Sashe 1
Buzu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BK 2
52
Jamila ta fashe da wani irin kuka tana tsuma, ta ce "Na shiga uku, yanzu Aljani ne ya kwanta da ni?"
"Eh amma a jikin bil'adama ya shiga, ya yi amfani da ke" ta gaya wa Jamila kai tsaye, ba tare da ta ji nauyin hakan ba.
"Na shiga ku, yanzu waye zai aure ni a haka? Ya zan yi. Na lalata rayuwata"
Hajiya Sa'a ta riƙo hannun Jamila ta ce "Na sha gaya miki, matsoraci ba ya zama gwani Jamila. Shi fa auren nan ba dole ba ne ba. Idan kina tare da ni duk abin da ki ke so za ki samu a tare da ni. Idan ma auren ki ke so miji sai kin zaɓa, kuma tsaf za a yi miki gyara babu wanda ya isa ya gane an taɓa amfani da ke. Kuma ƙungiya ta bayar da kuɗinki na shekara. Su na gurina zan din ga baki a hankali saboda kar a gane. Ki kwantar da hankalinki, ki ƙwarara jikinki, kar wani abu ya razana ki. Kuɗi kin same su kin gama ki saki jikinki ki mori duniya. Ke ce yarinya mafi ƙanƙanta a cikin ƙungiya. Ni dai ina matuƙar ƙaunar ki ne. 'yar uwakki na so na kawo, amma abu bai yiwu ba, ina tausayawa rayuwar da ku ke yi a gidanku ne. Ki cire duk wata damuwa daga zuciyarku, ki cire tsoro da tausayi baki ɗaya za ki je inda ba ki taɓa zato ba.
Jamila ta É—aga kai ta yi wa Hajiya Sa'a wani irin kallo, da ita kaÉ—ai ta san ma'anarsa. Ta share hawayenta ta ce "To shikenan"
Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta ce "Yauwwa Daughterna, tashi mu je na gasa ki, ki karya likitan ƙungiya zai shigo ya duba ki" Jamila ta ja jikinta da ƙyar, Hajiya Sa'a ta kama ta suka je banɗaki.
****
Yau kwana na huÉ—u kenan, Sayyid yana cikin wannan yanayin. Babban abin da yake damun Nana rashin cin abinci da kuma salla da ba ya yi, daga bacci sai zaman shiru. Ba ya cewa uffan, sai dai ya yi ta bin ta da kallo. Ta din ga Addu'a Allah ya taimake ta, ko Ummi ba ta zo gurin ta ba, balle ta san halin da suke ciki.
Ƙarfe tara na dare ta na zaune a ƙasa inda ta ajiye fulo tana kallonsa a kwance a kan katifar. Ta ɗaga hannayenta kamar za ta yi addu'a, ta karanta suratul mulk, da ayatul kursiyyu, da Suratul falaƙi da Nasi. Ta tofa a hannunta, ta ƙarasa kusa da shi a ɗan tsorace ta shafa masa a fuskar sa. Ta ja da baya tana jira ta ga abin da zai yi, amma ta ga bai yi komai ba. Ta nemi guri ta kwanta tana ta tunani a ranta.
A cikin bacci ta ji ana ture ta, ta buɗe ido da sauri, ta ga yana ƙoƙarin kwanciya a gefen ta, duk da yadda gurin ya matse su.
"Sayyid" ta kira sunansa.
"Na'am"
Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta riƙo hannunsa ta ce "Mene ne?"
"Na kasa bacci, kin bar ni nikaÉ—ai a kan katifa"
Cikin farin ciki da kulawa, ta shafa bayansa ta ce "Gani na yi ka na numfashi da ƙyar, kamar na matse ka shi yasa na saukko nan"
"Ma vie"
"Na'am Shugabana"
"Yunwa nake ji, kamar ban taɓa cin abinci ba"
"Bari na yi sauri na dafa maka wani abin, amma zo mu je ka wanke bakin ka, ka ga yanzu tsakiyar dare ne" Ya yinƙura ya tashi, ta kama shi, yana ta jiri, saboda yunwa ga rashin lafiya, ga kuma mutuwar jiki.
Ta kai shi banÉ—aki, ya wanke bakinsa, ta dawo da shi ya zauna.
Ta feraye doya a cikin ɗakin, ta ɗaukko gas ɗin ta, ta ajiye a bakin ƙofa ta ɗora.
Ta É—aukko mafici tana ta yi masa fifita.
"Rayuwata"
"Sayyid"
"Kamar yau ba mu ci abincin safe ba ko?"
Nana ta ce "Kwanan ka huɗi fa ka na bacci. Babu abin da zan ce wa Allah sai godiya, da ka farka" ya yi shiru bai kuma cewa komai ba. Ta sauke doyar ta dafa masa shayi, ta ajiye tana jira ya sha iska, ta ba shi da kanta. Amma bai jira ta ba, ya din ga hannu baka hannu ƙwarya. Sai dai hakan ya yi wa Nana daɗi, ganin ya ci Abinci da yawa yau.
Ya gama ci, ta dafa ruwa ta kama hannunsa zuwa banÉ—aki, tamkar jaririn goye ta yi masa wanka. Shi kansa a lokacin ya din ga jin wata lafiyayyiyar iska na shigar sa. Ta saka ya yi alwala, ya fito ya zauna ya fara jero sallolin da ake bin sa.
Ta ce "Sayyid kar ka ce sai yi a yanzu duka, sallolin da yawa.ka bari ka din ga ramawa a hankali.
Ya jinjina mata kawai kawai, tun yana yi a tsaye ya kasa tsaiwar ya koma yi a zaune. Ta yi shiru tana kallonsa, ta wasu guraren suna da kamanceceniyar halayya ita da shi.
Duk yanayin da yake ciki, muddin ba hankalinsa ne ya gushe gaba É—aya ba, ba ya wasa da salla ko kaÉ—an. Hakan ya sanya take jin ko a ainihin rayuwarsa haka ya siffantu da kiyaye salla a kan lokaci.
Har ƙarfe uku da rabi, dan kansa ya ce "Ba zan iya ƙarasawa ba, numfashina"
Ta ce "To ko za ka yi a kwance?"
Ya girgiza kai ya ce "Na fi so na yi a zaune, ko a tsaye"
Ta ɗage masa labule, ganin yadda yake ta gumi. Ta shimfiɗa masa sallaya a bakin ƙofa, ta jera masa fululluka, ya kwanta.ta zauna a gefen sa tana yi masa fifita. Ta ɗora hannunta a goshinsa tana karanta masa abin da Allah ya sa ta tuna a zuciyarta.
Hannunsa ta ji yana saka wa a rigar ta, duk da idonsa a lumshe yake. Murmushi ta yi ta ci gaba da abin da take yi. Jin yana yi mata cakulkuli, ya sanya ta kwanta a jikinsa tana dariya. Shi ma dariyar ya yi. Ya ce "Ki kwanta a kusa da ni" ya yi maganar yana nuna mata kusa da shi. Kafin ta yi magana ta ga an dalle su da fitila.
Cikin hanzari ya juya kansa, ya ɓoye fuskarsa a cinyar Nana, gashin sa ya kwanta a kan filon. Nana ta saka hannu ta kare fuskarta.
Muryar Barira ta ji ta ce "Yi haƙuri dan Allah, jin motsi ya yi wa na fara jin tsoro, shi ne na fito na duba, ku yi haƙuri.
Ta kashe fitilar ta koma ɗaki. "Sayyid ka yi haƙuri, na san ba ka ji daɗi ba, ka yi haƙuri"
Ya yi mata shiru, kuma bai É—ago daga kan cinyarta ba. Ta shafa gashin ta ce "Shugabana, ka yi magana mana, ko na ji daÉ—i, kwana huÉ—u ka na bacci, ba ka yi mini magana dan Allah kar laifin wani ya shafe ni"
Sai kuma ya juyo a hankali, ta ce "Yauwwa Rayuwata"
"Kin daina aman?" Ta ji ya tambaye ta babu tsammani.
"Eh na daina"
"Allah ya sa ki haihu wannan karon "
"Amin, kuma Allah ya baka lafiya na haɗa jariraina biyu, babba da ƙarami"
Ya yi murmushi ya ce "In sha Allah, kafin ki haihu, idan na ji sauƙi zan nemi aiki, na kula da ku da kaina"
"To Allah ya amince. Amma Sayyid ina kuÉ—in nan da na gani rannan, a cikin wardrobe É—in ka? Da na haÉ—a mana kaya ban gan su ba. Da sai mu É—auka a yi maka magani, kuma mu canza gida"
"Ai Habu ya karɓa, ranar da ya zo na ƙarshe, ya karɓi kuɗin Nigeria da yawa, ya bar mini wasu, ya ce na Nijar ne. Kuma da kin duba kayan nawa sosai, su na ciki"
"A'a ni ba na caje maka kaya, idan Allah ya kaimu gobe, sai a lissafa mu gani idan za su isa."
Ya ce "To. Kwanta ki yi bacci" ya yi maganar ya ƙara matsa mata. Ta kwanta tana murmushi.
"Sayyid, idan har ba a ga su Habu ba, ina ga da ni da kai zamu je Nijar, mu nemi danginka da kanmu"
Ya yi shiru bai yi magana ba, ta ɗan taɓa shi ta ji har ya yi bacci.
*****
Jamila a dole ta saki ranta, jikinta ta ɗan samu ƙwari, ya daina yi mata wannan mugun ciwon da yake yi mata. Raɗaɗin ma duk babu. Sai dai tana jin ƙasan zuciyarta kamar za ta yi bindiga, saboda damuwa da tashin hankali. Sosai abin da ya faru ya tsaye mata, ta shiga banɗaki ta sha kuka. Wai ita Aljani ya kwanta da ita, ta gaba da baya aka ci zarafin ta ta wannan mummunar hanyar.
Tana kwance a cikin bargo, Hajiya Sa'a ta fita shashashancinta. Wayarta ta fara ringing. Ta janyo ta ɗaga. Muryar Abba ta ji ya ce "Ƙanwata, wunin yau ban jiki ba, lafiya kuwa?" Wani irin abu mai zafi ya taso mata, ya haddasa mata karaya. Muryarta na rawa ta ce "Yaya Abba ba ni da lafiya"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Me ya same ki?"
Rasa abin da za ta ce masa ta yi, kawai ta saka kuka. Aikuwa ya rikice ya din ga rarrashin ta.
Da ƙyar ya lallaɓa ta ta ce masa cikinta ne yake ciwo.
"To ina Mummyn take? Ba ta kai ki Asibiti ba?"
"Ta kai ni, an ba ni magunguna ma, dan Allah kar ka yi mata zancen, ta yi mini iya ƙoƙarin ta,kar ka yi mata zancen dan Allah"
"No ai ba zan yi mata ba, ba ta san ma ina da lambar ki, mu na magana ba. Ki kwanta ki samu hutu kin ji Ƙanwatax
"To shikenan na gode sosai" suka yi sallama ta ajiye wayar, ta kwanta hawaye na ci gaba da bin idanunta.
*****
Yana zaune a cikin mota, yana ƙoƙarin kunnawa, wayarsa ta fara vibrating. Ya kalli screen ɗin wayar, ya ga baƙuwar lamba. Ya ɗauki wayar ya ɗaga ya saka a kunnensa.
"Hello" muryarta ta doki dodon kunnensa. ÆŠan waro ido ya yi, ya gyara zaman sa ya ce "Wa ke magana?"
A raunane ta ce "Beb abin har ya kai ka manta muryata ma? Shikenan na gode" ta kashe wayar.