Sashe 23
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To ai ban gane ya ɓatan ba ne? Mutumin da yake jinyar ne ya iya tashi ya fita har ya ɓata?"
"Ai kwana biyu jikin da ɗan sauƙi, dan har ya ce mu zo nu gaishe ki" Ta yi maganar ba tare da tana iya tantance me ma take faɗa ba.
"A'a Nana, wataƙila dai wani wajen ya je zai dawo. Tashi ki yi sallar magariba, zuwa anjima a raka ki gidan ko ya dawo"
Nana jin Uwani kawai take yi, ta tashi ta yi sallar magariba, aka yi isha'i. Uwani ta saka Nana a gaba zuwa gidanta, sai dai kamar yadda Nana ta bar gidan wayam babu Sayyid babu dalilinsa.
Nana dai ba ta gaya wa Uwani abin da Ashiru ya gaya mata ba, na ya ga an zo da mota an tafi da shi ba.
Sai wajen goma na dare, hankalin Uwani ya tashi. Ta sanar da samarin gidan halin da ake ciki. Nan suka bazama a cikin Buda yawon neman Sayyid, duk da galibi ma ba su san shi ba, kwatancensa Uwani ta yi musu, suka tafi yawon neman sa, har gurin jami'an tsaro aka kai rahoto.
Sai dai har bayan sha biyun dare, babu wanda ya ji ko É—uriyarsa.
Uwani ta saka aka rufe gidan, ta ce Nana ta zauna a nan, ko zuwa dare zai dawo.
Nana a ranta ta ce "Wane dare kuma bayan wannan"
Daren ya zame wa Nana dare mafi tsawo a rayuwarta. Damuwa da tunani ya cika mata zuciya. Ba ta tunanin Sayyid zai iya tafiya ya bar ta. Idan kuma da gaske zuwa aka yi aka tafi da shi, to suwaye su ka tafi da shi? Ina suka kai shi, me ya yi musu? Ko dai wani laifin suke aikatawa ba ta sani ba? Amma shi da yake kwance babu lafiya, kullum tana tare da shi a gida, yaushe har yake aikata wani rashin gaskiya da ba ta sani ba.
A haka har aka yi assalatu, a kan kunnenta.
****
Dare malafar rana, kowa ya bika ya shirya maka.
Danƙareriyar mota ce, ƙirar highlander baƙa, take ta kwarara gudu a saman kwalta, tamkar hanyar domin direban kawai aka yi ta.
Gefe da gefen hanyat baki É—aya babu komai, banda yashin sahara, sai busassun bishiyu jefi jefi. Kasancewar dare ne, wata ya kai kwana goma sha huÉ—u, ya haska ko ina, ga taurari sun yi wa sararin samaniyar ado.
Titin ta tsakiyar sahara ya ratsa, wadda yashin saharar ya bayar da sassanyan yanayi.
Kallon sa ya yi, daga bisani ya ce "Kilomètre nawa ce ta rage mana ne?"
Direban ya waiwayo ya kalli mai maganar wandaa fuskarsa a rufe take cikin rawani ya ce "Bai fi 95 kilomètre ba"
"Dans quelques minutes ?? (Nan da wani lokaci?)".
"Bai fi awa É—aya ya rage mana ba"
"Dole fa mu ƙarasa dai-dai lokacin da aka umarce mu, ni ina tsoron ma kar ya farka. Ka ƙara sauri"
Ya yi maganar yana haska fuskar Sayyid, da yake kwance a jikinsa ya haɗa gumi, cikin wani yanayi kamar bacci kamar suma, sai dai yadda yake gumi ya nuna a wahale yake baccin, babu in da yake motsi a jikinsa, sai ƙirjinsa da yake ɗagawa yana sauka lokaci zuwa lokaci, numfashinsa yana fita da ƙyar.
Ya kai hannunsa, ya ɗora a kan ƙirjin Sayyid, idan zuciyar sa ta buga sau ɗaya, sai ta jima kafin ta sake bugawa. Sai dai duk bugawar da za ta yi, da ƙarfi take bugawa tamkar za ta tsaga ƙirjinsa ta fito dummm!.
Cikin damuwa ya ce "Lowalli, sai ka ƙara gudu fa, kar ya mace mana, bugun zuciyarsa raguwa fa yake yi. Kuma ka san idan ya mace mana mun shiga uku mun lalace"
Lauwalli ya jinjina kai yana ƙara gudun motar. Ya ce "In sha Allah a raye za mu kai shi, ba za a samu matsala ba. Dan dai ka ƙi yarda ne, da na ce mu tsaya a Asibiti".
"Kai dalla ka daina maganar tsayawa a wani Asibitin nan. Ka yi ka hanzarta mu cika umarnin nan, mukaÉ—ai ake dako"
"To shikenan, mun kusa in sha Allah" ya yi maganar yana ƙara gudun motar.
****
Antin Yusra ce ta kalle ta, ta ce "Yusra duk wannan kwalliyar fa? Ta karɓar baƙon ce?"
"Eh mana Mami, yana hanya ma ai" ta yi maganar tana tafiya É—akinta, ta fesa turare.
Wayarta ce ta fara ringing, ta É—aga wayar tana murmushi ya ce "Gani a layin"
"Duba lambar gidan, za su buÉ—e maka"
Ya ce "Ok"
Bayan mintuna goma sha biyar, ta fito ta ce "Mummy na tafi"
"To a gaida baƙon, ya tabattar mana da alkhairi"
Kawai ta fice tana murmushi. Tana zuwa ta gan shi a tsaye a cikin falon, yana kallon ƙaton frame na hoton mai gidan, da yake retired soja.
Ganin abin take tamkar a mafarki, wai Sagir É—in ta ne a gabanta.
Jin ƙamshin turarenta ne ya sanya ya waiwaya.
Da gudu ta ƙarasa inda yake ta faɗa jikinsa.
Babu tunanin komai, Sagir ya ƙanƙame ta a jikinsa, bar siririn mayafin da ta yafa a kanta, yana zamewa gyararren gashin kanta, da yake ta ƙamshin mayuka ya bayyana.
Ya din ga shafa bayanta yana murmushi, kawai ya ji tana sheshsheƙar kuka. A ɗan rikice ya ce "Lafiya, kuka kuma Yusra?"
Ya zauna tare da ita a jikinsa, ya ce "Ina ta murna zan zo na gan ki, amma in zo ki din ga kuka, ko ba kya son ganina ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"To mene ne"
"Ka daina so na, tun da ka sake ni ba ka ƙara nema na ba" Ya ɗago fuskarta su na kallon juna yace "Da na daina son ki, ba zan zo nan ba Yusra, kin san yadda rabuwarmu ta kasance, ban daina sonki ba, ban kuma daina tunanin ki ba"
"Almost three years, ba ka sake nema na ba"
Sagir ya marairaice murya ya ce "To yanzu ba gani na zo har nan saboda ke ba? Haba wifey" ta zumɓura baki cikin ɗabi'arta ta shagwaɓa. Duk da ya zuciyarsa na tunatar da shi, tare da gargaɗin sa a kan Yusra ba muharramarsa ba ce, amma ya kasa yaƙar kansa, ya ƙyale ta a jikinsa yana jin yadda ya yi kewarta.
"Talk mana, na zo kuma kin haÉ—e rai?" Tashi ta yi daga jikinsa, ta zauna a kusa da shi ta ce "Ya hanya?"
"Alhamdillah, ki na lafiya ya jikin naki?"
"Da sauƙi"
"Kin warware?"
Ta girgiza kai ta ce "Bayan ƙin yadda ku ka yi da gaske ba ni da lafiya. Sai ga shi na haɗu da wata Nana, ita ma tana irin ciwon da nake ji, ai ita ta san ba ƙarya nake yi ba."
Ya ce "To yanzu dai duk ba wannan ba, i miss you Yusra, irin sosai da sosai É—in nan fa"
"Bayan ka yi aurenka, ba wani missing ɗina da ka yi" ta yi maganar tana tsiyaya masa lemo a cup ta miƙa masa.
Ya karɓa ya kai bakinsa yana tsare ta da ido. Ta kalli screen ɗin wayarsa da ya kawo haske, hoton Haidar ya bayyana a kan screen ɗin. Ta ɗauki wayar tana kallon yaron ta ce "Waye wannan?"
"Ɗanki ne Haidar, recently ma ta kuma haihuwa ɗan ya rasu" ta yi masa wani kallo, da bai tantance na mene ne ba ta ce "Da tuni nima wataƙila na haihu"
Ya yi murmushi ya yi shiru, yana cin abincin da ta zuba masa. Cikin hikima ya karkatar da zancen suka ci gaba da hira.
Wayarsa ce ta fara ringing, ta ajiye masa ganin hoton heart a kan sunan. Ya É—aga wayar tare da yin sallama "Hello love"
"Ka sauka lafiya?"
"Alhamdillah am good dear"
Shukura ta ce "To sai ka dawo, Allah ya tsare mana kai, take care"
Ya yi murmushi ya ce "In sha Allah dear" wani abu ne ya tokare wa Yusra a ƙirji, ta zuba masa ido.
Ya ajiye wayar, bai kalle ta ba ya ce "Yusy, kin san na yi missing É—in girkinki over?"
Jin ta yi shiru ya sanya ya É—aga kai ya kalle ta, ya ga tana hararsa. Ya yi murmushi ya É—ebo Abincin ya kai bakinta.
Ta murguÉ—a masa baki ta tsuke fuska.
"Smile, haba sweetheart" ta buÉ—e bakin ya saka mata Abincin. Haka ya ribace ta, suka ci gaba da hira.
A nan ya yi sallar la'asar, sannan ta fito raka shi.
A jikin motarsa suka tsaya, tana yi masa wani irin kallo mai ƙayatarwa.
"Tom sai yaushe zan dawo?"
"An jima kaÉ—an"
Ya yi murmushi ya sake kallon ta ya ce "Yusra"
Ta ce "Na'am"
"Yaushe za ki dawo gidana, ji nake kamar na É—auke ki, na tafi da ke Kano, ina kewar ki sosai da sosai. Yaushe za ki dawo gidana?"
Ta girgiza masa kai ta ce "Ba zan dawo ba"
Cikin mamaki ya ce "Saboda me?"
"Ka auri wata, kuma Hajiyarka ba za ta bari na dawo ba, su Mami ma ba za su bar ni ba, kuma ma haryanzu ban gama warkewa ba"
"Haryanzu ki na so na?" Ta kalle shi ta sunkuyar da kanta ƙasa.
"Idan ba kya so na, me yasa ki ka nemi lambata, ki ka kira ni? Kuma har ki ka ba ni dama na zo?" Ta sunkuyar da kanta ta ci gaba da murza yatsun hannunta.
"Yusra Sagir É—in ki ne fa, É—ago ido kalle ni" Kawai ya ga hawaye na bin fuskarta.
"Sagir ɗina, da ya rabu da ni, saboda ba ni da lafiya ba" Ta yi maganar tana sheshsheƙa. Ganin babu kowa a gurin da suke, ya sanya ya janyo ta jikinsa, ya ɗago kanta yana kallon idonta ya ce "Yusra, ki na so na haryanzu?" Ta yi shiru hawaye na ci gaba da bin idanunta.
"Ki na so na har yanzu, shi yasa ki ka neme ni. Dan haka batun ina da aure, Hajiyata ba za ta bari ba, 'yan uwana ba sa son ki, haryanzu ba ki da lafiya, duk ba ta taso ba. Za ki dawo gidana a karo na biyu in sha Allah. Haryanzu ina son ki Yusra"
"Amma...