Sashe 44
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ko? Amma idan an yi magana sai ki nuna kamar babu wata halitta da ta kai ɗan Adam tsarki da tsoron Allah. Allah ya karrama ɗan Adam a kan dukkanin halittunsa. Amma ba duk ɗan Adam ne mai tsarkin zuciya ba. Wannan zubar da jinin da kashe-kashen da yake rubuce a cikin littafin nan, da gaske an yi su, domin cimma buƙatar Duniya, kuma haryanzu ana kan yi ma. Abu ne da ya faru wani ƙarni a baya, kuma abin yake ta bibiyar zuriyar har wannan zamanin. Na ce ki karanta kin ƙi, kin ce ba kya so shikenan ba zan yi miki dole ba, amma bari ki ga wani abu.
Ya ɗauki littafin ya buɗe cikin wani feji, ɓangare ɗaya na bangon littafin zane ne, ɓangare ɗaya kuma bayanin yadda taswirar zanen take ne. Ya haska littafin a jikin mudubin.
A nan take hoton ya bayyana a jikin mudubin, wannan ɗakin da take ganinta a ciki ita da Sayyid shi ne ya bayyana a jikin mudubin, ba iya haka ba har ƙamshin da gurin yake yi ta fara ji a hancinta.
A rikice ta ce "Nan gurin? Dama ina son sanin ina ne, yaya aka yi muke zuwa gurin nan ni da Sayyid, kuma idan abu ya faru a gurin kamar gaske."
Ƙaisar ya rufe littafin ya ce "Ai kuma kin yi wa kan ki, ba zan bayar ba. Ya jefa littafin sama ya ɓace ɓat ita kuma ta tashi daga baccin.
****
Kwana biyu Jamila ba ta je gidan Hajiya Sa'a ba, saboda jikinta da ya matsa, idan Abba ya kira wayarta a kashe, ga shi ba ta zuwa gidansu, shi ba abin ya tambayi Mummy ba.
Yana kwance a ɗakinsa, ya tura mata saƙo. "Hankalina a tashe yake ƙanwata, dan Allah ki yi mini ko flashing ne, hankalina na matuƙar tashe dan Allah ki ɗaga wayata"
Ya tura mata saƙon, tare da ajiye wayar.
Hajjya Sa'a ce ta shiga É—akin nasa, ta iske shi a kan kujera. Yana ganinta ya tashi zaune. Daga tsaye ta ce "Abba ba zaka fita bane? Baka fito ka karya ba, kuma baka fita kasuwa ba meyafaru ne?"
Ya girgiza mata kai ya ce "Babu komai fa"
"A'a akwai wani abu, na kasa gane kan ka 'yan kwanakin nan, hatta shirin bikinka nikaÉ—ai nake abina, me yake damunka? Duk saboda Jamila ne?"
Ya girgiza kai ya ce "Ba kin ce ba kya son alaƙarmu ba, ni kawai ba ni da lafiya ne" ta yi shiru tana nazartarsa, kawai ta yi ƙwafa ta fice daga ɗakin.
Ya koma ya jingina, ya lumshe idanunsa, sai kiran Jamila. Ya ɗauka ya katse kiran ya kira ta cikin azarɓaɓi ya ce "Ƙanwata lafiya kuwa? Ba kya ɗaga wayata ko haryanzu kina fushin ne?"
Cikin numfarfashi ta ce "A'a Yaya Abba, ba ni da lafiya ne haryanzu"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ya aka yi ba ki gaya mini ba? Kina gida ne?"
"Eh" ta amsa muryarta ƙasa-ƙasa.
"To shirya gani nan, bari na zo mu je Asibiti"
"To Yaya Abba, na gode" ta ajiye wayar da ƙyar. Hankalinsa ya yi mummunan tashi, a zatonsa aika-aikar da ya yi ce, ta sanya mata rashin lafiya har haka.
Da sauri ya zura kaya, ya É—auki mukullin motarsa ya yi waje ya tafi gidansu Jamila.
Yanayin yadda Jamila ta fito, tamkar ya je ya É—aukko ta, fuskarta duk ta kumbura, da alama tana jin jiki sosai da sosai.
Ya buɗe mata gaban motar ta shiga. Cikin tausayawa ya ce "Sannu ƙanwata, haka jikin naki ya yi ba ki gaya mini ba?"
"Ba na son tayar maka da hankali ne, kai ma ba ka da lafiya, amma Mama fa ta kai ni Asibiti" Gabansa ya faÉ—i ya ce "Allah ya sa ba ta gane komai ba"
Ta girgiza kai ta ce "Babu abin da ta gane, zazzaɓi ne fa kawai"
A tsorace ya ce "Jamila ko ciki ne?"
Ta kalle shi, sai da ta ji kamar ta yi dariya, duk da halin da take ciki. "Tun kan hakan ta faru ai nake rashin lafiya, ba wannan ba ne ba, ba wani ciki".
Ya sake cewa "Amma duk da haka kamar ya assasa miki ciwon, amma bari mu je Asibitin" haka ya ja motarsa su ka bar layin.
Safiyya ce ta tarar da Hajiya Sa'a ta cika ta yi fam, tana zaune a falonta.
Da kyar Hajiya Sa'a ta iya amsa mata sallamarta. Ta zauna a kusa da Hajiya Sa'a ta ce "Mummynmu maganin kukanmu, lafiya kuwa na ga ranki a ɓace?"
"Ba dole ki ganni a haka ba? Da gaske fa Abba son Jamila yake yi, nema yake ya bujire mini, kin ga yadda duk ya damu saboda na raba su. Ga bikinsa na ƙaratowa da Yasmin.
Maman Khairat ta tuntsure da dariya ta ce "To meye a ciki, idan tana son sa ki bar su mana"
Hajiya Sa'a ta kalle ta ta ce "Amma ba ki da hankali, yarinyar da shugaban ƙungiya suka kwanta da ita, sai Abba ya auri ragowa? Ba ma wannan ba, kar ki manta idan ƙungiya ta buƙaci ta bayar da jininsa fa, shikenan ta bayar da jinin tilon ɗan nawa?"
Maman Khairat ta ce "Na fahimce ki Mummy, da wasa nake yi miki, amma maganar gaskiya yanzu haka kan na taho ma, na ga motar Abba a unguwarmu, kuma na san ba ku da kowa a unguwar, dan haka gurin Jamila ya je"
Cikin matsanancin ɓacin rai ta ce "Gurin Jamila kuma? Yarinyar nan ta zame mini masifa da bala'i ko? Maganinta zan yi, wallahi sai ta rabu da Abba, ko ita ta haifar mini shi"
Maman Khairat ta ce "Ki yi dai a hankali, kin san halin yaran zamanin nan" Hajiya Sa'a ta ci gaba da huci, tamkar macijiya saboda takaici.
Maman Khairat ta ce "Ina dai ƙara gaya miki, ki bi komai a sannu, kin san halin yaran zamanin nan, sai su baki mamaki. Shi kansa Abban duk yadda yake yi miki biyayya, idan ba ki yi wasa ba, a wannan karon tsaf zai bujire miki".
"Ai ga alamu nan ina gani, amma ni zan sanya wa Abba doka, na hana shi abu, amma ya zagaye ya je ya aikata? Shikenan, na san matakin da zan É—auka. Da ni suke zancen.
Alhaji Fatuhu ne zaune a harabar gidan sa, a kan kujera, ya kan É—an iya dogara sanda ya tashi tsaye yanzu. Idan aka taimaka masa har harabar gidan yake iya fitowa, duk da idan jikin ya tashi kuma, sai ba ya iya hakan ko kaÉ—an.
Yana zaune a harabar gidan, yana kallon ƙaramin ɗan sa na gurin Fadila, yana ta wasa da Ball, yana jin yadda ƙaunar ɗan ke ratsa masa zuciya. Gefe guda yana tausayin yaron nasa, dan bai taɓa iya saya masa abin naira biyar ba da kuɗinsa. Hatta abincin da suke ci, 'yan uwa da abokan arziki ne suke kawo musu, ga shi wanda ya sai gidansa ya ba du aronsa suke zaune a ciki, ya fara ƙishin-ƙishin ɗin yana buƙatar gidan.
Fadila ce ta ƙaraso tana murmushi ta ce "Daddy kallon Ball ka ke yi?"
Ya yi murmushi ya ce "Eh mana, yana ta in tashi mu yi tare, ina ma zan iya da ko sau É—aya mun yi tare, no na saka shi farinciki"
Ta zauna a É—aya daga cikin fararen kujerun, ta ce "A hakan ma, ka na sanya shi farin ciki ai"
"Fadila"
Ta tattara masa nutsuwarta ta ce "Na'am Daddy"
"Kin san wani abu?"
Ta ce "A'a sai ka faÉ—a"
"Ina yarinyar nan Nana?"
"Wace Nanan?"
Ya É—an yi shiru sannan ya ce "Malamar Muhsin, da yake faÉ—a"
Ta ce "Ohh Allah sarki, na tuna ta"
"Mafarkinta nake yi"
Ta É—an yi saroro ta ce "Mafarki kuma?"
"Eh Fadila, har aikawa na yi gidansu, a yi mini alfarmar a faÉ—a mini inda gidanta yake, wani abu nake gani da ya fara damuna"
Ta danne kishinta ta ce "To ka yi mini bayani mana"
"Kin dai san ni ba ma'abocin, biye-biye ba ne ba, da yarda da harkokin shirme da zai sanya na ji wani zai iya cutar da ni ba, amma a jere sau kusan biyar ina mafarki da ita".
Cikin ƙosawa ta ce "Daddy ka yi mini bayani, ka na ta kwana-kwana da ni"
"Ganinta nake yi a mafarki, tana ce mini an yi mini sihiri, karo kusan biyar fa"
Fadila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kuma ka yarda?"
"Ba ma son na yarda na gazgata hakan, amma na ji kamar na fara amincewa, saboda yadda nake ganinta abin ya yi yawa, ya wuce a ce shirmen mafarki ne kawai."
Fadila ta numfasa ta ce "Ai ni tuntuni na zargi hakan, amma sanin halinka na rashin son irin wannan abubuwan, ya sanya ba na yi maka maganar. Ko wannan sauƙin da ka ke samu, na san tasirin addu'a ne. Dan kuwa Umma kuɗi take bayarwa ana sauke karatun Alqur'ani."
Cikin mamaki ya ce "Amma ke kina ganin, akwai wanda zai damu da ni, har ya iya yi mini sihiri? Ina azkar É—ina da addu'oina, gani nake sun wadace ni, babu wanda zai damu da ni ya yi mini wani sihiri."