← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 69

Sashe 68

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan anyi sallah azahar wajen karfe uku gidan su AFREEN ya cika makil da mutane tanti ta sakankance cewa maganin ta yaci tunda hayanzu papa bai shigo ya koreta ba sai fara'a take, ai bata ƙarasa tunanin ba papa a gaban rai a matuƙar bace yana mata wani irin kallon da sauri ta tashi ta rike hannunsa da nufi ta ja shi suyi ɗaki amma ina sai ya warce hannun sa da ƙarfi tare da cewa cikin ɗaga muyar cikin bainar jama'a da gidan "Sakina (Tanti) tashi ki tattara kayan ki ki bar man gida macuciya azzaluma an namimiya na sake ki saki ɗaya tattara ki bar man gida ban son na kara ganin ki na tsane ki na kara maki wani sakin kije na sake saki biyu."

Tanti da hankalin ta ya tashi ta rikice da sauri ta rufe masa baki dan kar ya ida cika mata na uku da niyyar ta bashi hakuri da sauri anty hawa ta riƙe tana faɗin "Sakashi Sakina kada basa hakuri wallahi kin manta abinda aka faɗa maki, ki tashi muje in ya wuce sai ki dawo kamin ya kai ga cika maki uku baki ɗaya."

Ai Tanti da hankalin ya gama tashi ko sauran yar uwar tata bata yi ba kawai ta shiga bama papa hakuri ya yafe mata kamin take gama basa hakuri kenan ya idasa furta mata saki na uku duk da hakuri da mutane ke bashi dan ba wanda yasan abinda ya masa dan kuwa ko shi ba zai iya faɗa maka ga abinda ta masa.

Yana ida yima saki na uku ai kuwa sai buga hannun da hannu tace shikenan ai dama dole ka sakeni tunda na maka asiri na kada kara haihuwa tunda nima tawa ta tsaya kuma duk auren AFREEN da ke sakawa rana ana fasawa nicenan keyin asiri na yauma nayi asiri kansa amma bai ciba gashi ni ya kama Arahamat ma ninayi asiri ta daina haihuwa tun kamin na maka da na ita umma zeinab tanayi sai na yima ka ɗan kowa ma ya rasa kai gaskiya na ji dadin wannan sakin amma kar damu zan komo gidan kuma bacin na nayi asiri kalla kaza nayi na kaza," haka dai tayi ta tunawa kanta asiri har sai da takai aya, mutanen da suka taru wajen suka cikin da mamaki abinda idan har ba da bakin ta gayi ba kuma gaban su to wallahi yanda take masu kirki zasu iya cewa karya ce saboda shiru shirun ta ashe lumbu lumbu ce macijin kaikai.

Masu mata ya shirya suna mata masu zagin ta na mata kowa da abinda yake faɗa, papa da shok ta kama shi da mamaki ya ja ta hannun har waje ya fida ta Hajiya Zakiya nace masa mita masa tun ita batasan mike faruwa saboda yanzu tajiyo hayaniyar ta fito , papa kuwa bai ma bi ko takan mahaifiyar tasa ba sedai ya ga ya fida ta daga gidan mutane nace masa kada aje ta haukace ne har take tonawa kanta asiri ka ya sake taje tayi wani gun,

Tajuyo ta kalli mutanen dake ke faɗar hakanan tace"Lafiya ta babu wata haukacewa da daniya kuma zan baku mamaki ta fara gayi sunan wanda ta sani a cikin su sannan ta kalli papa tace "toh kaje ka ɗako man hijabi ai kasan ba zan bi hanya haka ba."

Tace bani ɗaukowa kuma bazaki kara takamin gida ba nan aka bashi hakuri yasa aka miƙo mata hijab tayi gaba abinta ko kunya babu.

Dan ita Aunty hawa tana fara tonawa kanta asiri ta fice daga gidan.

Biki sai ya komai na yada magana da kuma jimami da yi mata Allah ya isa Hamida ɗiyar ta kuwa ta shige ɗaki uwar tanata kuka.

Taro dai ya tashi lafiya inda sai washegari za'a tafi da AFREEN gidan mijinta, ida da dadare Hajiya Zakiya ta tara albarka Alhaji Sadisu da matan da yaran tace sai an faɗa mata abinda ya sa ya yima tanti korar karya a bainar jama'a, saida ya nisa sannan "Wallahi Hajiya Ni bata min komai ba kawai ina waje sai na rin gajin na tsaneta bansan dalilin nayi ta kokarin kwantar da hankali na amma abin ya citura kamar ana hura man hutar kiyayar ta cikin zuciya hardai na kasa jurewa sai nazo na mata wulakanci sannan naji sallama kuma daga haka sai ta fara tu nawa kanta asiri abinda ta ringa yi nasan hakan yanada nasaba da abinda ta jayowa kanta.

Washegari misalin ƙarfe 11 iyaye sun gama yiwa AFREEN nasiha aka shirya don kaita gidan ta da kukan ta da komai dan tana tirjewa ita bazata ba da khair mahaifinta ya lalaɓa dan ganin lokaci na kurewa saboda jirgin ƙarfe sha biyu zasu ya kaisu Niamey ita da uwan raki yar ta da zasu tafi Mandela hada hawaye duk juriyar ta ba wanda tayi kuka cikin diyanta don an masa aure za'a kaisa gidan miji sai ga AFREEN ko dan ita ba'a gari guda zasu zauna ba oho.

Anty fauziya, Aunty Khairat, umma zeinab, Momy Jannah, Hasina, Fanna, zeinab Maryam, da anna mata baba Adamu sune ƴan rakiyar amarya gidan ta kuma su duka a jirgi guda zasu da amarya.

Ba'a dauki wani lokaci ba suka sauka cikin garin Niamey gidan tanti Mariam yaya alhaji Sadisu suka sauka dan sai gobe za'a kai amarya gidan mijinta saboda shima Ali sai gobe za'a kai masa tasa dan ita ma har sun sauka gidan dady wajen Momy su AFREED

Tunda mahaifin AFREED ya dawo Niamey yake neman sa bai gansa ba kuma da an kira wayoyin sa a kashe Ali kaɗai yasan inda yake kuma yace kada ya faɗa yana son ya huta ne

Washegari da misalin ƙarfe 9:00 AFREED ya shigo gidan bai zarce ko ina ba sai ɓangaren Momy yana shiga ya tardo ta ita su Fariya da Khadijah Farisa kaɗai aka kai gidan mijinta Fariya kuwa sai sai idan anty aicha zata koma sai su tafi tare da sauran dangin mahaifiyar ta, suna ganin ya shigo fuskar shi ba annuri suka tashi su kayi sama suka barshi tare da Momy yan kai kusa da ita ya zauna saman kafet ya gaida ta ta amsa cikin sakin fuska sannan tace "Ango ka wani je ka ɓuya har amaryar ka sun sauka kai baka ma sani ba."

Ɗaya kai yayi ya kalle ta sannan yace "Momy kenan da sanin ki aka min auren doli ko ki sanar dani ace sai bayan ɗaura man aure zan sani."

Mahaifinsa dake sauka daga saman étage yace "Mahaifiyar ka batada laifin komai koma miye nine ke da laifin tun ninace kada a sanar da kai in ma laifi aka maka to ni nayi shi tunda gani kake an maka laifi. Har ya sauko ya kawo inda suke zaune ya zauna kusa da Momy, AFREED ya ɗago ya gaida shi ya amsa ba yabo ba fallasa.

Kusan kamar minti biyu babu wanda yace wani abu, sai dady yayi gyaran murya ya ce "AFREED Ni ba yi ma aure dan bani sonka ko kuwa auren doli ko saboda wata manufa ko dan na bata maka rai ba a'a asalima gata na maka amma ba zaka gane haka ba sai nan gaba, dan kanka zaka gane ko wace irin mata na aura maka kuma babu yanda banyi da kai ba kan ka fitar da wata amma fir kaki dan haka na maka zaɓi idan kuma ka nagani laifi aka maka toh rubuta takardar sakin yarinyar mutane ka bani tunda kai ban isa da kai ba, ita da iyayen ta suka isa da ita ai gashi bata sanka ba ta taɓa ganin kaba amma ta baro iyayen ta da garin su da gidan su dan yiwa iyayen ta biyayya, kai kuma naga za'a samu akasin haka."

Da sauri AFREED ya ɗago yace "Haba dady wallahi ba haka bane ko huta kace na faɗa zan faɗa ka sani ban taɓa bijire ma umarnin ka ba kawai dai nace yaka mata in sani kamin a ɗaura auren dady amma banci haka bance komai ba, Allah dai ya bamu zaman lafiya Allah sa ita ɗin alkairi ce.

Murmushi Momy da dady su kayi sannan a tare suka ce Allah maka albarka.

Dady yace "Tunda hakane inaso kaje ka gaida iyayen ta zan tura maka address ɗin gidan da suka sauka kamin dare ka tara abokanan ka aje dauko amarya, ai kasan gidan nan da na baku cen za'a kaita déjà iyayen ta sun gama saka komai a ciki an gama gyara gidan ."

Sannan yace inchallah dady kamin yake tashi ya bar masu gidan baki ɗaya a ransa yake cewa ai inda wallahi tayi mata yawa ita da kanta zata nemi na sawake mata ba dai ta yarda aka aura mata ni ba zata gani (nikuma nace kkai zaka gani ba🤣🤣🤣🤣🤣🤣 )

Ali ya nema ya rakesa suka je gaida su Momy Jannah inda Momy Jannah ta tsare shi da masifa tace "Kaga badan ba'a son yarinyar nan aka aura maka ita ba asali ba duk gidansu ita aka fiji dan haka wallahi ba minister kake ba ko shugaban ƙasa kake ka kuskura kayiwa yarinyar na wani abu mara dadi wallahi da kaina zan zo na sameka na rama mata ba wasu nake kuma wallahi ɗan jinjirin aiki bane."

AFREED ya ɗago ya kalle ta dam dam gaban sa ya faɗi ganin muguwar kama da matar take da AFREEN ɗin, a take zuciyar sa ta fara raya masa cewa kodai AFREEN ce matar da aka aura masa ɗin, amma ina inda itace ai da ba haka ba kawai ta fara maya kizo ne da duk abinda ya gani sai yaga kamar ita.

Hardai Momy Jannah ta gama masifar ta suka tashi sukayi tafiyar su Ali dai na ta masa dariya a hanya yana cewa ashe dangin fitina aka aura maka.
Chapter 68 · 0% Book details