← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 78

Sashe 39

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Jamila kuwa ta din ga ƙissimawa a ranta, muddin abin da take zargi ya zama gaskiya game da Hajiya Sa'a za ta ba ta mamaki ba kaɗan ba.

*****
Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta kwana arba'in cif da haihuwa.
Sai da Nene ta kwana goma sha biyar, ba ta fita gurin sana'arta, saboda jegon Nana sai dai yaranta su je, sai bayan kwana sati biyun sannan ta fara fita, shi ma da wuri take dawowa.
Ranar da Nana ta kwana arba'in, ta saka Nana ta shirya suka je gidan su Hajara.
Sun yi murna sosai da sosai da ganin Nana, duk da ta rame, amma yanayin ta akwai nutsuwa a tattare da ita.
Auwwalu ya É—auki Muhsin ya ce "Ohh Allah ka bamu mu ma É—an kyakykywan jariri, ka ga É—a kamar na larabawa"
Hajara ta amsa da "Amin dai"

Nene ta ce "Ka ga fitsararru, babu ko kunyar idona?"

Auwwalu ya ce "To ai addu'a muka yi. Ban da rashin kara ma, a ƙa'ida fa ɗan nan, sunana na ya kamata a saka masa"

Nene ta ce "Saboda kai É—in waye?"

Nana ta yi murmushi ta ce "Yaya Auwwal, ai sunanka ne da shi, laƙanin ne kawai ba ɗaya ba"

Ya yi murmushi ya ce "Kuma fa haka ne" sosai suka karrama su Nana. Da suka tashi tafiya ma, sai da suka kuma bawa Jaririn kyautar kuɗi da kaya, a so samu Nana ba ta so suka karɓa ba, amma Nene ta amshe.
Da suka dawo kuma ta zagaya da Nana gidajen maƙwabta, suka gaggaisa.
Tun da suka doshi wani gida, Nana ta din ga jin gabanta na faɗuwa, kamar ta cewa Nene ba za ta shiga ba, amma ta kasa. Ta din ga addu'a tare da fatan Allah ya rufa mata asiri ya sanya ba wani abin ne zai faru da ita ba, ko Ƙaisar ne zai dawo ya hana ta sukuni a ƙasar da ba ta da kowa ba.
Ko da su ka shiga cikin gidan, sai Nana ta fara jin sanyi, yana ratsa ta a hankali.
Aka shimfiɗa su tabarma, da ƙyar Nana suka gaisa da mutanen gidan, ta nemi guri ta zauna. Sai ta daina gane abin da Nene suke faɗa ma. Ta din ga jiyo muryar su Nene can nesa da ita, hakan ya tabattar mata da gidan akwai wani abu.
Wani irin sauti ta din ga ji, a cikin kunnunwanta, kamar gurnani kamar nishi.
Ta daina ganin su Nene gaba ɗaya, sai wata mata da ta fito ta tunkaro ta. Ga matar babba da ita amma jikinta ɗauke da zaren mahaifa daga cibiyarta dogon zaren har kan wani baƙin ƙwarangwal da yake bin ta, hannun ƙwarangwal ɗin kuma mahaifa ce yake lasa da jini da komai a jiki.
Jikin Nana ya hau tsuma, ta din ga kallon matar da ƙwarangwal ɗin, tana son yin addu'a ta kasa.
"Nana" ta ji muryar Nene ta kira sunanta.
Sai ta buÉ—e ido ta kalli Nene.
"Tashi mu tafi yamma ta yi"
Nana ba ta motsa ba, ta ga matar da ta gani yanzu tare da ƙwarangwal ta nufo ta.
Matar gidan ta ce "Kar ki kuskura ki taɓa ta, yi haƙuri dan Allah ba ta da cikakkiyar lafiya ne" ta yi maganar tana kallon Nana.
Sai dai matar ba ta tsaya ba, ta yi kan Nana gadan-gadan. Wani irin azababben ƙarf ya zo wa da Nana, ta ji zuciyarta na tafasa jira take matar kawai ta ƙaraso gare ta, ta illata ta.
Amma Nene ta danƙi hannun Nana, ta hana matar ƙarasawa gurin Nana ta ce "Ke Ashura, meye haka ne? Ba ki ga baƙuwa ba ce?"
Matar cikin wata irin harɗaɗiyar magana da zubar da yawu ta ce "Magana zan yi mata, ta saka wannan ƙwarangwal ɗin ya daina bina" gaba ɗaya suka kalli Nana. Ɗaya matar ta ce "Wani ƙwarangwal ɗin, rabonta da magana ma fa ta fi sati biyu"

Kawai matar ta saka kuka, lallai sai ta je gurin Nana, ta cewa ƙwarangwal ya daina bin ta.
Nene ta ja hannun Nana suka yi waje. Sai dai ta ji jikin Nana tamkar gawa saboda sanyin da ya yi.
Su na zuwa gidan Nana ta nemi guri ta zauna, ba ta cewa Nene uffan ba.
Can bayan magariba, sai ga matar da su ka je gidanta ta zo, Nene ta ce "Gaji lafiya kuwa?"

"Dan Allah Nene ki taimaka mini, ko 'yar nan taki za ta zo mu je gurin Ashura, sai ihu take tana burgima tun da ku ka tafi"

"Ta zo ta yi mata me?"

Gaji ta ce "A'a ban sani ba ko akwai wani taimako...
"Taimakon me?" Nene ta katse ta.

"Kin san dai Ashura ba hankali ne da ita ba, wataƙila almatsutsan haukanta ne kawai ya tashi take wannan abubuwan, ki tafi babu inda Nana za ta zo"
Gaji ta fita jiki a sanyaye, dan idan ta matsa sai Nene ta balbale ta da masifa.
Nene ta ajiyewa Nana nonon raƙumi, da abincin dare, amma ta ƙi ci saboda sanyin da take ji.
Nana ta haÉ—a kanta gwiwa, tana jin yadda jikinta yake tsuma ta ce "Sayyid sanyi nake ji"

"Ke Nana" Nana ta É—ago ido ta kalli Nene. "Ba za ki ci abincin ba ne?"

"Na ƙoshi, amma dan Allah Nene mara lafiyar can ta can gidan, ta faɗi wani abu a kaina ne?"

Nene ta ce "Za ki ba ta magani ne?" Sai Nana ta yi turus tana kallon Nene, gabanta yana tsananta faÉ—uwa.
"Ba ta ce komai a kan ki ba, amma idan kin amince za ki yi magana da aljanin nata, ko ki bata magani kamar yadda ake so ki yi, sai mu je"
Gaban Nana ya faɗi, ta bi Nene da kallo cike da mamakin, yaya aka yi Nene ta san wannan maganar, alhalin ko da wasa ba ta taɓa gaya mata ba.

"Nana mamaki ki ke yi? Ai ba a banza na yarda na karɓe ki muke zaune a cikin gidan nan ba da ni da ke.
Tun zuwanku na ga abubuwan da na gani a tattare da ke.
Na ga inuwar rauhanin aljani a tattare da ke, kuma da alama ko dai kin gamu da baƙin aljani a hanya, ko kuma kin yi rayuwa da shi, saboda akwai warinsa a tattare da ke, saboda yana ta'amalli da jini, har ma warin nasa yana ƙoƙarin danne, ƙamshin rauhanin da yake tattare da ke. Sannan akwai alamu na alaƙa mai ƙarfi a tsakanin wannan rauhani da Aljanin da yake tattare da ke. Jiri ne ya fara ɗibar Nana, cikin wani yanayi mai kama da fitar hayyaci ta ce "Nene, wace ce ke? Ya aka yi ki ka san abin da ban gaya miki ba? Ki gaya mini ke wace ce?"
Chapter 39 · 0% Book details