← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 78

Sashe 55

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana ta yi turus tana tunanin a ina za ta zauna, sama ko ƙasa.
Matar ta kalli Nana cikin zare ido ta ce "Ke ki rage tsawon ki, kin tsaya mata a ka"
Nana ta ja guri ta zauna a kan carfet É—in ita ma.
Asal kamar ba za ta yi magana ba, sai da ta gama iyayinta ta sauke ƙafarta ƙasa ta dubi Nana ta ce "Amm na saka an kirawo mini ke, saboda ki san abin da na kawo ki gidan nan ki yi. Ke dai da ganin gidan nan kin san ba gurin da za a yi wasa ne ko shirirta ba, babban gida ne na mulki.
Saboda dalilin girki da kuma wani dalili na ƙashin kaina, ya sanya na kawo ki gidan nan. Ba a ɗaukko bare wanda yake ba jinin gidan nan ba, ko ƙabilarmu ba ya yi mana aiki, amma na ga wasu abubuwa a tattare da ke da ya sanya na kawo ki cikin gidan nan.
Kamar yadda na gaya miki, ina ƙara jaddada miki, zaman ki a gidan nan dole ki yi taka tsantsan, babu ruwanki da shishshigi, saka ido, gulma ko kuma shiga abin da babu ruwanki.
Sannan kar ki kuskura wani ya ce zai haÉ—a kai da ke a yi wani abu, rayuwarki za ta iya salwanta ba tare da kowa ma ya sani ba, dan haka sai ki san irin zaman da za ki yi."

Nana ta yi shiru ta gama sauraren ta, sai dai har a lokacin ba ta ji dalilin da ya sanya Asal kawo ta gidan ba, dafa abinci kowa ma zai iya mai yasa sai ita.

Wannan matar da ta tarar a zaune, ta tafi da ita, ta kai ta gurin da ake girke-girken abinci, da gaya mata yadda jadawalin girke-girken gidan yake. Ta É—aukko kayan ds Asal ta bayar a ba ta, na kayan shafe-shafe da mayukan wanka zuwa kayan sakawa.
Da Nana ta koma É—akinta, ta kalli kayan ta fara tunanin Allah ya sa ba kwance Asal ba ne, dan gara ta saka kwancen Ashura da ta saka na Asal, da ba ta da mutunci.
A washegari Nana ta fara aiki a wannan madafa, sai dai madafar daban-daban ce. Akwai wadda ake girkin da ma'aikatan gidan ne suke ci, akwai wadda na baƙin da suke zuwa ne, sai kuma masu girka wa Asal abinci daban, dan haka Nana na cikin masu yi wa Asal girki.
Sosai matar nan ta ƙara jan kunnen Nana, a kan ta kula da kanta, dan muddin aka samu matsala ba za ta sha ba.
Nana a ranta ta ce "Ji wata jaraba, da wannan wahalar mutum ya girka abin da zai ci mana da kansa."

Kwana huɗu da fara aikinta, ranar Alhamis da daddare, tana shirin kwanciya, aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta.
Ta tashi ta buÉ—e, ta ga shugabar girke-girke ta gidan, kamar yadda aka gabatar mata da ita a baya.

"Ki sako hijjabinki, ki biyo ni"

Nana ta saka hijjabinta ta fito tana tunanin ko lafiya.

Harabar gidan matar ta yi, Nana ta bi bayanta, ta nuna mata mota. Nana ta kalli dare ya yi kuma an zo da mota an ce a tafi da ita.
Cike da mamaki Nana ta shiga motar, sai ta ga mutum uku, da su ma duk tare suke aikin girkin a gidan a cikin motar.

Ta shiga ta zauna, ita ma shugabar ta su ta shiga. Nana ta gaza haƙuri ta ce "Dan Allah ina za mu je ne?"

"Za ki gani"

"Eh amma na ga dare ne fa"

"Idan mun je za ki ji dalilin fitar" Nana ta yi shiru tana tunani, ita ba ma wannan ba, hankalinta ya koma kan rashin samun damar kiran waya da ba ta iya yi, kuma ba a kiranta ya shigo. Dan sai da ta tambayi ɗaya daga cikin masu aikin, ko matsalar daga wayarta ne, ta ce mata kar ta kuskura ta bari ma a san tana da waya, dan sai an ƙwace ta.

Tana ta zancen zuci, har suka isa inda aka tsaya suka sauka, aka shiga da su.

Asal ce a tsaye, tare da dattijuwar matar da ta saka ta raka Nana masauki. Suna tsaye a cikin É—akin Nanan.

Asal ta ce "Zazzage mini kayanta, ki É—aga mini komai É—aya bayan É—aya"

Ayshercool
71

ÆŠaya bayan É—aya, aka din ga zazzage kayan Nana. Aka zazzage su tsaf aka Azzage jakar da ta zuba kayan turarukanta da mayukan shafawa, duk ba ta ga wani abu ba, sai jakar gurin sarkin baka.
Ta nuna jakar ta ce "Mene wannan?"

Ta É—ago jakar ta ce "Jaka ce"

"BuÉ—e ta ki zazzage na gani" Ta fara kokowar buÉ—e jaka, amma babu gurin da zata buÉ—e ta. Kawai ta ce "Shikenan" ta fice ta bar É—akin.

Can gurin kuma Nana tara su aka yi, su shida. "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya aka kawo ku nan, to zaɓo ku aka yi saboda an yarda da amanarku, ana daf da yin taro da Sultan da kuma dukkanin Imams na gidan nan. Dan haka ku aka zaɓo za ku yi girki na musamman. Amma ku sani kamar yadda wasu sani wasu ba su sani ba, muddin aka samu wata matsala ko ƙware wani ya yi, a sanadin abincin da ku ka dafa, to ku tabattar da rayuwarku za ku biya. Dole ku yi taka tsantsan ku kula." Matar ta yi maganar daki-daki.

"In sha Allah" suka amsa mata.

Ta ce su bi bayanta, suka je wani ƙaton guri, ɗauke da nau'oin kayan masarufi kala-kala. Ta yi musu bayanin da su ne za su yi amfani su yi girkin, sannan ya zama dole su sanya wa bakinsu sakata su yi aiki cikin amana, kuma kada wanda ya san su aka zaɓa da za su yi wannan girki. Nan ma suka amsa, ita dai Nana sai kallo da ido, dan abubuwan sun daina ba ta mamaki, wannan maganar ce ta sanya aka taso ta a daren nan, sai ka ce wanda za su girkawa wasu waliyyai abinci.

Ko da aka mayar da su Nana gida, ta sha mamakin ganin kayanta a hargitse a cikin ɗaki. Da mamaki ta ƙarasa kan kayan nata, ta ɗaɗɗaga.
Cikin takaici Nana ta tashi ta fita, sai dai kowa ya tafi makwancinsa ya kwanta. Kawai ta ji taku a bayanta. Ta waiwaya ta ga Asal na fitowa.

"Har kun dawo kenan?"

"Eh, sai dai na shiga ɗakina na tarar da an caje mini kayana an zubar da su a ƙasa, ban sani ba ko kina da masaniya a kan haka?"

Asal ta ce "Me yasa ki ka zarge ni?"

"Saboda na ga ba a gudanar da komai a gidan nan sai da izninki"

Asal ta yi murmushi ta ce "Haka ne, kina da kaifin ƙwaƙwalwa kamar yadda na yi tsammani, ni na saka aka caje kayanki saboda na san da wa nake zaune"

"Me yasa ba ki tambaye ni abin da ki ke buƙatar sani ba, za a caje mini kaya"

"Saboda a ƙarƙashina ki ke, a gidana ki ke zaune dole na sani idan da wani abu da ki ke tattare da shi na cutarwa"

Nana ta ce "Kin yi kuskure, dan ina zaune a ƙarƙshinki, ina da personal life ɗina, da 'yancin adana abin da yake sirrina, bai halatta ki bincikar mini kaya a bayan idona ba. Yaushe na san ki, da zan ƙulla wani abu da zan cutar da ke? Kina gudun hakan ki jawo ni ki ka kawo ni?"

"Yi ƙasa da muryarki, kar ki kuskura ki ɗaga mini murya, kin san matsayina? Za ki iya janyo wa kan ki gagarumar matsala muddin ki ka ci gaba da yi mini magana ba ladabi"

"Babu ruwana da matsayinki, da koma me za ki yi mini, kar ki sake shigar mini ɗaki ki taɓa mini kaya, idan kuma ki ka ci gaba za ki iya binciko abin da zai hana ki sukuni, idan kin ji ba ki yarda da ni ba, ki sallame ni na koma inda na fito, ba zai yiwu na zauna da ke kina zargina kuma kina cin dunduniyata ba."

Asal ta bi Nana da kallon mamaki, amma ta danne mamakinta ta haÉ—iye fushinta, ta ce "Gaskiya ne, kin yarda da kan ki har haka kenan? Shikenan amma idan na ga akasin abin da ya fito daga bakinki, za ki sha mamakin abin da zai faru"

Nana ta yi mata banza, ta koma É—akin nata, ta gyara kayanta tsaf.
Ta kulle ɗakin ta koma ta ɗaga katifar ɗakin, ta ɗaukko wata jaka, a cikin jakar ta zuba duk tarkacen kayan Sayyid. Ajiyar zuciya ta ts yi, da tayi wannan dabarar ta ɓoye su. Haka kurum take jin kayan na buƙatar sirri.
Ta nemi guri ta kwanta tana sauke numfashi a hankali, tana tunanin yadda rayuwa ke ta jujjuyata.

*****

Shukura na zaune a ɗakinta tamkar zuciyarta za ta yi bindiga ta fito, Sagir ya buɗe ƙofa ya shigo ɗakin. Kallo ɗaya ta yi masa ta sunkuyar da kai. Tuni t yi shirin kwanciya baccinta, sai ƙamshin turare take zubawa.
Ya sha manyan kayansa, hannunsa riƙe da baƙaƙen ledoji. Ya zo ya zauna a kusa da ita, tamkar ta kifa masa mari haka take ji.

"Wai har kin yi shirin kwanciya? Na zata zaku gaisa tukuna sai ki kwanta" Mugun kallon da ta yi masa ya sanya shi haÉ—iye maganar da ya yi niyyar yi.
"Ga wannan naki ne" Ya yi maganar yana ajiye mata ledojin hannunsa.
Ba ta kalli kayan ba, kuma ba ta motsa ba.
Chapter 55 · 0% Book details