← Book details Buzu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 78

Sashe 53

Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu irin gidaje ne manya-manya na alfarma da ƙasaita a cikin gurin.
A ƙofar wani gida direban ya tsaya, ya cewa Nana ta fito sun zo. Haka ta saukko ƙafafuwanta duk sun yi tsami saboda azabar gajiya.
Ya buɗe bayan motar ya ɗaukko ƙatuwar jakar Nana, ya rufe motar, ya yi gaba Nana ta bi shi a baya tana karanto addu'oin da suka sauwwaƙa.
Cikin wani matsakaicin gida suka shiga, gidan ya ƙawatu ya yi kyau sosai da sosai.
A falon gidan ya ajiye wa Nana kayanta ya ce "Ki zauna ki jira a nan"

Nana ta ce "Amma wa zan jira a nan É—in, ban ga alamar akwai mutane a gidan nan ba"

"Za ki gan su, ni a nan aka yi mini umarnin na kawo ki kawai"

Nana ta yi shiru tana nazari, shi kuma ya juya ya fice.
Nana ta din ga rarraba ido, tana son ta yi salla amma babu wanda za ta tambaya. Harabar gidan ta fita saboda ta ga famfo ta yi alwala, ta dawo falon ta yi salla.
Gajiya ta yi ta koma harabar gidan da kayanta, ta zauna tana rarraba ido.
Can ta ji ƙarar mota, aka buɗe ƙofar wani jami'in tsaro ya shigo ya buɗe gate ɗin, aka shigo da wata haɗaɗɗiyar mota aka yi parking ɗin ta.
Aka buɗe ƙofar motar, sai ga Asal ta fito sanye cikin doguwar riga, ta ɗaura mayafin a wuyanta, kanta babu ɗankwali. Har bakin ƙofar shiga suka rakata, ta wuce Nana ta shige ciki kamar ba ta gan ta ba. Nanan ma ta yi zamanta ba ta shiga ba, ta jingina da jikin kayanta taka addu'a saboda a gajiye take matuƙa, ga uwar yunwa tana ji ga tulin damuwa.
Sannu a hankali take tuna yadda ta shigo ƙasar Nijar ba ta san kowa ba, da yadda ta din ga raragefe har zuwa kan zamanta da Nene. Sai ta tsinci kanta da tattara su baki ɗaya tana yi musu addu'a, da fatan dacewa a Duniya da lahira.
Ba ta san iya adadin lokacin da ta É—auka a gurin ba, ta ji muryar Asal a kanta.
"Wai ke wace irin bagidajiya ce, a Nigeria daga wani ƙauyen ki ke ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalle ta.

"Na saka an kawo ki guri, ki shiga ki jira ni kin zauna a waje, na dawo ma kin nemi guri kin zauna ba za ki shigo ba?"

"Ta yaya zan shiga gurin da babu kowa na zauna, ni da ban san ma aikin da ki ka kawo ni na yi miki ba?"

Haushi ya kama Asal, ta ce "To idan kin ga dama ki shigo, idan kuma ba ki ga dama ba, ki yi ta zama a gurin" Ta shige ciki Nana ta bi ta da harara, kamar ba za ta tashi ba, sai kuma ta tashi ta ja kayanta, ta shiga falon ta nemi guri ta zauna a kan kujera. Asal ta saci kallon Nana, da yadda take gudanar da lamarinta cike da ƙarfin hali.

Nana ba ta kula ta ba, ita ma ba ta kula ta ba, Nana ta gaji da zama, ta saukko ƙasa ta miƙe ta kwanta.
Can Asal ta ce mata "Ga kitchen can, akwai abinci"
Daga haka ta tashi ta bar falon.
Nana ta tashi ta shiga kitchen É—in, ta tarar da Abinci, ta É—auka ta ci sannan ta É—an dawo hayyacinta.
A nan falon Nana ta kwana, da Asuba ta yi alwala a harabar gidan, ta koma falon ta yi salla.
Duk wannan abin zuciyarta a cike da zullumin aikin da za ta yi wa Asal.
Da gari ya yi haske, Asal ta fito Nana ta gaishe ta, amma ta yi kamar ba ta ji ba, ta fice ta bar gidan ta bar Nana.
Nana tana nan zaune, aka zo aka ƙwanƙwasa ƙofar falon, ta tashi a ɗan tsorace ta buɗe, wani mutum ya miƙo mata takeaway ya ce "Ga shi nan, aka ce a kawo miki" daga haka ya juya ya tafi.
Nana ba ta sake ganin Asal ba sai dare, ba ta saurari Nana ba still. Ta cika gidan ita da ƙawayenta, suka hau saman bene, suka kunna kaɗe-kaɗe har kusan ɗaya na dare su na abu ɗaya, suka hana Nana bacci.
Sai gefin Asuba suka daina wannan shirirtar, Nana ta din ga mamakin ita Asal zaman kanta take yi ne, ba ta da magabata ko kuwa?
Sai washegari sannan ta saukko ƙasa, a lokacin ƙawayen nata duk sun tafi.
Ta kalli Nana ta ce "Daga yau kar ki ƙara kwanar mini a falo, ga ɗaki can kusa da kitchen, a nan za ki din ga kwana. Na kawo ki ne duk da ba yanzu ne za ki yi aikin naki gaba ɗaya ba, amma za ki din ga yi mini girkin Abinci da ni da ƙawayena, da sauran aikace-aikacen gida.
Abu na farko dalilin da ya sanya na ɗaukko ki, ke ba ƙabilarmu ba ce ba, ba na son saka ido, ba na son surutu
Duk wani abu da za ki ga na yi, ko ina yi babu ruwanki, aikin duk da na saka ki shikaÉ—ai za ki yi mini"
Nana ta yi shiru tana tunani, dama duk wannan abin ba wani branch ɗin za a kai ta aiki ba, wannan zuƙaƙƙiyar za ta yi wa bauta, shi ne har da ci mata mutuncin cewa an yi amfani da kuɗi sai ta yi abin da ake so. Kuma me yasa ba ta zaɓi kowa ba sai ita?.
"Ba kya ji na ne?"

"Na ji"

"Ban gane kin ji ba? Haka zan din ga yi miki magana ki na amsa mini, ke ni fa ba Hasna ba ce ba, dole ki yi mini biyayya ki yi duk abin da nake so".

Nana ji ta yi tamkar ta yi tsaki, ta ce "Amma yanzu fisabilillahi duk faɗin ƙasar nan ki rasa wanda za ki ɗaukko ya yi miki aikatau sai ni. Ni harkar dafa abinci nake yi, amma kin kawo ni nan in din ga yi miki girki da boyi-boyi ba tare da an yi mini bayanin haka ba, ni gaskiya ba a kyauta mini ba"

"Da hakan ki ka dace ai, ko kina ganin kin cancanci wani abin bayan bauta? Idan ba za ki zauna ba ga hanya nan za ki iya tafiya" Ta yi maganar tana miƙewa tsaye.
Har ta yi gaba sai kuma ta tsaya ta ce "Duk wani abu da za ki buƙata akwai shi a kitchen, kina iya dubawa, wanda babu kuma ki sanar mini, shi ma idan ba ki ga dama ba kar ki yi aikin" ta yi gaba ta bar Nana da ta gama ƙulewa.

*****

Gaba ɗaya Shukura ta burkicewa Sagir, ba ɗaga masa hankali ta yi da rigima ba, tattara shi ta yi ta watsar gaja ɗaya take harkokinta, da gaske take ƙoƙarin gano abin da mahaifinta yake ɓoyewa tsawon wannan lokacin da har ya hana Hajiya Amina bincike a kan lafiyarta.
Ga shirin tariyar Yusra Sagir na yi, ga damuwar rashin sakin jiki da shi da Shukura ta yi, ta tattara shi ta watsar.
Ɓangarensa ya saka aka gyarawa Yusra, dama ba amfani yake yi da shi ba, aka ƙara gyara shi, aka haɗa gidan gaba ɗaya aka sake yi masa fenti. Daga gaya mata batun dawo da Yusra zuwa gyaran gidan da kawo kayanta, ba a yi sati guda ba, gida ya ɗau harama.
Duk yadda ya so ya lallaɓa Shukura, ta saukko ta din ga saurararsa ta yi burus da shi.

Nana ta shafe sati guda tana gidan Asal, tana yi mata hidima, ta hantare ta ta kyare ta, dandazon ƙawayen da take tarawa ma, su hana ta sukuni da aiki. Nana ta din ga iya ƙoƙarinta, gurin kai zuciyarta nesa, amma abin ya fara isarta.
Tana tsaka da nazarin yadda za ta ɓullowa lamarin, da safe Asal za ta fita ta kalli Nana ta ce "Ki shirya nan da sati ɗaya zamu bar nan, zamu je asalin inda na ɗauke ki ki yi mini aiki a gurin"

Nana ta ce "Ina kenan? Kuma aikin me?

"Idan mun je za ki gani" Ta ba wa Nana amsar a taƙaice.

*****
Jamila tana kwance tana chatting da Abba, bikinsa saura sati biyu.
Hajiya Sa'a tana ta zaginsa da yi masa bala'i, a kan yadda yarinyar take ta ƙorafin ba ya kula ta, waya ma sai dai ita ta kira shi, babu abin da ya yi masa zafi da ita.
Yanzun ma kamar ya yi wa Jamila kuka.
Ita take ta rarrashinsa tana nuna masa babu komai ya yi aurensa kawai.

"Ƙanwata ko na yi aure hankalina ba zai kwanta ba, kar ki manta da ɓarnar da ta faru tsakanina da ke, ya zan yi da shi"

Ta ce "Na san kai mutumin kirki ne yayana, hakan ne ya sanya ka ke jin damuwa a kan abin da ya faru, amma ka yi haƙuri ka yi aurenka kawai, ina roƙon Ubangiji Allah ya kawo mini wani mijin"

"A'a ki daina faɗa mini haka, zuciyata tana sosuwa, baki da wani miji sai ni in sha Allah" haka suka kasance tana ƙarfafa masa gwiwa, shi kuma yana rarrashinta.
Ta gama wayar ta ajiye, ta ga Suwaiba ta ƙuro mata ido tamkar ba ta taɓa ganinta ba.

"Meye ki ke kallona, lafiya?" Suwaiba ta yi shiru ba ta bata amsa ba, kuma ba ta yi magana ba.

Jamila ta ja tsaki, tana ƙoƙarin kwanciya, Suwaiba ta ce "Jamila"

"Na'am mene ne?"

"Ki ɗauki saƙonki mana"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wane saƙon?"

"Na cikin jakarki"

"Cikin jakata kuma? Mene ne a jakar tawa? Wato bincike ki ke yi mini a jakar ko?"

"A'a ni tuni kawai nake yi miki da saƙonki na cikin jakar"

Jamila ta tashi zaune ta ce "Wai wani saƙon? Miƙo mini jakar dai na gani"

Suwaiba ta ce "A'a ba zan taɓa miki jaka ba"
Chapter 53 · 0% Book details