← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 69

Sashe 18

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Seda ya d'an sosa kai sannan yace "A'a baba."

Murmushi Abbu ya saki ciki zuciyar shi yace "Yaran zamani" a zahiri kuma sai yace "To karka damu kai dai kaje ka nemi soyayar ta in ta amince shikenan sabida ni najima ina shirya ma auren yarinyar nan da k'anwata."

Sun d'an jima suna tataunawa kamin daga bisani yayi wa Abbu sallama ya fita.

Yana fita Abbu ya k'wala mata kira a firgice ta farka sabida har bacci ya fara d'ibarta kawai sab'o hijab tayi ta fito taje gun Abbu ta durk'usa yace "Tashi je kiyi masa sallama tafiya zaiyi."

Da sauri ta d'ago ta kalli mahaifin nata tace "wa?" don ita har ga Allah ta manta da wani yazo gidan.

Abbu yace "Wa kuma? Sadisu mutuman daya taimaka miki ranar nan yana can waje yana jira."

"Oh wallahi Abbu har na manta da yazo gidan nan ni harma na fara bacci, kenan sad.... Bata k'arasa fad'in sunan ba sanadi nuhi fad'i da taji ya mata a baki sanan tace "Kenan Hakane sunan shi bari naje muyi sallama" haka ta fad'a tare da fita daga gidan.

Abbu yayi murmushi tare tashi ya shiga d'aki.

Tana fita ta tardo shi baki k'ofar gidan yana jiranta tace "Har zaka tafi?"

"Hum wai har zaka tafi?" yayin yanda tayi sannan yace "Bayan nakusa kwana a gidan ku sabida ke."

"Kwana a gidan mu kuma ka rufa man asiri nidai."

"To baki son na kwana a gidan kune? ni ina cewa yanzu mun zama 'yan uwa zan bar kwana a cikin makaranta na dawo da kayana gidan ku a sama min gun bacci? amma shine zakimin rowa."

Waro ido tayi da sauri tare da cewa " Yo zaka iya?"

"Yo mi zai hana?"

"To shikenan zan gayawa Abbu sannan."

Dariya yayi sannan yace "Kewa wasa nake maki."

Murmushi tayi tare da sun ne kai gyara tsayiwa yayi sannan ya kira sunan ta "Arahamat."

Amsawa tayi da "Na'am."

Yace "Ki nutsu ki bani hankalin ki nan zamuyi wata magana."

A sanyaye tace "To ina jinka."

Seda ya k'ara gyara tsayiwa sannan yace "Zaki aure ni?"

Kamar saukar aradu taji maganar da sauri ta d'ago ta dubeshi tare da yin sauri maida kanta k'asa wai itace yau wani ke furtama wanan kalmar da ba wanda ya tab'a mata ita shin mafarki take ko a farke take? da alama ba bacci take ba da gaske ne."

"Yanaji kinyi shiru ko baki ji mi nace ba ko baki fahimci mi nake nufi ba? In hakane bari na miki yanda zaki gane, Arahamat inason ki ina kaunarki fiye da yanda kike tunani sonki ya ratsa ko ina na jikina, shin zaki aureni?"

Da sauri tasaka hannu ta rufe mashi baki a lokaci guda kuma ruga da gudu cikin gida sabida jin kalaman sa take kamar ana mata ihu cikin kunne. Amma ba karamin farin ciki tayi dajinsu ba.

Yau sati biyu kenan da Sadisu ya baya nawa Arahamat abinda ke cin zuciyarsa kuma ta amince shakuwa da soyaya mai k'arfi ta shiga tsakanisu Sadisu kuwa har ya shedawa mahaifiyar sa kuwa tayi na'am da zancan yawaci ma idan yaje zance yana kiran Hajia Zakiya ya bata su gaisa da Arahamat wada tun tanaji kunya har yakai ta saki jiki suna fira sosai dan hajia Zakiya tace ita ba surukar ta bace kamar 'ya haka ta ke gunta, kuma hajiya zakiya ta shedawa yaronta ta cewa nan da sati biyu za'a zo kawo komi da komi na aure harda lefe, shima kuma har ya shedawa iyayen Arahamat.

B'angaren Ufadi kuwa ta rage tsangwamar da take yiwa Arahamat sanadin aure da zatayi taje ta bar mata gida.

Yau ta kama lahadi kuma yau ne ranar da za'a kai lefe shalele kuma auta a gun hajiya zakiya tunji jiya alhaji suley da wasu abukan sa biyu sukazo da komi da komi da za'a bukata. Haka yau ma suka d'auki niki niki kayan lefan sukai gidan su Arahamat ida a ka kashe kud'ad'e sosai sabida auren buzuwa fah sai mutum ya shiyar dole sai kasaka g'wala g'walai kuma ka siye rak'uma anyi bajin ta masha kuma ankashi kud'i akasa aure nan da wata guda.

Kawanci tashi ba yuya a wajan ubangiji yau ya kama saura sati biyu auren Arahamat da Sadisu, yau ne kuma tanti Fatima k'anwar mahaifiyar su tazo gidan gani tayasa Arahamat cikin farin ciki da anashuwa amma da taga ba da k'anwar a ka zoba sai murna ta koma ciki tace "Tanti où est ma petie soeur (where is my lil Sister)."

D'an murmushi Tanti tayi tace " kwantar da hankalin sai saura kwana uku zata zo sabida école (school) sai a sannan ne ta saki ranta nanfa tanti Fatima tashiga gyaran amarya.

Yau ya kama saura sati d'aya d'aurin aure Arahamat na zaune tsakar gida tana alwala taji anyi sallama da sauri kuma a firgice ta mik'e don jin murya da ko ta mutu bata zata iya mantawa da ita ba tsurawa k'ofar shigo wa gidan tayi tana adu'a Allah sa abinda take tunani ya zama gaskiya aiko wanda yayi sallama na shigo wa ta saki wata irin razananiya k'ara mai sauti sai wani tippppppp kake ji ta fad'i k'asa somamiya..........

To masu karatu mai ya tsoratar da Arahamat da yasa ta fasa ihu, sallamar wa taji ta firgice, wane abu ta gani har yasa ta suma?

Ku biyoni a next page don samin amsar wa'inan tambayoyin???? Amma sai kuyi comments kuma next page sosai zata k'ayatar daku. In bakuyi comments ba ba zanyi next page d'in ba.

Ina jiran comments d'inku💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

ECRITE: 📝📝📝

_PAR_

*QUEEN ZEEFAT*

Yar
Mutan
Niger

Wattpad@nazhabibou

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
Hh
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_

~Masoyan wannan novel nasan kuna hakuri sosai akan d'aukar lokaci da nake banyi typing ba, to ina mai baku k'ara baku hakuri wallahi karatu ne yaman yawa, nima ba da son raina hakan ke faruwa love you more my FANS....😍😍😍😍~

Page : 13 & 14

Lafiya lau suka sauka cikin garin Niamey direct gidan hajiya Zakiya aka nufa dasu suna zuwa ta k'arb'esu hannu bibiyu da fara'a a fuskar ta ta masu tarba ta mutunci a falon ta suka sauka aka kai masu kayan su a cikin d'aki da zasu zauna, amma kayan Arahamat a d'akin hajiya Zakiya aka kai mata su cikin k'ank'anan lokaci aka cika gaban su da kayan ciye ciye da lashe lashe, tanti Fatima da Ufadi sunci sun sha amma banda Arahamat dake rakub'e yuri guda ta k'asa koda d'aga kanta har saida Hajiya Zakiya ta fito daga d'aki kamin tajata suka nufi d'akin ta sannan lalab'ata ta ci abincin tana gamawa tasa tayi wanka da sallah sannan hajiya Zakiya tasaka ta d'ane gado ta kwanta bata dad'e da kwanta wa ba bacci ya kwashe ta.

Sukuwa su Tanti Fatima na d'akin da aka tana domin su suma sunyi wanka tare dayin sallah suka kwanta don hutawa.

Arahamat ba itace tashi ba sai da ana kiran sallah magariba sannan hajiya Zakiya ta shigo d'akin ta tayar da ita.

Koma yin wanka tayi sannan ta d'auro alwala magariba tazo tayi sallah, tana gama hajiya Zakiya ta shigo mata da abinci ta d'an ci kad'an sannan aka shirya don kaita gidan ta dake cikin gidan hajiya Zakiya.

Ana gama shirya ta su Tanti suka nufi d'akin hajiya Zakiya suka tardo ta zaune bakin gado tasha ado tayi kyau sosai kamar balarabiya suma zaunawa suka, suka soma mata nasiha mai ratsa jiki tanata kuka, haka hajiya Zakiya ta shigo ta iskosu tace "Dan Allah ku barta haka zaku saka kwalliyar da aka mata ta goge daga ganin d'iyata ba mai kwaramniya bace nasan zata zauna lafiya da mijinta insha Allah, gashi tun kamin kuzo nan nasan kunyi mata nasihar kuma ta d'auka, gaskiya ku barta haka kuma insha Allah Arahamat ba zata maraici a gidan nan ba da yarda Allah, ni d'iyace kuka kawo min ba suruka ba don haka ku kwantar da hankalin ku, kuma ke Arahamat ki d'auke ni a matsayin mahaifiyar ki inason duk abinda Sadisu ya maki na k'untatawa ki fad'a min kiga hukuncin da zan yanke a kansa wallahi ko da kuwa kece mai laifin idan har ya nemi takura ki zo ki sameni ki sanar dani zaki sha mamaki insha taron dangi zamu masa" Hajiya Zakiya ta fad'i haka tana dariya.

Tanti tayi saurin cewa a'a zaluntar yaron albarkar nan zakuyi kenan to wallahi baku isaba zan kirasa na fad'a masa daga Arahamat tayi masa laifi ya hukunta ta sannan ya kirani ya sanar dani don wallahi mota zan tako daga Arlit har Niamey nazo nayi maganin ta sabida bani goyon rashin kunya da zata masa, sannan kuma ace shine mai laifi ko alama ki dai ji abinda na fad'a kuma kinfi kowa sanin zan iya aikata wa da haka kada ma ku taru kumasa taron dangi nima shigar masa zanyi ehe ga kuma Ufadi nasan itama tana bayana ah to."

"Ah wallahi ina bayan ki ai tare zamu biyu mota muzo hukunta ta ai tafi kowa sanin halina sedai ta ba wani labari ehe" haka Ufadi ta fad'a tana dariya.

Hajiya Zakiya ta yi dariya sosai, sannan tace "Kam ashe dai da kunga irin namu taron dangi sabida ko banza muda kenan mun fiku yawa, kuma kamin kuzo mu mun riga da mun gama namu hukuncin, sannan zanga wanda ya isa ya shigo gidan mu yace zai hukunta min yarinya wallahi da zaku sha mamakina."
Chapter 18 · 0% Book details