← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 78

Sashe 31

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce "Wanne daga ciki?"

Ya zauna tare da faɗin "Ba shekaranjiya muka yi zancen Nana da ku ba? Gidansu na je, daga gidan nake na samu babanta a waje, ya gaya mini wai mijinta ne ya ɓata ta bi shi Nijar neman sa"

Hajiya Amina ta dafe ƙirji ta ce "Ya ɓata kuma garin yaya? Ko shi ma ɗauke shi aka yi kamar yadda aka tafi da 'yan uwansa? Anya ba wani laifin suke aikatawa ba hakan ta faru? To ta san inda yake a Nijar ɗin ne?"
Yusuf ya ce "Wallahi nima ban sani ba, haka dai ya ce mini"

Alhaji Zailani da hantar cikinsa ta kaÉ—a ya ce "Wai maganar wa ku ke yi ne?"

Cikin dakiya ta ce "Nana mana, yarinyar nan da ta kula da Haidar, wadda babanta ya aura wa Buzun nan"

"To sai aka yi yaya?" Yayi maganar yana tsare ta da ido, yana tunanin ko Hajiya Amina ta ci gaba da bibiyarta, ta gaya mata abin da yake tsakaninsu.

"A'a dama Shukura ce ta ce, kwana biyu shiru, kuma ba ta samun ta a waya, nima kuma ba na samun ta, shi ne na ce masa dan Allah idan ya biya ta hanyar gidanta, ya tsaya ya karɓo mini lambarta, to kuma wai sun tashi daga gidan. Shi ne ya je gidansu aka sanar masa da ta bi mijin Nijar" Ya yi wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya yi shiru bai kuma cewa komai ba.
Hajiya Amina ta yi ta jajanta lamarin, tare da tausayawa Nana.

Alhaji Zailani kuwa rikicewa ya yi, cike da kiɗima. Domin yana ta tsara yadda zai samu Nana ko ta halin ƙaƙa domin samun biyan buƙatar sa. Yaronsa da ya bawa ragamar bibiyarta, bai taɓa gaya masa ba, ce masa kawai ya yi ta koma Kurna.
Wani irin gumi ya fara keto masa, ta ina za a fara neman ta yanzu har a gano ta, a Nijar.
Sai ya ɗora wa kansa alhakin sakacinsa ne, da ya din ga bin al'amuran a sannu, duk da hakan ya faru a dalilin halin da yake shiga, a duk lokacin da ya yi yinƙurin aiwatar da wani abu a kan Nanan.

****
Nana kuwa wuni ta yi tana gararanba a titi, daga wannan inuwa ta koma waccan, ga uban kaya ga kuma ciki. Dama Abinci ba damunta ya yi ba. Buredinta da ta yi guzuri ta ci abin ta, ta kora da ruwa.
Tana son samun muhalli, tun da akwai kuɗi a hannunta, akwai na Nigeria akwai na Nijar, sai dai amana ta yi ƙaranci, ba ta san wa za ta tunkara ya taimake ta ba, tana tsoron a cutar da ita.
Dare ya yi bayan sallar Isha'i, ta sake lallaɓawa ta koma gidan nan ta kwana a rila, da Asuba mijin matar ya sake ganin ta, hakan ya sanya hankalinsa fara tashi, ga shi ya kasa magana kamar wanda aka yi wa asiri.
Yau bayan magariba da ya koma gida, sai ya sanya wa rilar sakata, ya kulle ta ciki.
Sawu ya ɗauke, Nana ta lallaɓo ta zo ta kwana, kawai ta tarar da rilar a rufe, ta jijjiga ta ji an garƙame ta ciki.
Jikinta ya yi sanyi, ga shi duk inda ta tafi ko ta yi niyyar ta yi gaba ta tafi wani gurin, sai hankalinta ya kasa kwanciya sai dai ta koma gidan nan.
Ga yau wani irin bacci take ji, kamar ta kifa, ga shi tana son yin wanka, saboda yadda kayan jikinta suke mintsininta, tun da ta zo da su take yawo.
Ta samu gefen gidan ta takure, tun tana hamma har bacci sosai ya yi awon gaba da ita.
Da Asuba ta ciro jarkar ruwan da ta saka wasu yara suka zuba mata a cikin ƙaramar jarka, ta yi alwala ta yi raka'atanul fajr. Tana kallon mai gidan ya fito ya tafi masallaci yana haske-haske, amma bai gan ta ba, har ya tafi.
Ya dawo daga masallaci kansa tsaye zai shiga gida, ya ga Nana a cikin rilar. Wata irin razana ya yi, ya kuma kasa magana sai kallonta da yake yi fuskarsa na bayyanar da tsoro ƙarara.
Nana ta ce "Ka kulle rilar gidanka, jiya a waje na kwana, duk da ban ga laifin ka ba, amma da ka tambaye ni, me yasa nake kwana a nan"

"Wa..wa.wace ce ke? Me ki ke yi a nan?"

Ayshercool
08081012143

63

Nana ta ce "Dan Allah ka kwantar da hankalinka, kar ka tsorata wallahi ni mutum ce, ba abin da na isa na yi maka na cutarwa, ba kuma ni da nufin cutar da ku"

"To me ki ke yi mini a gida?"

"Wallahi baƙuwa ce ni, ranar da na sauka a garin nan, na shiga gidanka, matarka ta bani gurin salla, har da abinci, dan Allah taimakona za ku yi"

Ya ce "Baiwar Allah wallahi mu ma talakawa ne, ba wani taimako da za mu iya yi miki"

Ta ce "A'a amma ai ku musulmai ne, gudun zargi dan Allah idan babu damuwa, mu shiga ciki a yi maganar a gaban matarka, ku ji taimakon da nake buƙata idan za ku iya yi mini, idan kuma ba za ku iya yi mini ba, babu komai sai na nema a gaba"
Kamar ya ce a'a, amma yanayin Nana sai ta ba shi tausayi, ya bata dama suka shiga gidan, yana gaba tana bin sa a baya.
Nana ta tsaya a tsakar gida, ya shiga ya taso matarsa. Ta fito tana mustustuke ido, ya nuna mata Nana ya ce "Kin san wannan?"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Kamar shekaranjiya ta zo, ta ce mini baƙuwa ce za ta yi salla"

Ya ce "Yauwwa, sau uku ina ganinta a rilar gidan nan. Wai a nan take kwana, ta ce mini taimako take nema, amma a zo a gaban ki, sannan ta faÉ—i me take son mu yi mata".

Matar ta kalli Nana,ta ce "Baiwar Allah, wane taimako za mu yi miki?"

Nana ta ce "Ni baƙuwa ce daga Nigeria, dan Allah ku taimaka mini da inda zan zauna, ban san kowa a ƙasar nan ba. E"

"Gaskiya baiwar Allah, ba bu gurin da za mu iya ajiye ki a gidan nan" matar ta tari numfashin Nana.

Nana ta ce "A'a ba a nan za ku ba ni gurin zama ba, da kuɗi a gurina, sai dai ban san kan kuɗinku na ƙasar nan ba, ina da wasu ma na Nigeria, ban san yadda zan canza su ba. Kuma ina tsoron na faɗa hannun da ba na gari ba a cutar da ni. Haka kawai na ji na nutsu da nan tun lokacin da ki ka karrama ni, ko na tafi sai na dawo nan na kwana nake samun nutsuwa. So nake ku taimaka a sama mini gidan haya, ko ɗaki da zan kama dan Allah. Kuma wallahi ni ba macuciya ba ce ba zan cutar da ku ba. Ku yi wa Allah da ma'aiki ku taimaka mini, dan Allah"

Ya kalli matar matar ta kalle shi, ta É—an jinjina masa kai.
Ya kalli Nana ya ce "Kin san harkar taimakon ce wuya ne da ita yanzu, sai ka taimaki mutum amma ya sanya ka a masifa.
Nana ta ce "In dai kun yi niyyar taimakona, ko macuciya ce ni, Allah ba zai ba ni damar cutar da ku ba. Ku taimaka mini dan Allah, ko iya gidan hayar a sama mini"

Ya kalli matarsa ya ce "Hajara, bata guri ta zauna, zuwa gari ya ƙarasa wayewa, sai mu san abin yi, mu duba girman Allah da ta haɗa mu da shi"

Hajara ta ce "To shikenan babu damuwa" wata irin ajiyar zuciya Nana ta yi, ta risuna ta ce "Na gode, Ubangiji Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi, yadda ku ka taimaka mini Allah ya taimake ku haka"

Suka amsa da Amin. Matar ta kai Nana wani É—aki, ta É—aukar mata kayanta ta shiga da su.
Tana fita daga ɗakin, Nana ta zube ta yi sujjada tana gode wa Ubangiji buwayi gagara misali, ta san wannan ɗaukin kai tsaye daga gare shi ne, amma ba dan haka ba ta san ba ƙaramar wahala za ta sha ba.
Sai yanzu da ta nustu, ta din ga jin ta a takure, saboda rashin wanka, ga cizonta da kayan jikinta suke yi.
Gari ya yi haske matar ta shigo ta ce wa Nana "Ki na buƙatar wani abu ne?"

Nana ta ce "Eh dan Allah zan yi wanka"

"To shikenan babu damuwa, da kin sani tun ranar da ki ka zo, ki ka yi mini bayani, ga ki da juna biyu, amma a ce ki na kwana a waje bai dace ba"

Nana ta ce "Larura ce, ba yadda zan yi, kuma babu daÉ—i ka É—ora wa mutane É—awainiya sama ta ka"

Ta ce "Haka ne" ta haÉ—a wa Nana ruwa, Nana ta duba kayanta ta É—auki soso da sabulu, da brush.
Ba ƙaramin daɗin wankan nan Nana ta ji ba. Ta koma ɗakin da suka sauke ta, ta fito koma ɗakin da aka sauke ta.
Ta fito da mai ta shafa, ta saka kaya. Ta ji wata sassanyar iska na ratsa ta. Ta É—aukko jakar kayan turarrukan Sayyid, da kayan gyaran gashin sa, ta yi zuru da ido, tana kallonsu.
"In sha Allah za mu haɗu Sayyid, ina fatan Allah ya ƙaddara haɗuwarmu nan kusa" ta yi maganar a sanyaye.
Sallamar Hajara ce ta sanya ta mayar da kayan cikin bagcconta, ta mayar da hankalinta kan ta.

"Ko ki na buƙatar wani abun ne?"
Nana ta girgiza kai fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "A'a ba na buƙatar komai, na gode sosai da sosai"

"Ba komai, bari na kusa gama abin karyawa"

Cikin murmushi Nana ta ce "Ba raina miki na yi ba, amma ni wannan taimakon da ku ka yi mini ya wadatar, ba sai kun ba ni Abinci ba, na gode sosai da sosai"
Hajara ta ce "Haba dai, ya ma za ayi ki na baƙuwarmu a ce ba za mu ba ki Abinci ba, ai ba zai yiwu ba sam"

"Ai kar É—awainiyar ta yi yawa ne, abin da ku ka yi mini ma, na gode Allah ya biya ku"
Chapter 31 · 0% Book details