Sashe 37
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ji na yi kawai fitsari yana bin ƙafata, kin ga" ta yi maganar tana ɗaga wa Nene doguwar rigarta, ruwa na ta bin ƙafafuwanta".
"Nana wannan ai kamar naƙuda ki ke yi, anya ba ruwan mahaufa ba ne?"
Duk da ƙoƙarin da ta yi, za ta yi magana, sai ta kasa saboda wani irin gigitaccen ciwo da ta ji.
Har Nene ta fita suka samo abin hawa, Nana na cikin halin ciwo, ba ta iya gane komai.
Nene ta É—aukko wa Nana wasu kayan, su ka fita suka tafi Asibiti.
A Asibitin ma, da aka tambayi Nana, cewa ta yi cikinta wata bakwai ne, sai dai da aka yi hoton cikin, ya nuna satin cikinta arba'in da biyu.
Likitan ya yi mata tambayoyi, yaushe ta yi al'ada na ƙarshe, ta ce ita ba za ta iya ganewa ba, saboda ɓari kawai take yi a jere.
Ya tabattar mata a cikin ɓarin da ta din ga yi, tun da ba Asibiti take zuwa a duba ba, akwai wanda bai fita ba ya ci gaba da girma, dan haka naƙuda take yi.
Gaba ɗaya Nene ta rikice, kamar 'yar ta ce za ta haihu, sai a lokacin ta fita, ta sayo kayan jariri da ba ta san ma na wani jinsi ba ne, da ɗan abin da za a buƙata.
Ma'aikata na tsaye a kan Nana, su na ƙoƙari, duk ta galabaita ma ta kasa nishin can ta ce "Ya hayyu ya ƙayyum" ta yi yinƙuri sai ga kan ɗan ya fito. Ita dai ba ta san yadda aka ƙarasa ba, ta ji kukan jariri ya cika ɗakin.
Likita ta É—ago mata jaririn ta ce "Kalli me ki ka haifa?"
Nana haushi ya kama ta, ta gama shan wannan uwar wahalar ga É—an a hannunta, kuma a din ga tambayarta me ta haifa.
Ta kalli yaron namiji ne, ta ga wani irin shirgegen É—a, kamar É—an wata biyu, sai ta hau mamakin yanzu wannan É—an duk girmansa a jikinta ya rayu, kuma ta É—an wannan gurin ya fito?
Wata irin zabura ta yi ganin fuskar yaron, ta miƙa hannunta gaba ɗaya tana ƙoƙarin karɓe yaron daga hannun Likitar a kiɗime.
Yana kan gadonsa na marasa lafiya a kwance, su ka ga ya yi wata jijjiga sai da gadon ya girgiza kamar an jona masa wani abu, kawai suka ga ya buÉ—e idonsa.
A rikice suka kewaye shi, su na kiran sunansa, sai dai babu wanda ya amsawa sai bin su da yake da ido, kamar ya ga baƙin halittu.
Sultan ya riƙo hannunsa ya ce "Imam ka gane mu kuwa?"
Ya yi shiru yana bin Sultan da kallo.
Abduou ya ce "Ikon Allah, ka ga wannan karon bai tashi da ihun ba, sannu Imam"
Kawai ya yi shiru kamar saƙago, sai ƙwayar idonsa da yake juyawa.
Ayshercool
08081012143
65
Nana kuwa da sauri wata ma'aikaciya ta mayar da ita ta kwantar, ta ce "Kar ki tashi, ai miƙo miki shi za a yi"
Abin da ya razanata kuwa, bai wuce yadda ta ga fuskar Sayyid sak, a jikin ƙaton jaririn nata ba, ga sumar kansa a cike har goshinsa. Ga shi jariri amma hatta girar sa da gashi, haka jikinsa ma akwai gashi sosai.
Aka ɗora mata shi a ƙirjinta, ta yi wata nannauyar ajiyar zuciya, tare da furta Alhamdillah.
Ta sanya hannayenta, ta zagaye shi, ta É—ora hannunta a kansa ta din ga karanto masa addu'oi.
Ta din ga hasko irin murnar da Sayyid zai yi, da ya na nan aka haifi jaririn nan. Hawaye ya din ga gagangarowa ta gefen idonta.
Tana jin Likitan tana tsokanarta da har da kukan daÉ—i, ba za ta bayar da jaririn ba sai an ba ta tukuici mai tsoka. Nana dai ta lumshe idanunta tana murmushi. Aka É—auke jaririn aka gyara ta, aka yi mata É—inki, sannan aka kai ta É—akin hutu.
Bakin Nene ya ƙi rufuwa, ta din ga kallon jaririn. Ta kira wayar su Hajara, ta gaya musu baƙuwar su Nana ta haihu.
Nana ta din ga kallon Nene, da mamakin yadda take ta murnar haihuwar nan, tamkar ita ta haihu.
Sai dai da Nana ta kalli fuskar jaririn sai jikinta ya yi sanyi, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, tana tsoron idan ba ta haɗu da Sayyid ko 'yan uwansa ba, yaya za ta yi mene ne makomar yaron kenan? Ga fargaba da tsoron kar su Ƙaisar su yi masa wani abu, kar shi ma ya yi mummunan gado kamar yadda ta yi.
Haka dai ta É—an saki fuska babu yabo ba fallasa. Bayan awanni shida aka sallame ta daga Asibitin suka koma gida. Aka bata magungunan da suka dace ta yi amfani da su, duk Nene ta biya komai.
Nene ta shiga hidima da Nana sosai, ruwan wankanta da na jariri. Ga lafiyayyen Abinci, Hajara kanta idan za ta zo, sai ta yi girki.
Kowa ya É—auki jaririn Nana, sai ya burge shi.
Ita kanta Nana tasirin Addu'a ne ya sanya Allah ya kawo mata wannan É—aukin da gaggawa, mutanen da ta haÉ—u da su suke sonta.
Kwana na biyar da haihuwarta, ta É—ebo kuÉ—i a cikin jakar gurin Sarkin baka, ta samu Nene ta ce "Nene kuÉ—in nan za su isa a sai wa yaron nan abin yanka?"
Nene ta ce "Kar ki damu, mun yi magana da Auwwalu za a samo abin yanka in sha Allah"
Nana ta ce "A'a Nene, ko ke ki ka haife ni, wahalar da za ku yi mini kenan, kuɗinki na sana'a ne. Ina son a saya masa kaya, a saya masa abin yanka, ko ba za su isa ba, a karɓa a ƙara irin kuɗin mahaifinsa ne, dan Allah kar ki ce a'a" Da ƙyar Nene ta karɓa.
Dan kuɗin da yawa, aka sayo ƙaton rago, Nene har da ɗawainiyar yin girki, ta gayyaci maƙwabtanta suna.
Muhammad Muhsin, shi ne sunan da Nana ta sanya wa jaririn, Muhsin saboda sunan É—an gidan Alhaji Fatuhu da har abada ba za ta manta da mutuwarsa ba.
Maƙwabtan Nene da ma'aikatanta sun yi wa Nene kara, sosai suka tara mata abin alheri na kuɗi, da kayan sakawa kasancewar Nene duk masifarta akwai kyauta, shi yasa take shiri da mutane.
Da daddare Nene ta yi wa Muhsin wanka, Nana ma ta yi ta ba ta jaririn ta shayar da shi. Ta fita tsakar gida ta ƙarasa aikace-aikacenta. Kukan jaririn ta din ga ji, Nene ta ce "Nana ya ne, ki kula da shi mana"
Amma Nana ba ta amsa ba, sai kukan jaririn da ta ci gaba da ji. Ta koma É—akin ta É—aga labule, kawai ta tarar da Nana, ta saka jaririn a gaba tana ta uban kuka.
Hankali tashe ta shiga ɗakin cikin damuwa ta ce "Ke lafiya, kukan me ki ke yi?" Nana ta kasa magana, ta ci gaba da kuka, ga jaririn a kan cinyarta amma ta kasa riƙe shi. Nene ta ƙarasa ta ɗauke jaririn ta ce "Ba za ki illata ɗan mutane ba, maza yi ta kukan, idan kin gama kya kula da shi" Nene ta goye shi a bayan ta, ta ci gaba da sabgoginta ta ƙyale Nana.
Ba ta sake kula Nana ba, sai da ta yi kuka mai isarta ta gaji.
Nene ta gyara shimfiÉ—arta, ta kwantar da Muhsin da ya yi bacci.
Ta koma gurin Nana, ta zauna. "Nana" ta kira sunanta.
Nana ta É—aga kai ta kalle ta.
"Ki gaya mini tsakaninki da Allah, yaron nan ta hanyar aure ki ka haife shi ko kuwa? Na san tambayar nan tana baƙanta miki rai, amma haƙuri za ki yi da ni"
Nana ta share hawayenta ta ce "Nene ni ba ƙarya na yi miki ba, ina da aure wallahi ɗan sunna ne"
"To Alhamdillah, dama jira nake Allah ya sauke ki lafiya, idan ta kama da kaina sai na je Nigeria, na mayar da ke gaban iyayenki Nana, wannan zaman naki kina yarinyar mace, ba kamace ki ba"
"A'a ba zan koma ba Nene"
"To saboda me?"
Hawaye na ambaliya a fuskar Nana ta ce "Sai na haÉ—u da Babansa, ko danginsa. Ai sun san na taho neman sa"
Nene ta ce "To a wane garin baban nasa yake?"
Ta girgiza kai ta ce "Nima ban sani ba"
"Kamar yaya? Meye sunansa da garin da yake ko hotonsa, sai a taya ki cigiyarsa" Nana ta sake girgiza kanta ta ce "Ban sani ba"
"Wacce daga cikin tambayar ce ba ki sani ba?"
"Nene ban san garin su ba, ban san sunansa ba, kuma ba ni da hotonsa"
Nene ta ce "Ke kar ki raina mini wayo mana, na kwaɗe ki, ta yaya za ki auri mutum ba ki san sunansa ba, ba ki san sunan garinsu ba kawai ki ka kamo hanya ki ka taho? Me ki ke ɓoye mini ne?"
Nana ta ɗan yi shiru ta numfasa ta ce "Ƙaddara ce ta haɗa ni da shi muka yi aure, ban san sunansa na gaskiya ba, ni ba shi sunan Sayyid. Ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa kuma." Nan Nana ta warware mata komai da ya danganci aurenta da shi, duk da ba komai ta gaya mata ba.
Nene ta yi shiru sannan ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, dama shi ne Sayyid É—in da ki ke ambata idan kina bacci? Amma Nana iyayenki sun yi ganganci. Ke yanzu ko hotonsa ba ki da shi.
Kawai Nana ta É—aga mata kai alamar eh.
"To ai Nana zama guri ɗaya a haka, ba zai sanya a gano shi ba, dole sai an taɓuka wani abin, wane ƙabilar ne ko shi ma ba ki sani ba?" Nana ta yi shiru ta rasa ma me za ta cewa Nene.
Nene ta ce "To shikenan, amma ba kya ganin yakamata gidanku su san kin haihu?"
"Nene babu buƙata goben jaririn nan nake hange"
"Haka ne, to Ubangiji Allah ya kyauta, amma wannan lamarin naki akwai sarƙaƙiya Nana. Amma ba komai Allah ya taƙaita"
Nana ta amsa da Amin.