← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 69

Sashe 13

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba tare da ta d'ago ba tace "To katsaya a nan dan Allah naje na kai kud'in adashan dama sune aka aike ni kaiwa tsausayi ya samesu idan matar ta bani cikon sai na kawo ma wallahi idan naje da cikon kud'in nan gida matsala za'a samu tunda kaga ga gidan da zan shiga can ba jimawa zanyi ba ina kai mata zan fito." ta fad'i haka tana nuna masa wani gidan.

Kollon gidan yayi sannan ya dubeta yace to jeki ina nan ina jiranki."

D'ago kanta tayi da niyar masa magana ta kasa sakamakon haduwa da idanun su su kayi sanadin jin wata irin bugawa da zuciyar ta tayi kawai sai tayi saurin juyawa ta fasa maganar ta nufi hanyar gidan.

A k'ala zata kai kusan minti goma da shiga gidan sannan ta fito, kanta na duk'e ta na kallon k'asa ta nufo idan yake tsaye yana jiranta.

Sallama tayi masa ya amsa sannan tace cikin sanyi jiki "Dan Allah kayi hakuri na b'ata ma lokaci daga taimako na, wallahi matar ta tsayar dani itama bata da canjin kuma har yaro ta aika ya nemo bai samu ba, shine tace na bar mata kud'in idan ta samu canji zata kaimin har gida, to shine na fito na tambaye idan har ka yarda sai ka gayamin ida zan sameka in ta maido da cikon sai na kai ma."

Murmushi yayi sannan yace wai miye kike ta wani sunne kai baki son kallo na tunda d'azu duk kin wani canza duk naga jikin ki yayi sanyi, kuma ni na ce maki na barmi ki sauran kud'in kawai ki rike idan ta dawo da cikon."

Waro idon tayi waje tana kallon wani gefe tace "So nawa zan gayama ka cewa da akwai matsala idan a gida a ka gani da kud'in nan dan Allah ka rufan asiri ka gayamin inda zan ganka? Don na mayar maka da kud'in ka, yanzu ma sedai nace ma mai a dashan idan ta sami canji kada ta kai min gida zan zo na karb'a wallahi."

Sak'e yayi yana kallon ta ita kuna ko da wasa bazata k'ara yarda ta sake had'a idon da shi ba.

Wani tunani yayi sannan ya saki murmushi yace "To gashi nikuwa bason na saka ki a matsala amma kinsan mi za'ayi? Gigiza masa kai tayi alamar a'a, sannan ya ci gaba "Yanzu muje ki nuna man gidan ku idan kin karb'o canjin sai naje da kaina har gidan ku na karb'a."

Ba tare da ta d'ago ba tace "Taya zaka gane cewa na karb'o."

"Bata yada zayi na gane kin karb'o gaskiya, amma ba gobe sai na dawo nazo na karb'a ba, sabida nasan bazaki fuce gobe da yamma ba baki karb'o kudin ba nikuwa sai nazo da dadare na karb'a."

Ba tare da tayi wani tunani ba tace "To muje na nuna maka."

Tafiya suke ba me cewa dan uwasa wani abu kowa da tunanin da yake suna shiga wata wahalaliyar anguwa wada kana ganin ta kasan ta irin wanan talakawa nan talak ne.

Ja tayi tatsaya dan nesa da wani gida batare da ta kalle shi ba tace "Kaga wacan gidan to shine gidan mu idan kazo nan zaka shiga ka tambaye dani sai na fito na baka kud'in ka."

Sak'e wayi ya kollon gidan da ta nuna masa ya kuma juyo ya sake kallon ta yakai a kala sau biyar yana hakan, "Ko kad'an yarinya nan batayi kama da wada ke rayuwa cikin gidan nan ba duk da kayan jikin ta ka'dai ya isa ka gane cewa d'iyar talakawa ce amma bai tab'a tunanin har ya kai haka ba, ya fad'i haka a zuciyar sa sakamakon ganin ginin gidan da yayi na jar kasa duk yabi ya rarake sabida idan a kusan gidan kake ma zaka iya hagon mutanan gidan sabida k'ank'antar katangar take ya kara jin tausayin ta ya mamaye shi burin zuciyar sa ya k'ara k'arfi, a cikin zuciyar sa ya ce "Allah ka cika min burina."

Katse maya tunanin tayi tare da mika masa rigar sanyin sa tace "Ungo rigar ka nagode ni zan wuce gida.

Juyowa yayi ya kalle ta itama shi take kallo da sauri ta k'auda idonta, murmushi yayi sannan yace "Ki rike na bar maki."

Saida ta sauke numfashi sannan tace "So nawa zan gayama ka cewa idan nashiga gida da wani abu wanda ba a sanni da shi ba zan shiga matsala amma ka k'i yarda." haka ta fad'a tare da sake mika masa rigar.

Yana karb'a riga kamin yace wani abu ta bar gun ta nufi hanyar gidan su, bin bayanta yayi da kallo har ta shige cikin gidan, a sanan ne ya tuno da ko sunnan ta bai tambaya ba, murmushi yayi sannan yace "Bai komi idan na dawo zan san sunan." daga nan ya bar gun ya kama gaban shi.

Ita kuwa tana shiga gidan wata 'yar dattijuwa ta yo kanta da masifa tace "Oh ni duniya ina zaki damu yarinyar nan tun yaushe na aike ki, amma dan gantali sai yanzu kika dawo kina can kina yawon iskancin ki da kika saba to yau uban mi ya tsayar dake kuma? Yo tambaya mima zan maki nida na riga da nasan hali? maza ki wuce daga gaban tun kamin na b'ab'alaki wallahi, nidai wallahi an barmin fitina miyasa uwarku da zata mutu baku mutu tare kika je can ki bita ni kawai sai a barmin jaraba ni da ban haihu ba amma wata ta haifa tabar min bala'i."

Jikin yarinya na rawa ta gusa da ga gun matar tana sauke ajiyar zuciya ko kukan ma kasawa tayi sabida sabo da tariga tayi da halinta taje ta d'auki tsintsiya ta fara share tsakar gida.

Da marece wajan karfe biyar sai ga matar da taje kaiwa kud'in adashe ta shigo gidan da sallama, matar gidan na zaune saman tabarma tana sauraran radio ita kuma yarinya na cikin wata rub'ab'a cuisine (kitchen) ta na dafa masu abincin dare, wanda tunda taji sallamar matar gabanta ya yanke ya fad'i da k'arfi har saida ta saka hannu ta dafe gaban ta.

Mai adashan ta shigo ta zauna kussa da matar gidan tana washe baki, "Ah yar uwa kece tafe da marecan nan bari na koyo maki ruwa." matar gidan ta fad'a tare da k'ok'arin mikewa.

"A'a yi zamanki banida k'ishirwa."

Komawa tayi ta zauna tana me cewa "To kodai wacan 'yar iskar bata kai maki kud'in ba ne."

A'a ki kwantar da hankalin ba shine ya kawo ni ba wata magana ce na zo muyi."

"Ah to shikenan ina jinki." matar ta fad'a tana mai sake gyara zama.

Mai adashan ta saka hannu a cikin jakar ta tafido da kud'i ta mika ta sannan tace "Ga cikon kud'in da dazu yarinyar ta kai min 5000 to banda canji sai nace tayi tafiyar idan nayi canza sa nazo nakawo maki, amma sai cemin tayi a'a kadana kawo maki na bari taje ta k'arba , to ni kuwa sai nayi tunanin ko so take ta kashe maki kud'in shiyasa na taso da kaina na kawo maki sauran canjin ki."

Aiko ran matar a matuk'ar b'ace tace "Ni wallahi ban aikata da 5000 ba da 2000 na aiketa nace taje ta kai maki, amma bari na kirata na ji gidan ubanwa ta samu kud'in nan sabida nima da kyar na sami 2000 d'in na bata ta kai maki cikin d'aga murya tace ke uban miye ma sunan ki zonan yau sai naji ubanda ya baki kud'in nan.

Yarinyar da tunda mai adashan ta shigo gidan hankalin ta ke tashe, tana ji kiran da aka mata tasan ba lafiya ba take cikin ta ya murd'a ya bada sauti k'ululu, mikewa tayi da sauri har tana tuntub'e ta fito daga cikin cuisine (kitchen) ta k'arasa inda suke ta tsugun bakin ta na rawa tace "Gani Ufadi."

Bata tantance ba ta ji saukar mari biyu a tatare da sauri ta dafe kunci ta tana hawaye.

Ufadi tace "Ubanwa ya baki 5000 da kika kai ma mai adashe banyan 2000 na baki? Tsinanniya tambad'ad'iya mai yawon gantali wane mazinacin ne da yaje ya gama shanye ki ya d'auki 5000 ya baki, oh ni yau naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba dama ni nasan jimawar da kikeyi baki dawo gida ba idan an aikeki yawon iskanci ne kike zuwa shegiya mai biyan maza wallahi halinki sai ya k'are kanki, bari ubanki yazo sai na fad'a masa shi dake d'aure maki gindi idan ance mashi kinyi abu yace bahaka bane to yau zai zo yaga abinda nake fad'a masa ya tabata da kina bin maza gashi kud'ad'en da suke baki tun kina b'oyewa har sun fara fito wa sannan kuma abiya ni tawa 2000 d'in wly, karuwa kawai tsinanniya, k'ara uban naki yazo ya san abin yi tun kan ki d'auko mashi abin kunya.

Da sauri ta d'ago tana kuka tace " Wallahi Ufadi ba haka bane." Ta kwashe duk abin da ya faru ta gayama ta na mai k'ara fashewa da wani matsanancin kuka, ban abinda ya mata ciwo kuma ya sata kuka shine cewa wanda ya taimaka da ta kira mazinaci shine babban abinda ya ke kara sata kuka, idan itane ta riga da ta saba da wa'inan mugayan kalaman nan daga Ufadi har sun daina d'aga mata hankalin, amma gashi ta ja ma bawan Allah da baiji bai gani ba daga taimakon ta, bata k'arasa zancan zucin da take ba taji Ufadi nace wa.

"Kinji mak'aryaciya toh ko uban ki bai isa ya min k'arya ba na yarda ba bare ke banza wofi kawai, ni maza tashi daga gaba na tun kamin na buge ki daga ganin wanan banzan halin naki na uwarku kuka d'auko tunda gashi shima tambad'ad'en dan uwan naki yana can yawan neman mata har Canada wai da sunan karatu itama karama an kaita wai Arlit gun k'anwar uwar ku Allah kad'ai yasan abinda ake can ana koya mata dagin tambad'ad'u sai ni aka bar make dan jaraba, miyasa kema ba'a kaiki wani gun ba. irin asarar da kuka d'auko halin uwarku.
Chapter 13 · 0% Book details