Sashe 62
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nana ta ce "Kin yi kuskure, dan ina zaune a ƙarƙshinki, ina da personal life ɗina, da 'yancin adana abin da yake sirrina, bai halatta ki bincikar mini kaya a bayan idona ba. Yaushe na san ki, da zan ƙulla wani abu da zan cutar da ke? Kina gudun hakan ki jawo ni ki ka kawo ni?"
"Yi ƙasa da muryarki, kar ki kuskura ki ɗaga mini murya, kin san matsayina? Za ki iya janyo wa kan ki gagarumar matsala muddin ki ka ci gaba da yi mini magana ba ladabi"
"Babu ruwana da matsayinki, da koma me za ki yi mini, kar ki sake shigar mini ɗaki ki taɓa mini kaya, idan kuma ki ka ci gaba za ki iya binciko abin da zai hana ki sukuni, idan kin ji ba ki yarda da ni ba, ki sallame ni na koma inda na fito, ba zai yiwu na zauna da ke kina zargina kuma kina cin dunduniyata ba."
Asal ta bi Nana da kallon mamaki, amma ta danne mamakinta ta haÉ—iye fushinta, ta ce "Gaskiya ne, kin yarda da kan ki har haka kenan? Shikenan amma idan na ga akasin abin da ya fito daga bakinki, za ki sha mamakin abin da zai faru"
Nana ta yi mata banza, ta koma É—akin nata, ta gyara kayanta tsaf.
Ta kulle ɗakin ta koma ta ɗaga katifar ɗakin, ta ɗaukko wata jaka, a cikin jakar ta zuba duk tarkacen kayan Sayyid. Ajiyar zuciya ta ts yi, da tayi wannan dabarar ta ɓoye su. Haka kurum take jin kayan na buƙatar sirri.
Ta nemi guri ta kwanta tana sauke numfashi a hankali, tana tunanin yadda rayuwa ke ta jujjuyata.
*****
Shukura na zaune a ɗakinta tamkar zuciyarta za ta yi bindiga ta fito, Sagir ya buɗe ƙofa ya shigo ɗakin. Kallo ɗaya ta yi masa ta sunkuyar da kai. Tuni t yi shirin kwanciya baccinta, sai ƙamshin turare take zubawa.
Ya sha manyan kayansa, hannunsa riƙe da baƙaƙen ledoji. Ya zo ya zauna a kusa da ita, tamkar ta kifa masa mari haka take ji.
"Wai har kin yi shirin kwanciya? Na zata zaku gaisa tukuna sai ki kwanta" Mugun kallon da ta yi masa ya sanya shi haÉ—iye maganar da ya yi niyyar yi.
"Ga wannan naki ne" Ya yi maganar yana ajiye mata ledojin hannunsa.
Ba ta kalli kayan ba, kuma ba ta motsa ba.
Ya matsa kusa da ita, ya riƙo hannunta, ta fizge hannunta ta haye kan gadon ta kwanta.
Bai ji haushin abin da ta yi masa ba ko kaɗan, ya san idan ba ta son sa ba za ta yi kishinsa ba, sai dai ita ma Yusra tana buƙatarsa tun da tun farko bai kamata ya sake ta saboda larurarta ba.
Ya tashi ya kashe mata fitila, har zai fita ya koma gaban gadon, ya durƙusa daidai fuskarta ya ce "Ki yi mini afuwa Shukura, ban yi haka domin na cutar da ke ba, ko na muzguna miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki saboda lafiyarki da abin da yake cikinki" Daga haka ya tashi ya fice. Sai da ya fita sannan ta ba wa hawayen da suka maƙale a ƙirjinta damar zirarowa, zuciyarta ta din ga yi mata ƙuna, tamkar ta tashi ta bar gidan.
Duk da ya fita da damuwar halin da Shukura take ciki, amma bayan wani ɗan lokaci tuni ya manta, suka ci suka ƙoshi da shi da Yusra.
Bayan sun gabatar da salla, sun yi addu'oi, suka yi zamansu kawai su na hira.
Sai gurin É—aya saura sannan suka tashi suka kwanta.
Yadda Sagir yake murna da kasancewa da Yusra, ko aurensu na fari bai yi haka ba, tuni wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da su, daga shi har ita.
Shukura kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, ga wani irin zafi da ya addabe ta duk da na'urar sanyaya É—aki da ke cikin É—akin.
Washegari sai ƙarfe sha ɗaya na safe ya shiga ɗakin Shukura.
Idonta kawai ya kalla ya ga alamun rashin bacci a tattare da idanunta, sun yi jawur sun kumbura.
"Oum Haidar" ya kira sunanta, yana zama a kan gadon, tana shan tea.
"Ina kwana" ta faɗa a taƙaice.
Idanunsa ya sauka a kan ledar da ya kawo mata, babu alamar ko taɓa ledar ta yi.
"Shukura me yake damunki ne haka? Na kawo abu ko taɓawa ba ki yi ba, kin yi bacci makuwa"
"Sagir, dan Allah ka tashi ka bani guri, ni bana buƙatarka a kusa da ni, kaɗaici nake so"
"Ni ki ke cewa na fita na baki guri?" Ya yi maganar yana nuna kansa.
Ƙoƙarin mayar da hawayen da ke shirin zubo mata take yi, amma abu ya gagara kawai ya fara zubowa ba tare da ta shirya hakan ba.
Jikinsa ya yi sanyi, ganin yadda take kuka sosai da sosai.
Cikin kwantar da murya, yake ƙoƙarin rarrashinta, amma ta tashi ta shige banɗaki ta bar shi a gurin.
Ya yi shiru ya rasa abin da yake yi masa daÉ—i, shi babbar damuwarsa ma cikin da take É—auke da shi, ga matsalarta ta hawan jini.
*****
Tamkar bayi haka su Nana suke aiki, kullum za a É—aukkosu daga wancan gidan da Asal take, a kawo su nan su wuni su na aiki. Har mamaki take yi wannan mutanen su kuwa har su nawa ne, dan kamar har da almubazzaranci a cikin lamarin.
Sai dai kowa cikin kaffa-kaffa yake aikin tare da fatan kar wani abu ya biyo baya da za a kama su da laifi.
Kwana na uku, wanda ranar suka dafa normal Abinci, sauran kwanakin kayan snacks ne suka din ga yi. Duk cikin su Nana ce 'yar Nigeria, sauran duk 'yan Nijar ne, sai dai galibinsu baƙaƙen buzaye ne.
Sai da suka kammala aikin, aka ba su wasu kaya fararen dogwayen riguna, da rigar girki, aka saka su kai Abincin wani É—aki.
Katafaren ɗakina da dogon tebur, an gyara shi sai tashin ƙamshi yake yi. Sai dai gabanta ya yi mummunan faɗuwa da jin irin ƙamshin da yake tashi a ɗakin.
Take jikinta ya hau rawa, har ta nemi ta kifar da abin da ta É—aukko.
Ta É—aga kanta a hankali ta kalli jerin manyan frames É—in da ke É—akin, sai dai mutanen jikin hotunan, dukkaninsu fuskokinsu a rufe yake, ba ta iya gane kowa daga cikin su ba.
"Ke Nana ki kai mana kin ja kin tsaya" Nana ta jinjina kai jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban teburin. Ta ajiye kayan, ta ɗaga kai ta kalli yadda ginin ɗakin yake da matuƙar tsayi.
Jiki a sanyaye ta ci gaba da kai komo, su na shirya abincin.
Bayan sun shaƙe teburin da uban kayan Abinci, aka ba su umarnin su tsaya kar wanda ya fita.
Su na tsaye Nana ta kalli agogon ɗakin, ƙarfe goma na dare.
Wani ƙaton mutum ya shigo, ya kalli gurin da yadda aka shirya teburin, ya kalli su Nana ya ce "Waɗanan ne suka yi girkin?"
Balaraba wadda ita ce ta jagoranci su Nana gurin girke-girken ta risuna ta ce "Eh su ne ranka ya daÉ—e"
"Wace ce wannan? Na ga kamar ba tamu ba ce" Ya yi maganar yana nuna Nana, da gaba É—aya rabin hankalinta ba ya jikinta.
Balaraba ta ce "Gimbiya Asal ce ta zaɓo ta, ta saka ta a cikin masu girkin"
Ya yi shiru yana kallon Nana, daga bisani ya jinjina kai ya kalli Balaraba ya ce "Ki je, su su tsaya" Ta jinjina kai ta fice.
Wata ƙofa aka buɗe, wani matashi ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi, gaban Nana ya yi mummunar faɗuwa, dogo ne sanye da farar jallabiya ya ɗaura hirami a kansa, ba dan ta yi wa Sayyid kyakykywan sani ba, za ta iya cewa shi ne. Ƙirjinta ya tsananta bugawa, sai dai kafin ta daidaita nutsuwarta, wani ma ya biyo bayansa, shi ma dai kamarsa ɗaya da Sayyid ɗin.
Tunani ta fara yi ko Giyaz da Ƙaisar ne suka fara yi mata gizo suke yi mata wasa da tunani.
Ɗaya bayan ɗaya suka din ga shigowa, sai da ta ƙirga mutum biyar cif, biyu kamar su ɗaya sak, sauran ukun kuma su na kama amma ba sak da Sayyid ba. Duk suka jeru a kan kujerun teburin nan. Sai dai babbar kujera babu kowa a kai, kujerun gefe da gefen kujerar ma babu kowa a kai.
ÆŠaya daga cikin su ya ce "Ko waye zai hau wannan kujerar?" Ya yi maganar yana nuna É—aya daga kujerun da babu kowa a kai.
"Wannan karon dai za mu ji me Sultan zai ce mana a kan maganar"
"Nima dai abin da nake son ji kenan, magana ta gama cika gari ba a san inda yake ba, ana ma tunanin ko ya mutu suke ɓoyewa"
Nana ji ta yi ana busar sarewa a ƙofar bayan su, gaba ɗaya suka ja gefe domin bayar da hanya.
Wani dattijo ne fari sol, mai dogon gemu ya shigo jallabiyarsa baƙa, ya lulluɓe kansa da hiraminsa.
Gaba ɗaya ta ga abokan aikinta sun rikice, duk sun sunkuyar da kansu ƙasa, Nana kuma ta yi masa ƙuri da ido. Sai dai ba shi take kallo ba, ji take tamkar numfashinta ya ɗauke, kamar ba a cikin duniya take ba, duniyoyin da Ƙaisar ya saba kaita ne ya caza mata kai, banda haka wani irin mummunan gizo ne wannan?.
Gaba ɗaya matasan suka miƙe tsaye, cikin matsanancin mamaki suna kallon na bayan dattijon.
Tamkar yana tausayin ƙasar haka yake taka ta, yana ɗan yin rangaji kaɗan, sassanyan ƙamshin turaren sa da ko a mafarki ta ji shi tana tantancewa ya karaɗe ilahirin gurin, fiye da ƙamshin turarukan da ke tashi a gurin.
Ta kusa da ita ce ta ja hannunta da ƙarfi, saboda yadda ta tsare shi da idanunta ko ƙiftawa ba ta yi.
Ya zo zai gifta ta, amma ko gurin da suke bai kalla ba, É—aya bayan É—aya suka din ga rungume shi, cike da murnar da wasu har zuci, wasu kuma iya ta fuska ce. Ta ga ya zauna a kan kujerar da ake tababar wa zai zauna a kai kafin ya shigo.
Abdou ya ce "Kun yi mamaki ko? Ba ku yi zaton ganinsa ba?"
ÆŠaya daga cikin su ya ce "Gaskiya ne"