Sashe 7
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina fa lafiya Nana, meya haÉ—a ki da mutanen gidan nan, ga shi ana cewa ke mayya ce".
"Mayya kuma?"
"Eh mana, yanzu case na hannun 'yan sanda, Baba yana can tare da su, ana jiran likitoci su faÉ—i sakamakon binciken su."
Nana ta gaya wa Ummi iya abun da ta iya tunawa. Sai dai ta sha mamaki, ta ji wai Baba ya zo kan matsalar ta.
Ta kalli Sayyid da yake kwance lamo, abin Duniya duk ya dame shi.
Sajida ta haÉ—a kayanta, ta gudu ta ce ba za ta iya kwana da Nana a gidan ba.
Sai zuwa da safe, Likitoci suka tabattar da anemic shock ne ta samu, bayan binciken ƙwaƙwaf da suka yi, suka gano ta yi ɓari sati biyu baya, ta kuma zubar da jini sosai ba ta je Asibiti ba. Ta zo ta yi zazzafan zazzaɓi na typhoid amma suka alaƙanta hakan da mayu, nan ma ba a je Asibiti ba. Hakan ne ya haddasa faɗuwar ta. Bayan fito da sakamakon, mijinta da 'yan uwanta suka ce ba su yarda ba, sakamakon ƙarya ne kawai aka gaya musu.
Ga Barira ta farfaÉ—o, tun a cikin daren ma, har ta ci Abinci, amma suka ci gaba da surutu a kan Nana mayya ce.
Ummi tare da su Nana ta kwana, saboda tsananin tsoro. Dan da gidanta akwai guri can za su tafi ma. Sai dai tashin hankalin abin da ya faru, ya sanya jikin Sayyid rikicewa gaba É—aya, ya zamana kamar ma ba ya gane wanda yake kansa.
Hankalin Nana ya yi mummunan tashi, ga shi babu isasshen kuɗin tafiya Asibiti. Ta kuma san tashin hankali, da damuwar abin da ya faru ne, ya sanya jikin nasa ƙara rikicewa.
Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga matan gidan kowacce ta koma gidansu, sun ƙi dawowa gidan wai tsoro suke ji.
Ummi ce ta yi sallama, Nana ta amsa ta yi mata izini ta shiga ɗakin. Hannunta riƙe kular Abinci. Ta kalli inda Sayyid ke bacci a wahale, numfashinsa na fita sama-sama. Cikin damuwa Ummi ta ce "Yanzu Nana haka jikin nasa ya koma?"
"Wallahi Ummi, gaba É—aya hankalina a tashe yake"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ana wata ga wata"
Cikin damuwa da rashin fahimta ta ce "Me ya faru?"
Cike da karaya, da matsanancin tausayin ƙanwarta ta ce "Mai gidan nan ne, ya je ya same ni, ya bani dubu goma sha biyu, wai ga sauran kuɗin ku nan, ku tashi. Ba ya son tashin hankali, kuma ga sauran 'yan hayar sun ce ko ku tashi, ko ya mayar musu da kuɗinsu su tashi. Nayi-Nayi ya ƙara wani abu, tun da ko wata ba ku yi ba, amma ya ƙi wai wannan ɗin ma da ƙyar ya samo su ya kawo."
Nana ta jingina da jikin bango tana maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"
"Nana mene ne abin yi yanzu?"
Nana ta girgiza kai, jiki a sanyaye ta ce "Ban sani ba Ummi"
"To ko wani gidan za a nemo? Sai na koma na neme shi, na roƙi alfarmarsa?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a Ummi, an riga an yi mini mummunan tambari a unguwar nan, abu ne mai wahala ma mu sake samun wani gidan a unguwar nan"
"Bari na kira Baba na ji me zai ce"
Nana ta ce "A'a Ummi, kin san halin Baba, kar ranki ya ɓaci"
"To Nana ya zamu yi, dole a kira shi mu ji me zai ce" Ummi ta kira lambar Baba, yana É—aga wayar muryarsa a sama ya ce "Ya kuma aka yi, ba an kashe case É—in a gurin 'yan sanda ba?"
Ummi sai da ranta ya sosu, amma ta maze ta ce "Baba ba wannan ba ne. An kori su Nana daga gidan da suke ne, mai gidan da suke ya ce sai sun tashi"
"To sai kuma aka yi yaya? Ni zan nemo musu wani gidan? Ko kuma mijinta ne yakamata ya nemo musu wani?"
"Baba ka fa zo gidan nan, ka ga halin da mijin nata yake ciki na rashin lafiya, saboda haka aka kore shi daga gurin aikin gadi. Dan Allah Baba ka yi wani abu a kan yarinyar nan. Nana yarinya ce ƙarama pressure ta yi mata yawa."
"To Ummi ya ki ke so na yi? Ni dai nan gidan babu gurin da zan ajiye ta, ita da mijin nata, idan kuma ke ki na da guri ki taimaka ki ba su. Idan ba haka ba ta nemo 'yan uwansa su É—auke shi, su rakata inda danginsa suke. Kin san dai nan gidan idan ta dawo, abin da za ta ci ma aiki ne. Nima yanzu sai abun da aka samo aka bani"
Hawaye ya cika idon Ummi, cike da takaicin yadda Baba bai fiye damuwa da damuwarsu ba. Ta ce "Baba da ina da inda zan ajiye Nana da mijinta, wallahi ba zan kira ka ba"
Nana ta ce "Ummi, dan Allah ki katse kiran nan, nima ba zan koma can gidan ba."
Tarin Sayyid ta ji, ta mayar da hankalinta kan sa, ta nufe shi tana faÉ—in "Sannu Sayyid"
"Ki ba ni ruwa" ta amsa da to. Ta É—aukko ruwan leda, ta buÉ—e masa ya tashi zaune ta fara bashi.
"Sannu Sayyid" Ummi ta faÉ—a cikin tausayawa, kallo É—aya ta yi masa ta gane yana jin jiki. Da da ne, kome za a yi,ba zai bar gashin nan a buÉ—e ba. Amma yanzu ba ta gashin yake yi ba, ga fuskarsa duk ta kumbura. A zuciya irin ta Nana, ta san ko a titi ta tsince shi a wannan yanayin, ba za ta iya tafiya ta rabu da shi ba, balle mijinta.
Ƙarar da wayarta ta yi ne, ya sanya ta dawo hayyacinta. Ta ɗaga wayar tare da yin sallama.
"Ke Hansai, ina ta kiran wayar ki, amma ki ka ƙi ɗagawa?"
Ummi ta ce "Eyya, ba haka ba ne Uwani,ba na kusa ne, ya gida ya mutanen garin?"
"Lafiya ƙalau, ya na ji muryar ki ƙasa-ƙasa, laulayi ko rashin lafiya"
Ummi ta yi yaƙe ta ce "Ba gara a ce laulayi nake ina kwance ba, da abin da yake faruwa"
"Subhanallah, meyafaru?" Kasancewar Uwani kaka ce a gurin su Nana, ƙanwar kakarsu ce, da kakarsu wadda Nana ta ci sunanta da Uwani, uwa ɗaya uba ɗaya suke. Sai dai ita tana can Garko da iyalinta. Ummi ba ta ɓoye mata komai ba, ta gaya mata. Uwani ta rafka salati. Ta ce "Sai an yi magana ku nuna ku mutanen birni, kun fi mutanen karkara wayewa. Ina wayewar take. Aikuwa sai na kira Isa na ci ubansa mara mutunci. Tuntuni nake ganin take-takensa kamar har da ƙiyayyar uwar su, take shafar su a gurinsa. Ai Imrana yana zuwar mini nan. Ya hana kowa riƙe su kuma shi yana yi musu riƙon sakainar kashi. Yanzu ina duk sauran 'yan uwanki Ummi, ina 'ya'yan Atine, ina su Gaddafi da ba za ku iya taruwa ku rufa wa 'yar uwakku asiri ba?"
AREWABOOKS
"Wallahi Uwani mun yi iya yinmu ne.."
"Rufe mini baki, ina wani iya yinku, kuma duk wanda ya ce mana mayu Allah ya isa bamu yafe ba. Mu bamu gaji maita ba, balle a saka yarinya a gaba a tsangwame ta.
Na san babu lallai ta iya zaman ƙauye, amma mu nan akwai ɗakuna, har ma da gida da babu kowa, idan za su iya zama ta yi jinyarsa. Babu mai damun ta, kuma babu mai cewa ta tashi.
Amma tabbas kun ji kunya, idan har ku ka bari Asma'u ta wulaƙanta, a ce an rasa inda za ta zauna, ta yi jinyar mijinta, yawan ku kun zama taron tsintsiya babu shara." Ummi ta yi shiru, Uwani akwai kirki da karamci, amma idan ta botsare tana faɗa, to duk gaskiyar ka, sai dai ka yi haƙuri. Ta gama faɗan ta, Ummi ta kashe wayar.
Ta kalli Nana, ta ga yadda ta tattara hankalinta a kan mijinta, tana ba shi Abincin da ta kawo musu, sai lallaɓa shi take, da alamu abincin ma ba ya so.
"Nana, kin ji abin da Uwani ta ce?"
Nana ta girgiza kai ta ce "A'a.
"Cewa ta yi idan za ki iya zama, ku tafi can Buda ki kula da shi, akwai inda za ku zauna. Kin ga nan tun Baba ya san maganar maitar nan, kamar Mama ta ji ne. Ita kuma kin san gishiri za ta ƙarawa abin ta yi ta bayar da labari. Amma ban sani ba ko ki na da wata shawarar?"
"Ummi wace shawara? wanda yake ruwa ko takobi aka miƙa masa, ai karɓa zai yi. Sai dai shi nake tausayawa, amma ba ni da wata mafita da ta wuce wannan ɗin. Ni in dai zan samu inda zamu zaune na kula da shi, ba komai zan zauna ko a cikin dutse ne ba ƙauye ba"
"Kin tabattar Nana? Da wayonki fa sau ɗaya Baba ya taɓa bari, muka je muka kwana biyu"
Nana ta ce "Ba komai, zan zauna"
Sayyid ya sanya hannunsa biyu, ya damƙe na Nana.
Nana ta kalle shi ta ce "Sayyid, mene ne?"
Idanunsa sun kaɗa sun yi jawur, wata jijiya a saman goshinsa ta ɗaga ta kumbura, fuskarsa ta yi jawur. Laɓɓansa sauka din ga karkarwa yana son ya yi magana, Nana ta girgiza kai ta ce "Ba sai ka yi magana ba Sayyid. In sha Allah duk rintsi ina tare da kai, har Allah Ubangiji ya baka lafiya" Ummi ta kasa jurewa ta fashe da kuka.
Nana ta ce "Ummi idan ki ka yi kuka,ni ya zan yi? Kun saka ni a tsakiya, nama fi ku juriya, har da kai ma" ta yi maganar tana murmushi bayan saka idanunta cikin na Sayyid, duk da idon nata a cike da hawaye.
"Ummi ki gaya wa Uwani na amince"
Ummi ta share hawayenta ta ce "To shikenan, ya za a yi tafiyar to?"
"Ina ga a sayar da kayan É—akin nan, katifar ta ishemu, sai a sai ledar É—aki, sai kayan sawarmu"
"Nana, kina amarya amma a ce ɗakin ki babu kayan ɗaki, haka za ki je ki zauna? Kin san mutanen ƙauye ba sa raina abin surutu dai"
"Ummi ai ba ado da kwalliya zan je ba. Kuɗin kayan ma riƙe saboda ɗawainiyar abinci da kuma magani"