Sashe 61
Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani murmushin ƙarfin hali AFREEN ta antayo ma Mahaifin nata sannan tace "Haba papa sai kasa naji kamar nafi ƙarfin kamin zaɓin abinda kaga yafi dacewa dani, sai kasa nayi tunanin na kasa ma biyayya yanda ya kamata papa, miyasa dan kayi min miji kuma sai kanemi shawara na kamar ni ce na haifi kaina dama ai a musulunci iyaye su suke zaɓa yaran su miji na farko to miyasa ni dan an zaɓa min kuma za'a nemi shawara na ai kawai umarni zaka ban papa kuma na bi umarnin wallah, ni kawai fata Allah ya sa haka shi ne mafi alkairi dan na san papa ba zaku taɓa yimin zaɓin wanda ba na gari ba na san da har da son da kake min yasa kayi min wannan gatan, ba abinda zan maka sai godiya da kuma godewa Allah da ya bani mahaifi irin ka duk wanda ya samu iyaye irin ku ai sai hamdalah ga rabbil izzati. AFREEN ta ja tayi shiru dan jin zuciyar ta nason karyewa yanzu nan zata iya fashewa da kuka abinda kuma bata son papa ya gane ta na cikin damuwa kan wannan zaɓin nasa, dan da zata iya ƙurma ihu a lokacin da papa ke sanar da ita da tayi sai dai bazata iya ba dan farin cikin mahaifin ta ya fiye ma ta komai.
Cike da farin ciki papa ke kallon AFREEN da ta duƙe kai tana kallon ƙasa sannan yace "Allah maki albarka Allah maki albarka Allah maki albarka AFREEN har yau har kullum ina alfahari da ku duka yaran da Allah ya bani ba ma kamar ke ban taɓa aza magana kika tsallake ta ba Allah maki albarka Allah baki ɗiyan dake ma za su maki fiye da yanda ki ke ma mu Allah ya saka maki da aljanna firdaoussi."
Ameen AFREEN da mahaifiyar ta suka amsa sannan papa ya koma cewa kin amince da zaɓi na, amma ke baki faɗa man ko ki nada wanda ki ke so ba?"
Da sauri AFREEN tace ba bu kowa papa ai da na sanar da kai."
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Écrit
Par
*QUEEN ZEEFAT*
_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_
*Wattpad@nazichou*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*
*Page* : 59 & 60
"To shikenan Allah maki albarka ki rubuto man a takarda duk abinda kike so ki kawo man koma miye idan dai bai fi ƙarfi na ba zan maki shi kuma in ba na saɓan Allah bane, sannan zan turo maki da wasu kalolin motoci guda biyu sabin fitowa har yanzu basu kawo nan ba ko a ƙasashen waje ba ko wane ya san su ba sai ki zaɓi guda na siya ma kamin bikin ki sai a kawo maki insha allah da akwai wasu shaguna da na buɗe da sunan ki a garin Niamey na ki ne duka haka kayan dake cikin, dama faɗa maki ne bayan, amma idan kika duba account ɗinkin zaki ga kusan kullum kuɗin cikin ƙaruwa suke, har ma kin taɓa min magana akan haka na ce maki ni ne nake ajiya a cikin account ɗin to ba haka bane na ki ne kawai kuma duk ribar da ake samu ce ga shagunan Allah maki albarka."
"Nagode papa Allah saka da alkairi amma gani nake kamar sunyi yawa papa duba da ba ni ɗaya ba ce."
"Karki damu da wannan ke ta ki kyautar ta musamman ce, amma suma duk na shirya wa kowa ta shi sedai suma ma ba yanzu zan basu ba sai duk nan gaba sedai a gaskiya tasu ba kai taki ba."
"To mun gode papa Allah ƙara arziki mai albarka Allah ƙara lafiya da nisan kwana Allah kare ka da ga sharin duk wani abun shari ameen."
Da Ameen papa da maman suka amsa sannan papa ya ƙara cewa "Allah maki albarka ta shi kije ku fara shirin bikin ki tun yau saboda wata ɗaya da kwana shida ya yi saura."
Gaban AFREEN ya ƙara faɗuwa kuma ta ƙara shiga damuwa sai taji kamar ta aza hannun a kai ta yi ta kuka amma ba dama, kuma sai ba ta nuna ma papa da maman hakan ba se miƙe da tayi cikin mutuwar jiki ta bar ɗakin.
AFREEN na shiga ɗakin ta faɗa kan gado ta shiga rusa wani irin kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar duk wani mai saurare gwani ban tausayi, saida tayi mai isar ta sannan tayi shiru duk idanun ta sun kunbura sunyi tulutu gashi kuma abun ga mai mayan ido ta ta shi ta shige bayi ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallah azahar da ta dalilin kiran sallah yasa ta daina kukan, a sujidar ta ƙarshe ce ta shiga rera wani sabon kukan mai ci rai tana faɗawa Allah "Ya Ubangiji ya Sarkin sarakuna ya mai samai da ƙasai ya hayyu ya ƙayyum, ta shiga dai yiwa Allah kirari sannan tace ya Allah idan har zaɓin mahaifin na alkairi ne a gare ni Allah kasa na yarda da shi hakan kuma naso wanda zai haɗa ni dashi na amince idan kuwa AFREED shine alkairi a gareni Allah ka wargaza shirin mahaifina ka barni da masoyi na wanda nakeso idan shima ba alkairi ba ne Allah haɗi da alkairi sannan kasa nayarda da shi kuma na so shi."
AFREEN dai tai ta jero addu'a ta na kuka mai tsananin sai da har taji kanta zai fara ciwo kan ta daina kukan ta bawa kanta hakuri, sannan ta ɗauki Alkur'ani mai girma ta shiga karantawa a nan ne ta ji salama taji hankali ya ɗan kwata yunin ranar ta kasa saka kofa ruwa ne a cikin ta bare abinci, sau biyu mahaifiyar ta na shigowa ta kira ta ci abinci sai ta tardo ta kwance ta lahe kamar mai bacci, alhali ba bacci take ba kawai daga taji takun tafiyar za ta shigo ɗakin tane sai ta yi maza ta yi kwace ta lahe kamar mai bacci, haka AFREEN ta yuni ranar ko kiran AFREED ta kasa ɗauka don gani take mi zata faɗa masa ya zai ɗauki zancen ta ya zatayi itama da son da take masa yanzu nan rabata da shi za'ayi, idan ta tuna haka sai ta shiga furta inna lilahi wa inna ilaihi raji'un, tare da rokon Allah ya kawo ma ta sasauci raɗaɗin dake cikin zuciyarta dan ba ƙaramin so take yi wa AFREED, saboda bata san ya akayi take son sa ya yi mata mugun kamu har take ganin bata iya rabuwa da shi duk ratsi, haka ma bata iya watsa ma Mahaifinta ƙasa a ido kawai ta bar ma Allah zaɓi.
Da wajen ƙarfe huɗu da rabi AFREEN na zaune saman darduma wanda tunda ta gama sallah la'asar ba ta ta shiba saboda tana karanto azkar ɗin yamma mahaifiyar ta shigo ɗakin da sallama ɗauke da bakin ta, ba tare da AFREEN ta ɗago ba ta amsa sallamar, maman ta nemi guri bakin gado ta zauna sannan AFREEN ta ɗago tace "Maman barka da gida."
Saida maman ta kwashi kusan minti ɗaya ta na karantar halin da AFREEN ke ciki sannan tace "Yawa AFREEN lafiyan ki naga duk idon ki ya kumbura, ko kuka ki ka yi?"
Da murmushi AFREEN ta dubi mahaifiyar ta, Sannan tace maman kuka kuma da aka yi man mi zanyi kuka, kawai kaina yake man ciwo tun dazun nan nayi bacci na tashi amma bai daina ba sai na sha magani kuma na sake kumawa bacci saboda ina tunanin ko bacci da na jima bayi bane a daren jiya yasa hakan amma ashe ba haka bane, tunda ga shi yanzun ma ciwon ya ke min."
Har ga Allah maman ta yarda da hakan shiyasa cikin tausayawa tace "Haba AFREEN ya zaki zauna da ciwon kai har tsayin wannan lokaci ba zaki faɗa ba, gashi kuma kika yi ta bacci baki ci komai ba duk safiyar yau ko yinwa ai zata saka maki ciwon kai mana, tashi muje kici abinci sai mu tafi asibiti a dubaki ai ba a zama da ciwo haka yanzu haka zafi ne ya maki yawa.
"A'a maman da safe nayi breakfast fah lunch ɗin ma banji yinwa ne shiyasa bayi ba."
"To yanzu tashi huce muje ko ba kaijin yunwa zaki ci abinci mu wuce asibiti ehe saboda baki isa mahaifin ki ya dawo ya ta do baki da lafiya ya hauni da masifa ba gaskiya."
Ba musu AFREEN ta tashi ta lumke darduma ta mayar da ita inda take ta dawo kusa da mahaifiyar ta tace "Maman ai papa ba zai san haka ba idan bake ki faɗa masa ba kinga ba sai muje asibitin ba daga naci abincin sai na koma shan maganin shikenan zanji sauƙi da ikon Allah."
Wata yar harara maman ta sakar mata sannan tace "Ke ni wuce muje."
Maman tayi gaba AFREEN tabi bayan ta, suna zuwa falo maman ta nuna ma ɗaya daga cikin mayan kujerun dake falon tace "Zauna a nan zanje na sama maki abinda zaki ci."
"Ba musu AFREEN ta zauna inda ta nuna mata, sannan maman ta juya ta nufi kitchen, ba wani dauki lokaci ba ta fito da plet da kuma juice 🥤 ɗin mangue (mango🥭) ta ajiye a gaban AFREEN da keta raraba ido don samun mafita da zata hana su je asibiti.
Maman tace "Zauna saman kafet ki maida hankali kici bari na kawo maki ruwa, maman da ta nufi fridge sai ta ɗoko hada lait (milk🥛) da bidon ɗin ruwa ta nufo AFREEN da su sannan ta ajiye mata, ta zauna a saman kafet ɗin kusa da AFREEN tace "Mi kike jira da baki fara cin abinci ba maza ki fara kina ga bataman da lokaci," maman ta faɗa tana mai buɗe plet ɗin na sama.
Soyayyar doyace da taji kwai sai yar vinaigrette a gefe, daga gani kasan taji daɗi.
Har AFREEN ta fara ci ta ɗago tace maman ai dai kinsan ba duka zan ciye wannan abin mai yawa haka."
Wannan abin ne ke da yawa kawai dai baki son cin abinci narasa komai yasa haka duk gidan nan kece a baya wajen kincin abinci, to yi maza kici baki wanda zaki iya ci sai muje asibitin.