← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 69

Sashe 5

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Papa ya jawo AFREEN dake ya zaunar da ita hawaye cike da idonta yace "AFREEN maza yi zaman ki tunda bata son ki kama mata. wani yaro da bazaya fuce 12 ans (years) ba yace "Maman dubi yanda umma kema anti AFREEN fada hada tureta da kadan ta fad'i alhalin batayi mata komai ba, Maman kice ta bar mata fada kada tayi kuka maman ta juyo garshi ta na mai murmushi tace "laifi tayi shiyasa amma bakaga ta daina ba yace "to Maman mi tayi tace "yanzu dai yi shiru ci abinci ka ya maida hankali sa yayi ga abincin sa ya fara ci. Umma ta gala masa harara dai bai masan tanayi ba.

Papa ya kali AFREEN "yace maida hankali kici abinci ki kinji AFREEN tadago takali mahaifin nasu daidai lokacin da hawayen da take kokarin boyewa suka zubo. Subhanallah "AFREEN kuka??? Maza share hawayen ki, tashi dauko abinci mu koma cikin falon in baza ki iya ci nan ba papa ya fada yana mai mikewa.
Da sauri AFREEN ta mike tare da daukar assiete (plet) biyu nata dana papa, suka bar dinning d'in tare da koma wa cikin falon, papa ya zauna saman kujera, ita kuma saman tapis (carpet).

Papa yace" AFREEN miye kuma abin kuka daga maki magana tace papa baka ji munafuka tace min fah "to in tace miki hakanan sai mi bakin san bahaka nan bane ba, ta daga kai alamar "eh" to ki daina zubda hawayen ki sabida Salamatou,in ba haka ba to ta dinga maki abinda taga bakiso kenan, kina abudai kamar baki san halinta ba. haka dai papa yata bata baki har suka gama cin abincin,ta dauke assiete din takai cuisine (kitchen). Ta dawo ta dauko masu ruwa da jus (juice) da verre (cup) dukawa tayi kusan papa ta zuba masa jus (juice) sannan ta zuba ma kanta ruwa tasha, suna gamawa ta tatare komi ta mayar dashi ma'ajiyar sa.

sannan ta dawo wajan papa ta dan duka "tace papa zanje nayi karatu yace to 'yar albarka ayi karatu lafiya.

Daganan AFREEN ta nufi dakin ta. Papa na zaune falo 'yan ci abinci a salle à manger (dinning) suka shiga falon da alama sun karasa cin abincin.

Maman bata tsaya cikin falon ba ta nufi escalier (stairs) dan zuwa dakin ta, umma ta karaso ta zauna kan kujerar da papa ke zauna, tare dacewa "yo shalelan taka tafiya tayi ta barka, dagowa yayi ya kaleta ba tare da ya ce mata wani abuba ya maida kalon sa a tv, ta koma cewa " hada wani kicihin biyu yarinya falo wai ita yar so, "du ba kai ke daure mata gindi ba tana abinda take so nan ma baice mata komi ba hankalin shi ma bai wajan ta, take umma ranta ya bace tace "kar dai mukaga lega wlh, adai juri zuwa rafi watarana tulun zai fashe. "Wato baban fauzia nice na ke maka magana kana shareni sabida 'yar zinariya ko, wato kenan ga mahaukaciya wada batada hankali tana magana ana shareta to alhamdulilah watarana za'aga ranar magana ta.

Tanti yara dake tsaye tana sauraren abinda umma ke gayi tace "haba Salamatou miye abin cika mutane da surutu kamar an jonaki kinyi magana d'aya kinyi biyu an shareki, to miyasa bazaki hakura da zancan ba kinata nanata abu d'aya, du kinbi kin takurawa yarinya da bata maki komi ba kawai don kiyaya, Tanti taja wani dogon tsaki... Bata ida rufe bakinta ba, umma ta tashi cikin tsawa tace" yimin shiru 'yar biya yar cusa kai inda ba'a san darajar ta yar' neman gurin zama gun miji da kishiya kina wani shishige ma ya'yan' ta don munafurci wai ke mai son su, dan mahaifin su ya dinga kalon ki da dajara dan kinibibi, to wlh anyi walkiya mun ganku sedai ayi ma wasu ba muba munafuka ai wlh na ganoki kar nake kalonku gaba d'aya ah to, kuma wlh ki fita haraka ta ki daina samin ido tunda ni ba 'yar biya bace ehe. Ta tab'a hannu tare da komawa ta zauna, tanti harta bude baki zatayi magana, papa ya dago ya watsama ta wani irin kalo mai nuna cewa yi tafiyar ki, ki barta batada hankali, yasa Tanti juyawa ta nufi dakin ta itama, tajin umma nacewa "kika ki tsaya ki fad'i abinda ke ranki in ba tsoro ba, yanzu kiga b'acin raina, Tanti dai tashige daki batace mata kala ba bare tajuyo ta kaleta.

Falon ya rage daga umma da papa sai wasu yara 'yan maza guda biyu dake zaune suna kalon umma dake ta masifa kamar an aiko ta, don tuni ya'yan umma su nufi dakin su tunda sukaji tafara banbami fada. Dan babban daga cikin daba zaya fuce 16 ans (years) ba ya mayar da kalon sa gun mahaifin nasu yace "papa mu zamu koma ban'garen mu don muje muyi revision, cikin kulawa papa ya dawo da kalon sa garesu yace " to maza ku tashi ku tafi kuyi karatu, ka dinga nunawa k'aninka ida bai gane kaji ko fahad. Wanda aka kira da fahad "yace insha Allah to ku tashi ku je Allah maku albarka suka amsa da ameen sanan suka fita daga falon gaba d'aya.

AFREEN na komawa daki ta nufi gun da take ajiyar kayan karatun ta na école (school) ta ciro papier (peper) da tashigo da ita d'azu taje tanemi guri ta zauna ta fara traité din exercice (exercise) din cikin nutsuwa.

Khairat na fitowa daga salle à manger (dinning) dama ita bata tsaya cikin falon ba direct dakin AFREEN ta nufa, tana shiga ta sameta tana exercice ta zauna kan kujerar da ke dakin, "tace ma soeur (yar uwata) miyasa kike damuwa da abinda umma tamiki kamar bakisan halinta ba AFREEN ta dago ta kaleta tare da sakar mata murmushi da yasa fossette (dimple) dinta fitowa, tace "bakomi gande soeur (big sis) juste (just) munafuka da tacemin ne ya d'an sosa min rai, amma yanzu ni harma na manta da abin, wanan exercice din ke gaba na. khairat tace "kin tabata tace "wlh kuwa soeurette (sister) "to shikenan bari na barki ki karasa karatun, idan kin gama kizo daki na muyi fira sai ma ki kwana a can "to anti na sai na shigo AFREEN ta fada. Khairat ta tashi ta nufi kofa ta fita daga dakin ta nufi nata.

30 munite AFREEN ta dauka tana traité din exercice (exercise) din kamin ta kamala, wayarta dake saman gado kamar jira take ta ida karatun ta dauki tsuwa tana neman agaji karasa wa tayi ta dau wayar mon amie intime (aminiya ta) taga yana yawo kan écran ( screen) din wayar murmushi ta saki tare da dauka kiran ta kai kune har ga Allah taji dadin ganin kiran hasina. Daga cikin wayar akayi salama ta amsa, hasina cike da jin kunyar kawar tata tace " kawata bakiyi bacci ba ina ta tunanin kiranki yanzu, ina gudun kinyi bacci kar na tayar dake.

"A'a banyi bacci ba ya kike, hasina ta dan nisa tace "lafiya lau, dan Allah kawata ki yi hakuri ki yafemin abinda da miki dazu wly ba da niya nayiba kanin fuskarki yayi min bazata, wlh bata kamantaki ba da irin wanan mugun kyau da nagani a gareki bane shiyasa, wlh kyau ki ya firgitani sabida wlh kyau ki bai musultuwa kawata, Allah dai ya tsareki ya kare ki daga sharin mutun da aljan da karfe bature ashe ba banza kike rufe fuskaki ba, dan Allah kiyafe min.

AFREEN dake sauraren ta sauke wata agajeriyar ajiyar zuciya tace " Ameen bai komi kawata kuma ni baki min komi ba inda ma kinyi na yafe maki "alhamdulilah na gode kawata Allah barmu tare, bari na barki ki kwanta sabida gobe akwai école (school) hasina ta fada, AFREEN "tace to kawata Allah tashe mu lafiya, ameen hasina ta fada tare da katse wayar.

AFREEN na ajiye wayar ta nufi armoir (wardrobe) ta dauko kayan bacci ta ta fita daga dakin.

Bangaren hasina kuwa tana katse kiran ta daka tsale tace "ashe batayi fushi dani ba Allah na gode ma da kaban kawar kirki irin AFREEN..........

Ina kaunar ku masoya ...........💞

Commenté

Et

Partager

Comment

And

Share

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

ECRIT:

PAR

QUEEN
ZEEFAT

Yar
Mutan
Niger

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

Bismilahir rahamanir rahim

Page 5

Tana fita ta nufi d'akin Khairat da ke kusan nata da sallama ta shiga amsa mata sallama Khairat tayi dake bakin gado tana manipuler d'in wayar ta mike wa Khairat tayi taje ta kamo hannu AFREEN ta zaunar da ita bakin gado, tace "yawa 'yar k'anwata, ina aza baza ki zo ba?" AFREEN tace "mi zai hana anti? kawai natsaya yin waya ne." "waya kuma AFREEN, a cikin daren nan, to ko dai nayi k'ane ne banda labari ? "Lah anti wane irin k'ane kuma," "to ni sani nayi AFREEN, nufi na ko kinyi saurayi ke da toujour (kulin) kina cikin nikaf, bansan ko taya wani zai gan ki ba har yace yana son ki a cikin nikaf ba, an yi mutun kulin cikin nikaf kamar dai wanda yayi wani mugun laifi Police na neman shi, Allah dai shirye ki AFREEN."

"Hum anti kenan saurayi fah kika ce? wanan ai sai ku 'yan mata, ina ni ina saurayi yanzu duka ta nawa ni ke."

AFREEN ta fad'i maganar tana dariya tare da kalon 'yar uwar ta, itama Khairat dariya tayi tace "ke d'in ce ba 'yan mata ba? Tubarkallah god'aigo'd'ai da ke da 18 ans din shi ne zaki ce a ta nawa kike, baki isa aure bane ko miye nufin ki? ni dai naga har 'yan 15 ans an masu aure baran tana ke macha Allah da babu abinda kika rasa na manyan 'yan mata masu ji da kansu,"
"haba anti a 18 ans (years) a ka min aure ai rishin tausayi ne gaskiya ni ban wani isa aure ba yanzu, tu vois je n'ai même pas fini mon étude, kin ga kenan ban girma ba" AFREEN ta fad'a tare da yin murmushi.
Chapter 5 · 0% Book details