← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 69

Sashe 38

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali AFREED ya fara buɗe idonsa kamar me tsoron idan ya buɗe su zaiga wani abin tsoro ko abin ƙi, ya sauke su kan Ali cikin kwanciyar hankali ya miƙe zaune yace "Ali kenan babu abinda nake ɓoye maka kawai dai nima yau tunda na farka na tsintsi kaina cikin wannan farin cikin da bansan dalilin yin sa ba kada ka damu kaji ɗan uwana idan da wani abu ai zan faɗama kaima kasani."

Ali yace "To shikenan nikam nazo maka da wani albishir mai daɗi."

"Dagaske ɗan uwa to faɗa man naji." AFREED ya faɗa cikin zaƙuwa.

Ali ya gyara zaman sa sannan yace "Yaudai nasamu na faɗa wa Khadijah cewa inason ta zata aure ni."

Waro ido AFREED yayi yace "Lah wai Ali da gaske kake kenan, yau ka samu ƙarfin halin faɗa to ya tace maka ita?"

"Batace dani komai ina faɗamata ta rufe fuskarta tana murmushi se kawai tayi saman da gudu, hakan na nuna min ta amince, tunda ba zata fito ta faɗa min hakan kai tsaye ba, kasan halin mata da alkunya."

AFREED yace "Hakane ɗan uwa ina taya ka murna sosai naji daɗin zancen dama ba tun yau nake cewa ka faɗama ta tun kafin wani ya riga ka amma tunda ta amince yanzu dai ya kamata kafin mubar garinan tanti Aicha tasan da zancen tunda kigin kwana biyar mu bar garin, kabari ni zan faɗa mata, ita kuwa sai ta sanarma dady."

"Eh haka za'ayi ɗan uwa."

Ali bai ida rufe bakinsa ba akayi sallama tareda turo ƙofar ɗakin AFREED Umar ya shigo, amsa masa sallamar sukayi kafin ya ke ƙarasowa gun da suke shima ya ne mi guri ya zauna sannan yace "Yaya AFREED wajanku nazo ku duka Allah ya taimake ni kuna tare, nazo ne muyi wata magana mai mahimmanci Allah yasa dai zaku goyi bayana kuma kusamin hannu ku masu albarka."

Murmushin shi mai birgewa yasaki sannan yace "To muna jin ka Umar ai tunda naji kace min yaya yau nasan da abinda zaka faɗa yanada mahimmanci, to faɗi muna sauraran ka idai maganar Allah da Annabi ce mizai hana mu saka maka hannu."

Ali yace "Sosai kam mu masu baka goyon baya ne akan komai idan dai bai saɓa wa Allah ba."

Murmushi Umar ya saki tareda sosai kansa sannan ya duke kansa yace "Yaya AFREED yaya Ali dan Allah ku taimaka ku bani auren ƙanwata kuma masoyiyata abar ƙauna ta Fariya ku taimaka ku min rai ba dan niba sai dan Allah, kuga dai kam ina da halin kwarai kuma zan riketa amana wallahi ba za'a samu matsala ba insha Allahu." Sai yayi shiru daganan yana jiran jin abinda zasu faɗa.

Kwashewa sukayi da dariya sosai suke yin dariyar, dan AFREED dariyar da yayi yau bai ma taba yin taba sabida abin ya mugun bashi dariya, saida sukayi mai isarsu sannan AFREED ya maida hankali sa sosai garesa tare da dafa masa kafaɗa yana murmushi yace "Dama ai nasan da walaki goro a miya, inba haka ba babu abinda zaisa ka zauna kana min magiya harda wani kirana da yaya yau da wani ladabi kamar da gaske, to wai ku yau wahayin soyayya aka maku ne da kowa yabi ya zare da zancen yana son waga yana son waga, dan yanzu Ali ya gama faɗa min cewa wai shima yanason Khadijah harma ya faɗa mata, injin dai kaima ka sami Fariya ka sanar da ita har kun daidaita?"

Da Dariya shima Umar ya kwashe sannan ya ɗan tsagaita yace "Ashe bani kaɗai ne na kamu ba to nagode wa Allah da yanzu kun haɗe man kai kuyi ta surfaman iskanci dan haka yanzu ai sedai a yiwa juna kuma na ma fasa ladabin daidai nake daku duk wanda ya taka ni zan rama."

Murmushi AFREED yasaki yace "Kaida Ali dai kudai ma juna dama ni ba ajinkun bane kusan da duk na girme maku, sannan kuma ni nace maku ga Wada nakeso nazo na zauna ina magiyar ku taimaka ku bani wacan inaso dan haka kuyi biyayya kokuwa na hana ƙannina wallahi naje waje na sama musa mazaje na gari na aura masu sabida kam yanzu nine mahaifin su kuma yayan su sai wanda nakeso zan bamawa kuma kam ko iyayenmu ba zasu can za zabina ba akan ƙannina." Ya ƙarasa faɗa yana murmushi.

Saukowa suka da sauri ƙasa tareda kama ƙafafunsa "Yaya AFREED gamu ƙasa dan Allah a taimake mu a bamu aurensu mun tuba ai ba zamu ƙaraba."

Murmushi AFREED yayi sannan yace "To shikenan ashe dai anaso da bakuyi biyayya ba sai na nuna ƙarfin ikona akan ƙannina na bama wasu amma tunda kunyi ladabi na baku halak makalak sedai wani abu da baku sani idan kuka kuskura kuka ɓata masu rai nima kam zakuga ɓaci raina."

Da sauri sukace "Hakama bazata faruba baba AFREED, dan wannan ya wuce yaya sai baba suka faɗa tare da kwashewa da dariya sannan suka koma gurinsu suka zauna."

Umar yace "To nifa yaya ban samu na sanar da ita wallahi dan na ƙasa sanar mata, gani nake kamar ba zata amince ba ko zaka taimaka ka faɗa mata?"

AFREED ya murmusa sannan "Ashe ban sani ba kai matsoraci ne haka za'ayi abin naje baka ƙanwar tawa idan akayi sallama ka shige ƙarƙashin gado kace taje ta buɗe mutanen banza su hallaka min ita, to nafasa baka."

Da sauri Umar ya riƙo hannu AFREED yace "Haba yayanmu ayi hakuri karmin haka, zanje na sameta na faɗa mata yau ɗin nan ba sai gobe ba a taimaka min idan basamu Fariya ba zaucewa zanyi."

AFREED yace "Dadai yafiye maka kaje kasame ta ku daidaita daganan sai musan abinyi."

Daga haka suka miƙe suduka suka nufi ɓangaren tanti.

******* ****** ****** ******

Yau saura kwana uku saukar su AFREEN kuma ya kama saura kwana biyar su AFREED za su koma garin su wato Niamey tunda hutun ya ƙare, kenan idan ayi sabkar da kwana biyu su zasu tafi.

Kuma sabkar da za'ayi harda Khadijah d'iyar tanti Aicha itama tana cikin wa'inda za'ayiwa saukar kallo kuma da Zeinab ƙanwar AFREEN.

AFREEN na zaune ɗakin tanti suna tsara abinda za'ayi a saukar Alkur'ani nasu mai girma, wayar tace ta hau ringin, tana dubawa taga KAMAL ne ke kiranta a take ta ɗaga sabida ita ganita miye abin ɓoyewa tanti wani abu daya dagan cewa ba dan haka, ta ɗoki wayar a gabanta, daga cikin wayar aka yi sallama ta amsa tare da cewa "Ina yuni?"

Batare da ya amsa ba yace "An yuni lafiya?"

"Lafiya lau, ya gari, ya aiki?"

KAMAL yace "Alhamdulilah, ya mutan gidan duk suna lafiya ko?"

Tace "Lafiya lau" a taƙaice

KAMAL yace "My FREENKA ( AFREEN KAMAL) dama na kirane naji abinda kukeda buƙata na saukar ku kinji ina jinki faɗa min."

A sanyaye tace "Non on a besoin de rien (a'a bamuson komai)."

Sai yace "Ah ban gane bakuson komai ba, kodai abinda zai fitowa daga gareni ne bakuda buƙata?"

A shagwaɓe ta ƙara lankwasar da murya tace "A'a wallahi ba haka bane mon roi (My king) kawai dai komai papa yace zai siya mana."

KAMAL yace "Haba my FREENKA to ni miye anfani na idan har na bar papa ya siya maku abinda za kuyi anfani da a saukar ku ki faɗawa su papa cewa na ɗoki nauhin komai na saukar nan dan Allah a barni nayi."

"A'a Please mon roi da ka barshi wallahi ai babu wani abu."

To bakinga irinta ba kece dama bakiso nayi shikenan babu matsala."

Yana ƙoƙarin kashe wayar tace "Tsaya kada ka tsike kiran dan Allah naya yarda zan faɗa masa shikenan ko."

Murmushi KAMAL ya saki mai sauti sannan yace "To koke fah yanzu kiyi liste ɗin abubuwan da kuke buƙata."anjima zanzo nakarɓa sai na siyo komai da komai."

AFREEN tace "Ok to babu damuwa insha Allahu zanyi."

Yace "To D'accord sai nazo ko?"

Tace "Eh Allah ya kawo min kai lafiya."

Yace "Ameen, ki kulamin da kanki."

Tace "Insha Allahu kaima ka kulamin da kanka."

Yace "Karki damu za'ayi yanda kikeso gimbiya ta."

Murmushi tayi tace "To sai anjima."

Ba tare da ta tsaya jin abinda zai faɗa ba ta katse kiran."

Tareda juyowa ta kalli tanti ta lokacin guda ta sada kanta ƙasa, dan ita tama manta cewa tanti na ɗakin ta biye masa sunata fira haɗa wani ya kulla mata da kanshi, kai amma naji kunya gaban tanti na zauna inata soyayya."

Tsira mata idon tanti tayi kamar mai son gano wani abu a tatare da ita, sai ɗan musƙuta tace "Aya ɗiyata ki daina jin kunyata ninan kamar abikiya ta na ɗauke ki dan haka ki daina kunyata kinji ko."

Murmushi tayi sannan tace "Wai tanti cewa yayi kada papa ya siya komai shi zai yi mana komai da akeyi."

Kura mata ido tanti tayi na ɗan lokacin sannan tace "To ai bai wani abu kawai abarshi yayi tunda hakan yakeso yanzu kije ki faɗa wa papa naku kamin je ya siyo abubuwan saukar ta ku dan nasan ba zasu wuce yau ba."

Tashi AFREEN tayi ta fita ta nufi sama dan zuwa ta gayawa papa.

Tana fita tanti tayi ƙwafa tare da cewa...............

Kuyi hakuri da wannan ba yawa😊😊😊🥰🥰🥰
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit

Par

*QUEEN ZEEFAT*

_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_

*Wattpad@nazichou*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

*Page* : 35 & 36

Tana fita tanti tayi ƙwafa tare da cewa "Zanyi maganin ku ke da KAMAL ɗin, indai ina raye ai ƙarya ne kiyi farin ciki
yarinya, cikin gidan ace anfi sonki kan kowa to ha indai ba Hamida ce akeson kamar yanda ake sonki ba, to insha Allahu farin cikin da na uwarki ya ƙare zanyi maganin keda maifiyar taki badai ku ƴan gaban goshin Alhaji ba, hum ai sai ya dawo daga rakiya ku har indai da raina sai na saka maku ɓakin cikin da zaku ƙasa fita daga cikin sa har ƙarshen rayuwar ku."
Chapter 38 · 0% Book details