← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 78

Sashe 22

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya yi maganar yana taɓa wuyanta "Sanyi ki ke ji Rayuwata"

"Eh, amma ba sosai ba"

"In baki ɗumi ne?" Yayi maganar muryarsa ƙasa-ƙasa

Dariya ta yi ta ce "A'a na yafe, ƙona ni za ka yi"

Shi ma dariyar ya yi ya ce "To ni ki bani sanyin ina so" Ya yi maganar da sigar shawaɓa.

"Wai kai ba ka jin bacci ne? Kawai ka farka cikin dare?"

"Soyayya ce ta tashe ni" Sai da jikin Nana ya É—an yi sanyi, ta ce "Soyayya kuma Sayyid?"

"Eh, je t'aime ma femme"

"To ai ban san me ka ce ba"

Ya yi kissing ɗin goshinta ya ce "Ina sonki matata" wani abu ne ya tsirgawa Nana, tun daga tsakiyar kanta, har tafin ƙafarta.
Shafa hannunsa ta yi, kamar mai tantamar abin da ya ce, ta ce "Sayyid"

"A'a, kar ki yi tantama, ko ki yi kokwanto, shi yasa na baki sunan Rayuwata. Ko a wannan Duniyar, ko ma a wace Duniyar, kawai ina son matata, saboda ita É—in Rayuwata ce. Babu abin da zai canza hakan."

"Sayyid ina tsoron idan ka tuna waye kai, ka ji ba ka so na, zan cutu da yawa, zamana da kai na shaƙu da kai sosai zuciyata ba za ta iya ɗauka ba" Ta yi maganar cikin rauni da tsoro.

Ya É—aga kan Nana, ya sanya hannunsa a wuyanta, ta lumshe idanunta hawaye na bin gefen fuskarta.

"Ƙa'idar ba za ta canza ba har abada, babu ruhin da zai samu nutsuwa a gangar jikin ɗayanmu muddin ba ma tare, ki saka haka a ranki. Sayyid yana son Rayuwarsa. Ko babu raina fatalwata za ta ci gaba da sonki" Nana ta yi ajiyar zuciya tare da dariya, ta shafa gashin kansa.

"Allah ya sa haka. Ina son mijina sosai nima" murmushi ya yi yana kissing É—in ta.

Har garin Allah ya waye, maganganun Sayyid ne ke kai komo a cikin ƙwaƙwalwa, zuciya da kuma gangar jikin Nana. Wani irin shauƙi da farinciki ne yake kama ta, da tuna kalamansa.

"Amarya" ya yi maganar yana kallon ƙwayar idonta.

"Amarya da wannan É—in?" Ta yi maganar tana nuna cikinta da ya fito sosai.

Yayi murmushi yana shafa cikin ya ce "Duk da haka amarya ce ai, ko kin manta?" Ya yi maganar yana kashe mata ido.
Ta yi murmushi tana ci gaba da ninkin kayan da ta wanke.

"Sayyid, bari na je kasuwa na nemo kayan magungunan ka, na dafa maka, ka ci gaba da sha, kuɗin hannuna sun ɗan taru, zuwa ranar Monday in Allah ya kaimu, duk yadda za a yi, mu tafi Kano Asibiti. Na ji haryanzu zuciyarka ba ta bugawa sosai, na san ƙarfin hali kawai ka ke yi"

"Gaskiya kin fiye saka ido, ya aka yi ki ka gane hakan, mai magani?"

Ta jinjina kai ta ce "Au haka ma za ka ce ko? Hmm ai shikenan, za ka ga mai magani, yau sai na wanke ka da magani na kulle ka a É—aki"

"Eh saboda cin zali ba, kuma ke ki gudu, alhalin kamata ya yi ki yi mana tare"

Ganin yadda yake rungumota ta ce "Sayyid na gama shiryawa, fita fa zan yi"

Ya ce "Na sani"

"Ka sani kuma ka ke son na ɓata lokaci? Dan Allah Sayyid jiya throughout the night mu na tare, yanzu kuma...

"Shhhh... Ba ki ji jikina ya fara zafi ba"

"Wallahi lafiyarka ƙalau, normal babu zafi a jikinka, wai wannan surutun duk daga ina?"

Haka ya hana Nana fita, har bayan Azahar, kawai ta zuba wa Sarautar Allah ido. Kuma a fuskar sa take ganin tsantsar ƙarfin hali, amma ba shi da lafiya.
Sai bayan la'asar ta marairaice ta ce "Dan Allah ka bar ni na je na haÉ—o kayan nan Sayyid, ko haryanzu ba ka gama jin Sanyin ba?"
Ya É—aga mata gira. "To ga mafici, yi ta fifita, har na dawo" Dariya ya yi yana É—an jan hancinsa. Ya kamo hannunta ya É—ora a wuyansa ya ce "Kin ji da zafi ko?"

"Ba wani zafi. Waccan ranar ma wayo ka yi mini, wai na baka sanyin jikina"

Dariya yake son yi sosai, amma sai ya yi kaɗan ya cije, ya ce "Ai ni Ƙaisar wasu lokutan taimakona yake yi"

A sanyaye ta ce "Shi me yasa ba ka kishi da shi?"

"In ji wa? Kawai abu ɗaya ne da babu yadda muka iya. Alaƙarsu ta ɗa da mahaifi tana tasiri a rayuwarmu ni da ke"
Cikin mamaki Nana ta ce "Ta yaya? Kuma ya aka yi ka san Ƙaisar ɗan Giyaz ne?"
"Yadda ki ke ganin Ƙaisar ku yi magana, haka nake ganin Giyaz, kuma na fuskanci waye shi a tattare da ni. Yanzu ki je ki dawo"
"Kai amma na yi mamaki fa, kuma ba ka taɓa gaya mini ba. Bari na je na dawo, ina da tarin tambayoyin da zan yi maka"

"Tom sai kin dawo"

Ta saka hijjabinta, har za ta fita ya kirawo ta. Ya ce "Ba ki yi mini ba"

Ta yi masa kiss a goshinsa, da bakinsa.

"Allah ya yi miki albarka. Ki kula mini da kanki, kar wani ya kula mini ke, ki kular mini da babyna ki tafi a hankali ki je ki dawo"

Ta kalli cikin ta ce "To Shugaba, in sha Allah"
"To a dawo lafiya, I love you"

Cikin murmushi ta ce "Inyee É—an gayu, ka yi furansanci, ka yi turanci, ka yi hausa ga kuma yarenku. Zan koyo yaren da baka iya ba, na din ga tashin kanka da kalaman soyayya"

Ya ce "Je ki dawo ki yi mini waƙa"

"Sai dai na je na yi maka tsifa, na yi maka sabon kitso" ya tsuke fuska yana hararata. Ta fita tana waigensa tana murmushi.

Tana fita ya jingina da jikin bango, yana dafe saitin zuciyarsa, yana haki sama-sama. Ya fito tsakar gida da kyar, ya zauna yana sake danne saitin zuciyarsa da yake jin wani irin abu kamar shocking daga zuciyarsa yana zagayawa bayansa har cikin kansa.
Tsayuwar motoci ya ji a waje, sai dai hankalinsa ba ya kan hakan. Ya ji an daki ƙofar gidan da ƙarfi. Ya ɗaga kai ya ga wasu murɗaɗɗun ƙarti sun shigo cikin baƙaƙen kaya.

Duk da mawuyacin halin da yake ciki, haka ya yinƙura ya tashi da ƙyar, ganin an shigo da Habu hannunsa da sarƙa.

Ya din ga bin mutanen da kallo, Habu cikin matsananciyar damuwa ya zube a kan gwiwoyinsa ya ce "Ka yi mini Afuwa Imam, ba laifina ba ne ka yi haƙuri, na gaza baka kariyar da ta dace" Sayyid ya din ga bin sa da kallo, da alama ma ba ya gane me Habu yake nufi.
Ƙartin nan biyu daga cikin su, suka yo kansa, suka riƙe shi.

A rikice ya ce "A'a, ku rabu da ni. Me na yi muku?"

Ƙoƙari suke su tasa shi su tafi da shi cikin salama, amma ya turje. Suka juya yare zuwa faransanci, su na rarrashin sa, ya wuce su tafi.

"Ba zan je ko ina ba? Ina zan tafi na bar matata" Habu ya din ga girgiza masa kai da alamar ya daina faÉ—ar maganar da yake yi.

"Ku rabu da ni, ina zaku kai ni na tafi na bar Nana" maganar da yake yi cikin ɗaga murya, ga ƙoƙarin turjewa da yake yi, ya sanya zuciyarsa yin rauni, ya yi baya zai faɗi. Suka tare shi suka saɓa shi suka yi waje da shi.
Aka saka Habu a cikin wata motar daban, Sayyid kuma aka saka shi a cikin wata baƙar Highlander mai tint glass, aka rufe suka tafi da shi.

Nana tana tsaye ta bayar da kuÉ—i, za a bata kankana, dan daga ita har Sayyid, kawai ta ji gabanta ya yi wata irin mummunar faÉ—uwa. Ta yi shiru, ta jiki gaba É—aya jikinta ya yi sanyi. Kawai ta juya ta tafi. Mai kayan yana ta yi mata magana, amma ba ta tsaya ba, ta nufi gida har da É—an gudu saboda azabar sauri.
Tana zuwa ƙofar gidan ta ga ƙofar gidan a ɓalle, da hanzari ta shiga gidan, tana kiran sunan Sayyid. Amma wayam ba ya nan, ta shiga ɗaki baya nan. Ta duba banɗaki nan ma ba ta gan shi ba.

Ta fita waje da sauri, tana kalle-kalle, ta tafi hanyar inda bishiyar kukar nan take, tana tunanin ko jikinsa ne ya motsa, ya tafi can, sai dai can ma baya nan.
Ta sake komawa gidan cikin tashin hankali, da wani yaro da yake zuwar mata aike ta haɗu a ƙofar gidanta ta ce "Ashiru, ko ka ga Sayyid ya fito daga gidan nan? Wannan mutumin na gidana farin nan?"

"Wasu mutane ne suka shiga gidan suka tafi da shi, a mota suka zo"

Sak Nana ta tsaya, tana ƙure Ashiru da ido, tamkar ma ba ta gane yaren da yaron yake yi.

Ayshercool
08081012143

60

Cikin rawar murya Nana ta ce "Wace irin mota kuma Ashiru? Ka tabattar kuma Sayyid ne?"

"Wallahi na tabattar, ina nan ina wasa suka zo, a motoci wannan farin na gidanki suka É—aukko."
Tamkar mahaukaciya ta bi sahun motar, ita ce har titi ko za ta ga motar da Ashiru ya ce, amma babu wata alama na za ta ga motar da aka daukar mata Sayyid aka saka a ciki.
Gaba É—aya ta kasa kuka, sai tsuma da jikinta yake yi tamkar mazari. Tuni rana ta faÉ—i, an fara kiran sallar magariba, ba ta san tafiyar da ta yi da nisa ba, sai da ta tashi dawowa.
Gidan Uwani ta nufa, ta tarar da ita ta yi alwala, za ta yi sallar magariba.
Uwani ta ce "Ke Nana, uban me ya fito da ke da magaribar nan, ga juna biyu kina da shi, duk da na san ba ki da ɗan aike amma koma mene ne, ai kya bari a idar da salla ko?" Nana ba ta yi magana ba, ta nemi guri ta zauna a ƙasa.
"Ke lafiya kuwa?" Uwani ta yi maganar tana tattara hankalinta a kan Nana. Amma Nana ta kasa magana, sai murza zoben hannunta da take yi, tana ajiyar zuciya.
"Ke ki yi mini magana, kar ki tayar mini da hankali mana".
"Sayyid ne ya ɓata"

"Kamar yaya sai ka ce wani zakara?"

"Da gaske nake"
Chapter 22 · 0% Book details