← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 78

Sashe 26

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke Maijidda, bari ki ji na gaya miki, wallahi sai yarinyar nan ta bar gidan nan"
Ya nemi guri ya yi kwanciyar sa, takaici ya ishi Maijidda.
Nana kuwa tana jiyo hayaniyar su sama-sama, abin ya tsaye mata ta kasa bacci sam. Sai juye-juye, ga mararta ta ƙulle duk jikinta ma ciwo yake yi mata.

****
Kwance yake a kan gadon Asibiti, jikinsa babu riga, sai dogon wando an rufe iya ƙafafuwansa da koren yadi. Ƙirjinsa kuma an manna masa abin ECG. Sai gashin sa a rufe da hular Asibiti. Na'urorin gefen gadonsa sai sauti suke fitarwa.
Dattijo ne a tsaye a kansa, dogo fari tas, ya É—aura hirami a iya kansa, ga gemunsa dogo duk farin gashin furfura a jiki.
Ya kalli mutumin da yake tsaye ya ce "médecin (Likita) yanzu mene ne abin yi?"

"Eh, gaskiya za a yi masa wannan allurar ne kamar yadda na yi maka bayani, idan kuma ba haka ba, gaskiya sai dai a saka masa na'ura a zuciyarsa wadda za ta din ga taimakawa bugun zuciyarsa"

Na kusa da Dattijon mai sanye da shuɗiyar shadda, da babbar riga, kansa ya yi naɗi da baƙin rawani ya ce "Ka gani ko Sultan, Allah kaɗai ya san abin da suka yi masa a Nigeria. Dole yaron nan ya ɗanɗana kuɗarsa a ci gaba da tsare shi, har sai ya yi bayanin abin da ya yi masa a Nigeria, da aka neme shi aka rasa tsawon wannan lokacin. Su kan su sauran da aka kama su tare, dole a killace su a guri ɗaya, haryanzu ban bari an sake su ba, saboda idan maganar nan ta fasu akwai matsala"
Sultan ya numfasa cikin damuwa ya ce "Ni wannan bai dame ni ba, na bar ragamar komai a hannunka, ni lafiyar sa ce a gabana yanzu. Likita ku yi duk abin da ya dace kawai. Lafiyarsa ce damuwata a halin yanzu"

Likitan ya ce "In sha Allah" Dattijon ya saka hannunsa a cikin na mara lafiyan,yana kallonsa cikin matsananciyar damuwa. Kamar mafarki ya ga yana motsawa a hankali, sai ya ƙara tattara hankalinsa a kansa yana kiran sunansa.
Wata irin miƙa ya yi, yana ƙoƙarin buɗe idanunsa, amma ya ji tamkar an cika masa idanun nasa da barkono.
"Imam..

Hannunsa ya É—ora a ka yayi wata irin kururuwa, jin yadda naman jikinsa yake yi masa wata irin azaba, tamkar ana cizgar naman jikin nasa. Ga wani irin zafi da raÉ—aÉ—i da yake ji kamar yana cikin wuta.

"Zafi! Wayyo wuta Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wuta zafi jikina"

Kansa suka yi gaba ɗaya cikin tashin hankali, su na ƙoƙarin rirriƙe shi, amma ya watsar da su ya diro daga kan gadon, yana girgiza kansa da yake yi masa wata irin azaba tamkar zai tarwatse. Tunaninsa ne ya hargitse gaba ɗaya, ƙwaƙwalwarsa na ta kokawar ƙwato wani abu daga cikin memories ɗin sa, amma abu ya kacame, gaba ɗaya tunaninsa ya hargitse, ya kasa tantance komai. Fizge-fizge ya din ga yi yana kururuwa jikinsa na rawa. Dattijon nan cikin jarumta da ƙarfin hali, ya bi shi da sauri ya damƙe shi iya ƙarfinsa.
Kokawa suka din ga yi, a rikice likita da É—aya mutumin suka yo kansu, likitan ya haÉ—a wata allura ya yi masa. Jikinsa ya saki a hankali bacci ya É—auke shi. Kan gadon suka mayar da shi suka kwantar. ÆŠaya mutumin ya kalli likitan ya ce "Ka na ji na?" Likitan ya jinjina kai cikin nutsuwa.
"Ka san dai waye wannan, kuma ka san matsayinsa da girmansa ko?" Ya yi maganar yana nuna masa mara lafiyan.

Ya jinjina kai ya ce "Na sani"

"To muddin mu ka ji maganar abin nan da ya yi, ya fita waje, to ba wani ba ne ba kai ne, dole ka yi shiru da bakinka, kare sirrinsa wajibi ne a kan duk wani wanda yake yankin nan, idan kuma aka samu akasi ka furta wani abu, da rayuwarka za ka biya"

Likitan yana tsuma ya ce "In sha Allah ba zan faÉ—a ba"

****

Da safe mijin Maijidda ya shura takalmansa ya fice, bayan sun gama jayayya da ita, tana ta roƙonsa tana yi masa magiya. Gaba ɗaya Nana ta ji dana sanin zuwa Bauchi da ta yi.
Babban abin da ya bata mamaki, ƙatuwar kaza Maman ta saka aka yanka, ta gyare ta tsaf, ta yi wa Nana farfesunta, aka sayo mata ƙaton buredi ta haɗa mata shayi.

"Mama daga zuwana na É—ora miki É—awainiya, ba ma na iya cin Abincin ni"

"Ɗawainiyar ƙaniyarki, da can na yi miki ne Nana? Dan Allah ki daure ki mayar da hankali ki ci ki ƙoshi, idan kuma ki na son cin wani abin, ki gaya mini sai na dafa miki"

"A'a ba na son cin komai, amma ki zo mu ci tare da su Walida"

Maijidda ta ce "A'a, babu wanda zai ci, da rana ma ci Abincin tare, wannan dai na ki ne" Haka ta takura Nana, ta karya.

Nana ta fito da nufin, ta kama musu ayyukan gida, amma Mama ta hana, ta dafa mata ruwa ta yi wanka. Ta fito ta tarar Mama tana wanke kayan da ta cire.

"Haba Mama dan Allah ki bari na wanke da kaina, ya za ki din ga yi mini wanki?"

"Tafi É—aki ki je ki zauna ki huta, ga lemon fata can da rake, ki É—an sha saboda É—anÉ—anon bakinki. Akwai riÉ—i ma mai gishiri da mai suga, idan da wanda ki ke so" kawai Nana ta tsaya tana kallon ta, tana murmushi.

Maijidda ta ce "Ya dai?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba komai Mama, na gode sosai"

Nana ta shirya ta canza kaya, Khadija da take 'yar autar Mama, Nana ta kama ta tana tsefe mata kai. Ta ɗauki wayar Nana tana kallon hotuna. Sai ta buɗe wani video da Nana ta yi wa Sayyid,  ta yi masa kitso sai hararta yake yi tana cewa "Ka ga yadda ka yi kyau 'yan matana, yi murmushi mana" ya ɗago kansa ya hargitse idanunsa. Nana tana dariya. Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, gani take kamar ta shiga cikin wayar ta ga Sayyid ɗin ta.

"Anty Waye wannan?"

"Mijina ne" ta ba ta amsa tana murmushi.

"Ya na gan shi da kitso, kuma fari?"

Nana ta yi dariya ta ce "Ni kuma baƙa ko?"

"Eh, kuma ba kyau maza su yi kitso fa"

"Wai in ji wa? Ba ki ga gashin nasa ne da yawa ba?"

Khadijah ta ce "Eh, to yana ina yanzu?"

"Ya je unguwa, zai dawo ya É—auke ni mu tafi"

"To ki nuna mini shi idan ya zo" Nana ta ce "To in sha Allah"

Mama ta ce "Ke Khadijah, tashi ki bar ta ta huta, Nana kwanta ki huta, ki rabu da surutun yarinyar nan"

Khadijah ta tashi tana zumɓura baki, Nana ta ɗan kashingiɗa kawai wani abu mai kama da bacci ya yi awon gaba da ita, kasa tantance ma me take yi ta yi, bacci ne ko kuma ido biyu.

"Ma Vie" ta ji muryarsa a kunnenta. A razane ta waiwaya cikin damuwa. A tsakiyar sahara ta hange shi ta ce "Sayyid"

Ganinsa ta yi a tsaye a kanta, kayan jikinsa duk a yayyage, ya yi baƙi kamar ya ƙone, gashin kansa a hargitse jikinsa sai fitar da hayaƙi yake, ya ce "Ma Vie sun mayar da ni inda za su kashe ni, dan Allah ki zo kar su kashe miki ni." Yayi maganar yana hawaye.

Ta tashi cikin tashin hankali ta ce "Suwaye? Kuma a ina suke?"

"Dan Allah ki zo, ni ban san su ba, amma na san mutuwa zan yi, dan Allah Husnah ki zo gurina, za su kashe ni. Idan kuma sun kashe ni, ki kular mini da É—a na"

"Sayyid, dan Allah kar ka tafi ka bar ni, dan Allah Sayyid ka dawo? Ka gaya mini kana ina, sai na zo na same ka na tafi da kai"
Guguwar Sahara ce, ta taso ta turnuƙe gurin.
Nana ta din ga tari, muryar Mama ta ji a kanta tana faÉ—in "Tari ki ke haka Nana?"
Kawai ta ga Nana ta tashi, ta yi waje. Ta riƙe ta ta ce "Ina za ki ke?"

Idanunta a rufe, fuskarta a murtuke ta ce "Ba ki ji Sayyid ne yake kirana ba?"

"Waye hakan?"

"Mijina mana" ta faÉ—a a fusace.

"A'a babu wanda ya kira ki fa"

Nana ta fara ƙoƙarin fizge hannunta ta ce "Yanzun nan fa ya fita daga ɗakin nan"
"Nana babu kowa fa a gurin nan, daga mu sai ke"

"Ni ki cika ni, na ji Muryar mijina gurinsa zan je yana kirana"

Tsawa ta daka wa Nana ta ce "Ina magana ki na ɗaga mini murya? Wuce ki zauna babu wani wanda yake kiran ki" Nana ta buɗe idanunta, ta kalli Mamanta, sai dai ba ta yi magana ba, kawai ta ga Nana ta yi baya za ta faɗi. Ta riƙe ta ta kwantar da ita. Jikin Nana ya hau karkarwa, idanunta na fitar da hawaye.
Cikin matsananciyar damuwa take kallon Nana, tana tunanin dama har zuwa yanzu, tana fama da larurar nan?.

Ta rungume Nana a jikinta, ta kama goshinta, ta fara karanta mata Suratul Jinn, tana tofa mata a fuskarta. A hankali jikin Nana ya saki ta fara bacci.
Ta yi shiru tana kallon fuskar Nana, tana tuna lokacin da take rungume da ita tana jaririya, cike da so da ƙauna.  Tare da tuno irin soyayya da rawar ƙafar da Isa ya din ga yi lokacin da aka haifi Nana, ba ta taɓa tunanin zai yi wannan riƙon sakainar kashin da rayuwar Nana ba.

Adda Saude ce ta yi sallama, Mama ta amsa mata.

Ta É—an yi turus ta ce "Ya dai Nanan ba ta da lafiya ne, na ganta a kwance a jikinki haka?"

"Wallahi kuwa, shigo daga ciki" ta zauna ta ajiye kayan da ta zo da su. Ta ce "Tun jiya na so zuwa, tun da muka yi waya da ita da ta ce mini tana garin nan, babansu ne baya nan bai dawo da wuri ba ga yara gidan babu kowa. Ikon Allah ciki ne ma da ita haka?"

"Ga shi nan dai, har ya yi girma ma"
Chapter 26 · 0% Book details