Sashe 24
Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su AFREED na ƙarasa primaire (primary) Alhaji Sumana ya mayar da su France a can sukayi secandary school da University sannan suka dawo Niger dan su riga da sun kammala karatun su nacan, watan su biyu a gida AFREED yace zai koma yaci gaba da karatunsa a USA shikuwa Ali yace makarantar horon sojoji zai wuce.
Haka kuwa akayi don iyayensu sun yi na'am da ƙudirinsu cikin ƙanƙanan lokaci aka shirya yawa kowa tafiyar sa ba dan sun so ba haka suka rabu da juna cikin kewa.
Lokacin da Ali ya kammala makarantar sa ta horon sojojin shikuwa AFREED yana sauran shekara ɗaya ya ƙarasa karatun sa, sabida degree da diploma da kega Ali yana samun aiki ya fito babba mai babban matsayi wanda aikinsa shine tsaron lafiyar shugaban ƙasa ko ministoci, AFREED kuwa yana kammala karatun sa ya dawo gida satin shi guda da dawowa daga USA aka ɗoke shi aiki cikin ministère kuma babban office yake occupé, amma cikin ƙanƙanan lokaci ya sami ƙarin girma idan aka ɗoke sa matsayin *MINISTRE DE DÉFENSE ET DE SÉCURITÉ* sabida gaskiyar sa da riƙon amana kuma ta dalilin sake zaben shugaban ƙasa da akayi wanda shine da zai zaɓi ministoci ya zaɓa hada AFREED, a lokacin nan ne AFREED ya nemi Ali ya dawo gunsa da a matsayin mai tsaron lafiyar sa kuma na kusa dashi domin shawara kan abinda ya shige masa duhu haka kuwa akayi ba wani bata lokaci aka dawo da Ali gun ɗan uwansa sukaci gaba da aiki guri guda cikin farin ciki da anashwa.
*CIGABAN LABARIN*
Yau ya kama week-end ne, misalin ƙarfe 11:20 AFREED ne kwance saman makeken gadon sa me kyau da laushi yana ta kwasar bacci cikin natsuwa kana ganin yanda yake baccin kasan ya najin daɗin sa, kirrrrrrrrrrr wayar sa ta fara tsuwa tana neman agaji amma har kiran ya tsike AFREED ko motsa wa baiyi ba sabida yayi nisa cikin bacci sa mai daɗin mai tatare da mafarkai irin masu daɗin nan da kwantar da zuciya ana cikin haka wayar ta sake ɗaukar tsuwa a karo na biyu sannan ya farka tare da sakin tsaki cikin bacci ba tare da ya buɗe idanunsa ba yasa hannu ya lalabo wayar ya ɗauki kiran ya kara a kune ba tareda duba sunan me kiran nan sa ba ya kara a kunne.
Daga can cikin wayar aka yi sallama firgigit AFREED ya buɗe ido tare da tashi zaune da sauri ya ƙara gyara zama yana murtsike ido sannan ya amsa sallama tare da cewa..............................
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Écrit
Par
*QUEEN ZEEFAT*
_Ƴar
Mutun
Niger_
Wattap:@nazhabibou
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_
PAGE: 21 & 22
Daga can cikin wayar akayi sallama firgigit AFREED ya buɗe ido ya tashi zaune da sauri jin Muryar da tayi sallama ya ƙara gyara zama tare murtsike ido, cikin natsuwa ya amsa sallamar tare dacewa "Tanti ina kwana antashi lafiya?"
Daga cikin wayar wada aka kira da tantin tace "Riƙe gaisuwar AFREED banida bukata wallahi gaisuwar daba za'a kirani Amin ita ba sai in nakira, can kaje ka gaida uwarka ita da kake so tunda ni ba kaunata kake ba, wai AFREED yanzu ace kafi ƙarfin ka kirani kaji yanda nake sedai ni a matsayi na na ƙanwar uwar mahaifin ka dan Allah ya azamin ƙaunar na kira na ji idan kana lafiya amma ba wani abu, shi mahaifin naka da ya san mahimmanci na ai kullum sai ya kira kuma duk idan ya dawo daga ƙasashen waje sai ya biyo tanan ya ganni, amma dayake kai bakasan kima taba ai ko kirana bakayi bare nayi tunanin zaka zo idan nake wallahi AFREED kaji tsoron Allah rishin son zumuncinka yayi yawa, zan kira uwar taka naji idan ita ke hana ka zuwa idan nake."
Wata gajerar ajiyar zuciya AFREED ya sauke sabida ba kanɗan ba maganar da tantin tayi masa me tsayi taso saka masa ciwon kai sabida rishin son hayaniyar sa, lumshe idon sa yayi sannan ya koma buɗe su kamin yace "Dan Allah Tanti kiyi hakuri wallahi yanda kike tunani ba haka bane sosai nakeso nazo na ganki kodan na samu nayi profiter na huta zaman Niamey din nan ya dan minyawa inason inje ida zan samu na shan iska yanda nake ba tare da wani ya takuraman ba, saida ya koma sauke wata ajiyar zuciya mai karfi kamin yaci gaba da cewa wallahi Tanti duk aiki ne ke rikeni badan ba naso zuwa b......."
Bai ƙarasa faɗar abinda yakeson faɗa ba ta katse shi da cewa "Yimin shiru AFREED dama ai nasan haka zakace kai kullum aiki aiki kamar injin, to ko injin na hutawa bare kai ɗan adam, ace aiki ya hanaka zuwa ida nake to ai ba zai hanaka kirana ba ko, ko har kiran aikin bai bari?"
Shiru yayi har kusan minti 2 sabida ba karamin gajiya yayi ba da wannan ƴar maganar da yayi ba ya buɗe baki zai koma yin magana, ta katse sa ta hanyar cewa "To kaga kai matsalar ka fah, ya za'a ce mutum da bakinsa amma magana na masa wahala yi yanzu zaka iya ce man bakin ka yayi ciwo daga yi wannan ƴar maganar da ko ta second 30 batayi ba, kai ba zuwan naka ba rashin maganar kane matsalar ba'a iya zauna wa dakai ayi hira haba AFREED dan Allah ka canza hali man, rishin son maganar ka yayi yawa, anyi mutum dai kamar gumki ba umm ba ummmmm ya kamata ka canza, naso naga yanda matar ka zata zauna dakai da rishin maganar nan taka ban sani ba ko ita ma irin ka zaka ɗauko, yawa m....."
Bata ƙarasa faɗar abinda tayi niyar faɗa ba yayi sauri katse ta da cewa "Insha Allahu Tanti ranar talata zan ɗauki hutu Alhamis zan shigo maraɗi da yarda Allah idan nazo kuwa sai na ƙarshe hutu na gun ki ko na dawo."
Ya hana Tanti ƙarasa maganar tane sabida yasan ta kaiwa ƙarshen zancen ta zatayi masa maganar aure ne shikuwa babu abinda ya tsana yanzu kamar amasa maganar aure dalilin kuwa shine baisan mi zaice mata ba sabida ba matar auren garesa ba kuma bai ma san ya za'ayi ya sameta ba yana tsoron kada lokacin da dady ya ɗibar masa yaje ya ƙare bai fito da matar da zai aura ba, shi kuwa dady yayi masa auren dole da baisan da wa zai haɗa saba. Shiyasa baison zancen kwata kwata.
Cikin wani irin farin ciki Tanti tace "Dagaske kake ɗan albarka? kai amma naji daɗi cewa zakayi in shiryar zuwa babban ɗana mafi soyiwa a gareni nasan idan kazo nan zakayi wata biyu ko uku ko?"
Wani gajeren murmushi ya saki sannan yace kai Tanti idan nayi wata biyu ko uku aikin nawa fah? Idai ba so nake a cireni daga aikin ba, sati biyu ne kawai za'a ban?
Murna ta koma ciki a faɗa ce tanti tace sati biyu ai wallahi baka isaba duk wanda ma zai maka signe hutu sati biyu kace masa nace bai isa ba duk ubanda ma ya ɗaure maku gidi idan kazo garin nan sai kayi wata wallahi kama shirya nida nakeso ka dawo Maraɗi da aiki, haba AFREED dan ni baka ɗauke ni uwa ba shine za kazo ka yi sati biyu ka koma, yaushe rabon ka da garin nan yanzu kusan shekara goma kuma sunan ace kanada uwa a garin nan kiran ma a gaidani ban samu ba shine kuma yanzu kace zaka zo amma wai sati biyu kawai zakayi ko dan kaga inason zuwan ka guna ne? To har indai sati biyu ne zakazo kamin kayi zaman ka kawai," aiko sai ta fashe da kuka sannan taci gaba "Kana son yaro amma shi yana nuna maka ƙiyayya ƙikiri."
Da sauri AFREED ya ce "Dan Allah Tanti kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki wallahi zanyi wata gurinki insha Allahu ina zowa sai nayi wata ko na dawo in badan aiki ba ai da ma gurin ki zan koma da zama baki ɗaya, haba Tanti Ni na'isa nace ban kaunar uwata adai min hakuri ai na kusan zuwa duk laifin da nayi zan karkare insha Allahu ma tanti chérie je t'aime beaucoup mon adorable mère (I love you so much uwata mai kauna)
Aiko sai ga Tanti da washe baki tana dariya sosai a sauti dariya zaka gane taji daɗi shikenan kuka ya koma ciki daman bana gaskiya bane kukan "Toh toh toh dan albarka na ba damuwa inajiran ka sosai naso ace yau ne zakazo amma ba komi yau da ranar Alhamis duk ɗaya ne wajen Ubangiji Allah kaman kai lafiya ɗan kirki kazo man tare da wannan ɗan uwan naka mai surutun tsiya shima najima ban ganshi duk da shi ya fika zumunci yana kirana mu gaisa, kuma zan samu abokin hira tunda kaidai ba magana kake ba kaji ko ka gaishe man mahaifiyarka da ƴan biyu da dady naku ko da yake shi baya gari amma yace man yau zai shigo."
Murmushi AFREED yayi sannan yace "Insha Allahu Tanti zasuji a gaida min kowa da kowa a huta lafiya."
"Ameen ameen ɗan kirki sai anjima." sannan ta kashe wayar
Murmushi AFREED ya koma yi tare dayin mika yana karanto addu'ar tashi daga bacci wada bayi ba a lokacin da ya farka da kiran ne silar tashin nashi sannan yace "Kai Tanti yanzu zata birkice tayi ta faɗa kuma a take zata sauko Allah dai kara lafiya da shekaru masu albarka Tanti na, oh ni yanzu ya zamemin dole nayi wata guda a maraɗi idai banaso ɓaci ranta, bai komi zan gyara komai gun aiki, Ni zai fi min ma naje nasha iska ba kamar nan ba da kullum akwai masu tsaronka kamar kayi wani babban laifi." mtssss yaja wani ɗan ƙaramin tsaki kamin yake sauka daga saman gadon ya nufi douche (toillet).