na raya mata kamar matakin da ta É—auka ya yi tsauri, wata zuciyar kuma na raya mata shi ne mataki mafi cancanta da za ta É—auka, mussaman idan ta tuna yanayin yadda ta yi mafarkin Sayyid.
Wayarta ta ciro, ta shiga lambar Ummi, ta rubuta mata saƙo, sai da ta tabattar ya tafi, sannan ta kashe wayar, ta cire layinta daga cikin wayar.

Gari ya ɗan fara haske, Baban su Walida ya fice, a matuƙar zuciye, ya yanke shawarar tafiya ya kai ƙarar ta, tun da dama ya san ya saba samun goyon baya, ba ga taɓa kai ƙararsa ba, amma shi ya kai ta ta, ya fi sau shurin masaƙi.
Su Khadija har sun fara ƙiriniya a tsakar gida, a zuciye kasancewar da takaicin ubansu ta kwana ta daka musu tsawa, ta ce su koma ɗaki, kar su tashi Nana. A zaton ta Nana tana cikin ɗaki tana bacci.

Jamila ce zaune a gidan Ummi, tana jajanta abubuwan da suka faru da Nana, ba tare da ta san ma hakan ya faru ba.

"Wallahi Ummi da an sanar da ni zancen matar nan, da suka ce Nana mayya ce, wallahi da sai na saka an rufe ta, sai na ja shari'a da su har gaban Alƙali, sun san girman sharrin maita kuwa?"

"Hmm ke dai a yi sha'ani, ga shi Nana ta bar gidan, amma an ce Haryanzu tana kwance babu lafiya matar, ni na fi tunanin ko Aljanun Nanan ne suka yi mata wani abin, tun da ta ce Nana take gani. Jamila wayar Nana fa ba ta shiga, ni kaina sai na shafe sati biyu ban yi magana da ita ba, saboda garin babu network. Haka nan za mu tafi kawai."

Ummi ta shirya, da Jamila Abba ta so ya kai su, sai ta yi wani tunani ta fasa, dan ba ta san a yanayin da za su je su tarar da su Nana ba.
Sai dai Ummi ta sha mamaki da suka isa garin, suka tarar da gidan Nana a garƙame.
"Ikon Allah, ita kuwa Nana ina tafi haka? Ko sun je Asibiti ne?"

Jamila ta ce "Asibiti yau Asabar?"

"To maybe emergency suka je, kin san matsalar Zuciya yake fama. Mu ƙarasa gidan Uwani".

Suka zagaya gurin Uwani, ta yi murna sosai da sosai da ganinsu, sai dai ta hau Jamila da faÉ—an ba sa zuwa sai yanzu, da yake Nana ce a garin.
Ummi ta yi ta bata haƙuri, ta ce sun zo duba Nana ne, sun tarar da gidan a rufe.

"Ohh abin tsiya, ba ma kwa bibiyar halin da take ciki, to Nana tun shekranjiya ta bar Buda, mijinta aka nema aka rasa ko sama ko ƙasa sama da sati biyu, ta ce mini gurin Babarta za ta tafi a Bauchi, babu yadda ban yi da ita mu yi zamanmu da ita a nan, amma fafur ta ce in ƙyale ta, tafiya za ta yi".

Jamila ta ce "Danƙari"

Ummi kuwa "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" kawai take maimaitawa.

"Amma me yasa Nana ba ta dawo gida ba, sai ta tafi Bauchi, bayan ta san halin Baba"

"Baban wofi, uban me zai tsinana mata, ko ta je gurin nasa"

Suka gama jimamin da za su yi, suka tashi suka tafi.

Jamila ta ce "Anya Ummi mu gaya wa Baba kuwa?"

Ummi ta ce "Tun da shi ya haife mu, ba dole a gaya masa ba. Wallahi duk cikinmu babu wanda ya sha azabar ds Nana take sha a rayuwarta, da kin ga yadda take shan wahala da mutumin nan, sai kin tausaya mata, gaskiya idan guduwa ya yi ya bar ta, bai yi wa kansa adalci ba."

Suka ci gaba da jajanta lamarin.

Da suka shigo gari, Jamila ta tafi gida, Ummi ma ta tafi nata gidan.

Mama na ganin Jamila ta dawo, ta fara yi mata tambayoyi, amma Jamila ta yi burus, ba ta gaya wa Mama komai ba.

****
Tare da Kawun Mai jidda Iliyasu ya dawo, yana ta faman bambamin ta lalace, abin da ta ga dama shi take aikatawa.
Sai kuma Adda Saude da suka taho tare, dama sai da ta yi tunanin a samu matsala saboda zuwan Nana.

Suka tarar da Maijidda idanunta jawur, fuskarta babu annuri.
Suka zazzauna a falonta, kawunta ya dube ta ya ce "Mai Jidda ban san ki da rashin ji ba, me yake faruwa ne?"
Chapter 27 · 0% Book details