← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 78

Sashe 38

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****
Baba yana tsakar gida yana shan kunu, sai ga Suwaiba ta fito, gaba ɗaya ta zama wata iri kamar shiri-shiri. Ta kalli Baba ta cake a ƙofar ɗaki ta ce "Nana fa ta haihu" ba shiri ya ajiye ludayin kunun ya kalli Suwaiba ya ce "In ji wa? Waye ya gaya miki?"

"Nanan ce ta gaya mini"

"Ke a ina ki ka ganta?"

"Ina bacci a É—aki, na ganta da jaririn, ta ce mini haihuwa ta yi"

Wani uban tsaki Baba ya ja, saboda jin shiritar da Suwaiban take faÉ—a. Dan da fari ya zata ma da gaske take yi.

Alhaji Zailani ne tare da Malam Gambo, su na zaune fuskarsa É—auke da damuwa.
Malam Gambo ya ce "Wai duk me yasa ka damu ne har haka? Ka na tsoron ƙungiya ta sake cewa ka kawo jininka ne?"
Alhaji Zailani ya numfsa ya ce "Abu na farko burukana biyu, ɗaya ya cika na durƙusar da Fatuhu. Amma samun yarinyar nan ya zame mini bala'i, ƙarewa ma da yake azzaluma ce mai baƙin hali, wai ta tafi Nijar. Ban kuma san ta yadda zan yi na same ta ba.
Babu yadda ban yi na samu yarinyar nan ba, amma duk lokacin da na yi wani yinƙuri a kanta, sai hankalina ya gushe. Yanzu babban tashin hankalina wannan jarababbiyar Sa'a, ashe ita ma ƙoƙari take yi, ta mallaki jinin yarinyar nan.
Ga shi na rasa dalilin da ya sanya Shukura take ta zargin likitan da yake yi mini aiki, da kisan jaririnta."

Malam Gambo ya numfasa ya ce "Ka tattara nutsuwarka guri guda, nasara na buƙatar kasada a kowane lokaci. Ita waccan yarinyar ka jingine batunta a yanzu tukuna, tun a wancan lokacin ai na gaya maka tana ɗauke da wani shu'umin aljani ne mai taurin kai a kanta ba zai taɓa barin burinka ya cika ta daɗin rai a kanta ba. Ba kai kaɗai ba koma waye kuwa. Sannan ƙungiya idan ta sake buƙatar jini, sai ka bayar da na ɗaya daga 'ya'yanka ko namijin, ko kuma ita yarinyar taka a bar jaririn nata ba shikenan ba. Kawai ya zuba wa Malam Gambo ido, idanunsa suka yi jawur sai dai bai ce komai ba ya tashi ya fita.

****
Ɓangaren Sagir kuwa, sosai yake sintiri tsakanin Kano da Abuja, saboda Yusra, saboda soyayyar da suke yi ma a yanzu, ba su yi ta a lokacin da suke saurayi da budurwa ba.
Wata irin muguwar shaƙuwa suka yi, da shaiɗan ke barazanar shiga cikin lamarin nasu, ga shi ya rasa ta inda zai tunkari Hajiyarsa da batun, domin ba son Yusra suke yi ba. Shukura tuni ta daɗe da gano inda ya dosa, amma ta zuba masa ido ta ga ina ne ƙarshen alewar zai kasance.

****
Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta yi wata guda da haihuwa, Nene ta tattara ta daina fita gurin sana'arta.
Sai aikin kula da Nana, ga shi kullum da sassafe kan ta ci komai, ake kawo nonon raƙumi fresh Nana ta sha, sannan ta ci Abinci.
Nana tana kwance tana bacci da azahar, saboda yadda Muhsin ba ya barin su bacci da daddare, saboda ba ya ɗaga wa Nana ƙafa da tsotso, ga kuka sai dai Nene ta taya ta riƙonsa.
Yana gabanta yana bacci, ita ma ya ɗauke ta, ta ɗaga kai ta ga ya shigo ta ƙofar ɗakin. Tana kwance ba ta motsa ba ta ga ya ƙaraso ya zuba musu ido, daga ita har Muhsin, ya sanya hannunsa ya shafa gashin jaririn, ya durƙusa ya sumbaci gishin yaron. Sannan ya kalli Nana idanunsa cike da hawaye.
"Sayyid, yaushe za ka zo ka ganmu? Mu na buƙatar ka a kusa da mu, dan Allah kar ka tafi ka bar mu"
Ya kama hannayenta ya riƙe a cikin nasa, sai dai bai yi magana ba. Sai da aka jima sosai yana murza yatsun ta a hankali sannan ya ce "Ma vie"
"Na'am"
"Gangar jikina ta kasa samun nutsuwa, rayukanmu su na kewar juna, ki kula mini da rayuwata da ke jikin ki, da jikin ɗa na, ina ƙaunarku Nana"
Riƙe Sayyid ta yi, tana kuka tana "Dan Allah Sayyid kar ka tafi ka bar mu, mu na buƙatar ka a rayuwarmu, dan Allah Sayyid, dan Allah"
Nene ta yi shiru tana kallon yadda Nana ta riƙe ta tana kuka.
Da yake sheshsheƙar Nanan ta jiyo, ta taho ɗakin tana zuwa ta tarar da Nana tana nema ta danne jaririn. Bayan ta ɗauke shi ne, Nana ta riƙe mata riga.
Nene ta zuba wa Sarautar Allah ido, Nana ta buɗe idanunta a hankali ta ga yadda ta riƙe Nene gam. A hankali ta cika ta tana sunkuyar da kai. Sai dai ta ɗaga kanta tana kallon ɗakin, tana jin ƙamshin turaren Sayyid a hancinta.
Nene ba ta ce mata komai ba, ta goya Muhsin ta fice da shi daga É—akin.
Nana ta lallaɓa, ta tafi gurin da kayanta suke, ta bubbuɗe jakar kayan shafe-shafensa, da take ta adanawa tana kallon su tana jin daɗi. Sai dai a wannan karon hawaye take yi, tare da jin zuciyarta tamkar za ta buga. Ta zazzage kayan ta din ga bin su da kallo, ta ɗago Azurfarsa da ya ba ta, ta ce ya yi mata yawa, ya ce ta ɗaure da zare ta yi sarƙa da shi.
A hankali ta furta "Da mutuwa ka yi na san Allah ne ya karɓe ka babu yadda na iya, da aurenmu ne ya ƙare shi ma na san wannan ƙaddara ce, ba a kaina a ka fara ba. Amma ban san a wani hali ma ka ke ba, duk a inda ka ke ina fatan Ubangiji Allah ya sanya ka na cikin aminci da kwanciyar hankali Sayyid.

****
Yana zaune a kujerar da ke cikin É—akin, da abu a cikin kofin yana sha a hankali.
Murmushi ya gaza barin fuskar Sultan, ya zauna a kusa da shi yana murmushi ya ce "Alhamdillah, sauƙi yana samuwa Imam, ya jikin naka?"
Ya kalli Sultan ya mayar da hankali ya ci gaba da shan shayin da ke cikin kofin hannunsa ba tare da ya furta komai ba.
Cikin damuwa Sultan ya ce "Har yanzu ba ka gane ni ba Imam?"
Har yanzun dai bai yi magana ba, bai kuma fasa shan shayinsa ba.
Sultan ya riƙo hannunsa guda ɗaya cikin nasa, ya ce "Imam ka kalli Abbanka mana, ka yi magana ko hankalina zai kwanta"
Ya waiwaya ya kalli dattijon.
Cikin murna Sultan ya ce "Ka na jin abin da nake faÉ—a?" Ya yi shiru yana ci gaba da kallonsa, bai yi magana ba.
"Ka yi mini magana ka ce wani abu mana"
A hankali ya zame hannunsa daga na dattijon, ya tashi daga kan kujerar ya koma gadonsa na marasa lafiya ya kwanta.
Sultan ya yi shiru yana kallonsa, sai dai ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Kar a ce ƙwaƙwalwar ɗan sa ta taɓu. A yadda alaƙarsa da ɗan sa take, ba ƙaramin abu ne zai sanya ya yi masa haka ba.
Kwanciyarsa ke da wuya, ya fara jijjiga, a rikice Sultan ya nufe shi. Sai dai ya fara kururuwa yana faÉ—in "Wuta zafi"
Matawalle ne ya shigo É—akin da sauri, suka rufu a kansa, Sultan ya din ga tofa masa Addu'a. Har ya daina jijjigar.
Abdou ya kalli Sultan ya ce "Abubuwa fa kamar ƙara rikicewa suke yi, mene ne abin yi yanzu. Ina tsoron a bi diddigi a gano halin da yake ciki fa"

"A fita da shi waje kawai, wataƙila a dace a can, ni na kasa gane kan abubuwan da ake yi masa a nan"

"A wannan yanayin, da ihun da yake yi"

"Abduou" Sultan ya kira sunansa cikin É—aga murya.

Abduou ya risunar da kai ya ce "Za a shirya duk abin da yakamata, za a yi abin da ka ce".

Jamila ce take ta juyi a kan katifarta, tana jiran reply É—in Abba, saboda chatting suke yi. Sai dai shiru bai yi reply ba har ta gaji ta yi bacci.
Da safe sai gurin sha É—aya ta tashi daga bacci, da yake tana fashin salla.
Ta duba wayar, ta tarar da tarin messages É—in sa da kiran waya, ta share ta je ta yi wanka ta shirya.
Daga tsakar gida ta ce "Mama ni na wuce"

"Ba za ki tsaya ki karya kumallo ba?"

"Zan ci a can, sai na dawo"

Suwaiba na tsakar gida, tana goge kaushi, ta ce "Jamila"

"Yes" Jamila ta amsa.

"Nana fa na gaishe ki, ba ki ga jaririnta ba"

Jamila ta ce "Ai dama ke da Nanan, kan ku ba ƙalau ba, shi yasa ke kaɗai take kawowa ziyara a mafarki." Sai kuma ta ɗan yi shiru cikin damuwa ta ce "Allah sarki Nana, ko ta na wani halin yanzu oho" ta ɗan ja numfashi ta sauke ta fita, tana ci gaba da tunanin Nana.

A falon Hajiya Sa'a ta tarar da Abba yana zaune yana Video game. Tana shigowa ya yi murmushi ya tashi zaune ya ce "Sannu da zuwa"
Ta murguÉ—a masa baki ta nufi bedroom É—in Hajiya Sa'a.
"To ai ba ta nan" ya yi maganar yana miƙewa ya bi bayanta.
"Me na yi miki ne ki ke hararata? Na tura miki saƙo duk ba reply"
Ta kalle shi ta ce "Ba jiya na yi ta jiranka da daddare ba, ka ƙi kula ni"

"Eyya, bacci ne ya kwashe ni, ki yi haƙuri"

"Ba wani nan, da budurwarka ka ke chatting ka share ni"
Ya waro ido ya ce "Wallahi ba ni da wata budurwa bayan ke, kema kin san ba na iya kula 'yan mata kema da ƙyar ai na gaya miki ina son ki" sai kuma ta tuntsure da dariya ya taya ta shi ma.
Za ta yi magana kawai Hajiya Sa'a ta shigo falon, ta gan su a zaune a kan dining suna hira har da dariya, alhalin a gabanta basar da juna suke yi.

Ɗan saroro Hajiya Sa'a ta yi tana kallon su, Jamila cike da bariki ta ce "Mummy sannu da zuwa" "Yauwwa" ta amsa a taƙaice. Abba ma kam kasa magana ya yi gaba ɗaya.

Ya yi wa Jamila sallama ya fita, sai dai Hajiya Sa'a ta yi kicin-kicin ta ƙi sakar wa Jamila fuska gaba ɗaya.
Chapter 38 · 0% Book details