← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 78

Sashe 74

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin matuƙar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buɗe ido a duniya ba ta taɓa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba.
Da ƙyar ta harhaɗo kalmomin da ta ce "Kai ka kashe Mummy, kuma ka bayar da mahaifar Mami? Da..da.dama aljani duk zai iya yin irin wannan abin?"

Yayi dariya ya ce "Ki na mamaki ne? Kodayake mutane duk abin da ba a kanmu ya faru ba, bamu fiye yarda ba, nima da fari kasa yarda na yi, abin ya ɗaure mini kai. Sai dai idan ki ka duba, ba a taɓa yi wa Amina aiki ba, kuma babu alamar tabo na tiyata a jikinta, dan haka ta yaya za ta rasa mahaifarta? Aljani muddin za ka yi masa biyayya, ka yi abin da yake so, to zai zama mai biya maka dukkanin buƙatunka. Da su ake sihiri, da su ake jifa, neman shugabanci, ɗaukaka kungiyoyin asiri da makamantansu. Duk wani siddabaru da za a ce miki sun yi ba abin mamaki ba ne ba" Ya yi maganar yana wata 'yar guntuwar dariya.
Shukura ta ƙara rikicewa ta kiɗime. Ta ce "Yanzu Daddy, duk son da mahaifiyarmu ta yi maka kai ka kashe ta? Ga amanarmu da Mami ta riƙe ta kula da mu, ashe dama rashin haihuwarta da ciwon nan na zubar da jini da take yi babu gaira babu dalili, kai ne sila? Kai ka haddassa mata? Yanzu tayaya zaka nemi yafiyar su? Ka rasa imaninka saboda abin Duniya? Kai fa ka kashe su"

Ya ce "No in ji wa? Ai ban rasa imanina ba, ai annabi ya ce duk wanda ya ce La'ila ha illalahu zai shiga aljanna"

Cikin kuka ta ce "La'ila ha illalahu ba ta fatar baki ba Daddy, tayaya za ka shiga aljanna bayan ka kai buƙatarka gurin wanin Allah da ya buƙaci ka saɓa wa mahaliccinka dan ya biya maka buƙata. Me yasa ka ga buƙatar ka ta yi girman da ta gagari Ubangijinka ka dangana ga waninsa"

"Wannan wa'azin naki kin riga kin makara Shukura. Ina da yaƙinin zan tuba kan na mutu, kuma Allah zai yafe mini"

"Wa ya baka garantin ganin nan da awa É—aya ma?" Ta yi maganar tana kuka mai tsuma zuciya.

"Ina da shi, dan ko ciwon kai sai na shekara ban yi ba"
Ya miƙe tsaye yana faɗin "Ki mayar da hankali ki din ga cin abinci, saboda ke da abin cikinki nake sanya ran ku zama sadsukarwar ƙarshe da zan yi a ƙungiya. Sai dai kafin nan, ina roƙon afuwarki ko ba komai ke ma kin ci albarkacin dukiyata. Ɗanki da ki ka rasa ni na yi amfani da shi" Daga nan ya ɗauki wayarsa ya yi gaba abin sa hankalinsa a kwance, kamar bai aikata komai ba.
Wani irin gunji Shukura ta din ga yi tana kuka mai tsuma zuciya, ta din ga fatan ina ma mafarki ne ba gaske ba. Tabbas wannan babbar jarrabawa ce, a ce mutum irin mahaifinta shi ne mahaifinka, gara a ce an haife ka ba ta hanyar aure ba, ko makamancin haka. Amma uba irin Alhaji Zailani ba shi da wani amfani. Duk wata gwagwarmayar sa da faɗi tashinsa a kan iyalinsa ya zama na banza, a dalilin wannan mummunar hanyar mara ɓullewa.
Abubuwan da ya gaya mata sun shallake tunaninta, yanzu yadda ya tafi haka zai je ya ci gaba da rayuwa da Hajiya Amina duk da zaluncin da ya yi mata. Ta ji dama ta ba wa Sagir damar kai ta Asibiti wataƙila da ba a samu damar sace ta ba. Cikin kuka take roƙon Ubangiji Allah ya tona wa mahaifinta asiri, saboda a yadda zuciyarsa ta ƙeƙashe ɗin nan, babu wani abu na rashin imani da zalunci da ba zai iya aikatawa ba.

Can gida Sagir ko abinci ba ya iya ci. Yusra kuwa abin ka da ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, sai ta kwanta rashin lafiya, saboda yadda ta addabi kanta da ɗorawa kanta alhakin ɓatan Shukura, dan cewa take saboda ta dawo gidan Sagir Shukura ta tafi.
Haka Hajiya Amina ma, Addu'a kawai take yi a kan Ubangiji Allah ya bayyana Shukura a duk inda take. Sosai take jin tamkar 'yar cikinta ce ta ɓata, tun tana daurewa har ta kasa ta fara zubar da hawaye, kasancewar babu wani labari mai daɗin ji da zai nuna an kusa gano inda Shukura take.

****

Asal ta na tsaye a banÉ—akin cikin É—akinta, bayan tabattar da Imam baya É—akin, ta danna wata lamba ta kira.
Can aka É—auka mutumin ya ce "Na'am ina jin ki"

"Ina da labari ne"

"Ina sauraren ki"

Ta numfasa ta ce "Hannun Imam babu zobensa na tambari, na tambaye shi ya ce mini karyewa ya yi ya kai gyara, daga bisani kuma ya ce mini bai san inda yake ba"
"Kin tabattar da hakan, ba kuma ɓoye shi ya yi a wani gurin ba?"
Asal ta ce "Eh na tabattar ai zobe ne da ba ya cire shi, tun da ya dawo babu zoben a tare da shi"
Mutumin ya numfasa ya ce "Madalla, ki ci gaba da sanya ido da sanar da ni duk wani abu da yakamata na sani"
Ta jinjina kai tamkar yana ganinta ta kashe wayar ta fita.
Jikin Nana tamkar an yi mata duka, saboda azabar gajiya da ta yi. Ta kammala aikinta tana ta gyaran kitchen, sai ga Balaraba ta shigo da ƙatuwar jarka. Ta ajiye ta ta ce "Gashi nan madarar raƙumi ce da Imam yake sha"

"To sannu da ƙoƙari Mama Balaraba"

Ta ce "Yauwwa kukun Imam, Allah ya taimake ki"

Nana ta yi murmushi ta ce "Kar ki ba ni kunya mana"

"Ba kunya zan ba ki ba, ai ke yanzu duk wata kuku a gidan nan a ƙarƙashinki take, ke kaɗai ki ke dafa abincin da zai ci, dole mu girmama ki saboda kema shugabarmu ce"

"A'a ni ba shugabarku ba ce ba, ni da nake bare ma a cikinku. Amma dan Allah Mama Balaraba wai su wa ake cewa Imam É—in nan ne? Dan na ga wanda ake kira da hakan da yawa"

"Eh su Biyar ne, galibinsu jikoki ne na gidan sarauta, su na cikin jerin waɗanda za su iya gadon kujerar Sultan. Shi Imam Hammad a gidansu su biyu ne  da shi da Imam Abdallah, sai Imam Zahradeen shi ma jikan marigayi Sultan ne, akwai Imam Asadullah yayan Asal, sai Imam Omar, waɗannan su ne jerin waɗanda ake sanya ran za su gaji kujerar Sultan. Duk da su na ganin cewa Sultan na yanzu nuna son kai ƙarara na son Imam Hammad ya gaje shi a cikin yaransa. Imam Hammad yana da 'yan uwa da suke uba ɗaya amma su biyu ne suka cika ƙa'idojin zama Imam.
A ƙasar nan ana girmama duk wani Imam fiye da zatonki, mu na ƙasa mu na son Imam Hammad sosai mussaman baƙaƙen buzaye da fararen ke  yi mana kallon kamar ba 'yan uwansu ne mu ba, bayinsu ne kawai.
Idan kin lura galibi hadiman gidan nan baƙaƙen buzaye ne, fararen kaɗan ne ƙarara yake ƙoƙarin yaƙi da kyamar da fararen buzaye suke yi mana, yana ta fafutukar nema mana 'yanci, da ƙoƙarin mu ma a din ga bamu dama a cikin shugabanci, bai kamata iyayenmu sun ƙare a bauta mu ma mu ƙare a haka ba. Amma manyan nan ba sa son shi sam, gani suke yana ƙoƙarin hana su rawar gaban hantsi. Ni tun da ya dawo ma duk ya canza mutum ne mai sanyin hali, amma kaifi ɗaya ne, ba sani babu sabo.
Shi ne shugaban majalisar duk Imam ɗin ƙasar nan. Duk da a cikin su akwai wanda suka girme masa, amma a haka dole su girmama shi kamar yadda yake a dokar ƙasar nan.
Tarihin masarautar Agadez yana da yawa da kuma faÉ—i Nana, bari na tafi na je na ci gaba da aikina.
Nana ta jinjina kai ta ce "To shikenan na gode sosai da sosai"
Bayan fitar Balaraba Nana ta naɗe hannunta a ƙirjinta, tana nazari da tunani.

Jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, ta duba kayanta ta lalubo takardar nan da aka kawo saƙon aka ce a ba wa Sayyid. Ta ƙare wa takardar kallo.
"Ko a cikin Imams É—in nan ne wani ya aiko da wannan takardar?" Ta yi maganar tana tuna maganganun da ta ji suna yi ranar da aka kai su yin girki a gidan Sultan. Ta koma ta lalubo zoben gurin Sayyid ta din ga jujjuya zoben ta ce "Ko kai a ke nema ne? Idan kai ne ta yaya zan ba shi abin sa, tun da ban san iya adadin muhimmancin sa a gare ka ba, idan na baka ka manta ni ta yaya zan yi bayani a yarda da ni?" Ta din ga surutai ita kaÉ—ai ta gaji ta nannaÉ—e kayan ta buÉ—e jakar sarkin baka ta watsa takardar da zoben ta rufe ta ajiye a cikin kayanta.
Bayan sallar magariba aka sanar mata baƙin Imam sun iso, su na can sashin karɓar baƙin sa wanda ɗaki ne a can wajen lambun gidan.
A kwanduna ta shirya kulolin Abincin, É—aya daga ma'aikatan gidan, ta taya ta kai wa.
Su na zazzaune a ɗakin, gaban su shaƙe da kayan marmari da uban soyayyen nama.
Duk wannan Imam Imam É—in ne, gaba É—aya zaune a gurin.
Ayabar hannun Sayyid ta kalla, da ya kai bakinsa ya gutsura fuskarsa ɗauke da murmushi. A take ta ga jini yana bin bakinsa, ayabar ta koma baƙa ƙirin, wasu abubuwa masu tsini tamkar ƙayoyi suka tsiro a jikinta.

Ayshercool
08081012143
77

Rikicewa ta yi, amma ta fara ƙoƙarin daidaita nutsuwarta dan ta san idan ta yi wani gangancin a gurin, babu lallai ta sha ta daɗin rai duba da girman mutanen da suke gurin a zaune.
Ganin ta tsaya ta zuba masa ido, ya sanya ya sauke hannunsa a hankali yana kallon ta shi ma.
Ta ƙarasa shigowa a hankali ta ajiye musu kwanukan abincin.
Chapter 74 · 0% Book details