← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 69

Sashe 21

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To yau ma haka ce ta faru AFREEN suka tara gabad'aya aka rufa gidan suka nufi masallaci don yin sallah juma'a kuma duka cikin su AFREEN ce kad'ai keda nik'af.

Sai mu had'u da next page💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃

Taku harkulin mai kaunar ku❤️🥰💓

"QUEEN ZEEFAT📝📝✍🏻

Inayinku irin sosai d'in nan masoyan 🌸ZANBA CIKIN AMINCI🌸 alkairin Allah ya kaimaku duk inda kuke💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

ÉCRIT:

_PAR_

*QUEEN ZEEFAT*

Yar
Mutan
Niger

Wattpad@nazhabibou

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM

Page: 17 & 18

Tangamemiyar ma'aikata ce mai matuk'ar kyau, ma'aikatar karshe ce wajan tsaruwa a saman k'ofar ma'aikatar da mayan harufa an rubuta *MINISTÈRE* (wato ma'aikatar ministoci, inda ko wane minister keda babba kuma had'ad'en office) sojoji ne sosai gewaye da ma'aikatar daga cikinta har wajan ta tsaro ke akwai sosai, wasu had'ad'un motoci ne guda biyar suka kuno kai a cikin ma'aikatar suna gama parking sojojin da ke cikin motocin guda hud'u suka fito da sauri tare da nufar cikon motar ta biyar, duk suka tsaya a tsaye kyam kamar an dasa su tare da haka bidigogin su irin ma su jiran tab'in nan su sakar maka alburushi, gaban motar aka bud'e Ali ne ya fito ya nufi k'ofar baya ta motar ya bud'e, kusan minti biyu da bud'e k'ofar sanan na cikin motar ya ziro kyakyawa k'afar sa mai sanye da wasu had'ad'un takalmi masu mugun kyau Kana ganin su kasan bana na k'ananun kud'i bane.

Ida fito da k'afar guda yayi kamin ya k'arasa fitowa gabad'aya, sai a sannan na gane da AFREED ne ya had'e colin wata dakakiyar shada bleu (blue) da tayi matuk'ar d'aukar jikinsa dan ba k'aramin kyau kayan suka masa ba.

Jerawa sukayi shida Ali suna tafiya sannu sannu cikin kwonciyar hankali da nutsuwa kamar basa son taka k'asa su kuwa garde-corps (bodyguard) d'insa na take masu baya abin kwanin sha'awa masha Allah, kana ganin AFREED da Ali zaka iya tunanin 'yan biyu ne sabida suna matuk'ar kama da juna, sedai AFREED ya fishi tsayi shikuwa Ali ya fi AFREED haske.

Suna shiga cikin katafariyar ma'aikatar k'ananun ma'aikata na kwasar gaisuwa amma hannu kawai AFREED ya samu damar d'aga masu 'yar karama tafiya suka Ali yayi Saurin k'arasawa bakin k'ofar Wani bureau (office) wanda sama k'ofar bureau (office) d'in an rubuta *MINISTRE DE DÉFENSE ET DE SÉCURITÉ* (wato ministan sojoji da na tsaro).
Masha Allah baban office ne k'ayatace wanda ya amsa sunan sa office don table ma da kujerun dake cikin bureau (office) d'in kad'ai abin kalo ne.
AFREED da garde-corps d'in sa na ida k'arasawa bakin k'ofar office d'in bai tsaya komai ba ya shige ciki sukuwa suka tsaya a bakin k'ofar kamar an dasasu, directe (direct) wajan luntsumemiyar kujerar sa da ke gaban table d'in bureau sa ya nufa ya zauna da bismillah ya fita da hular dake saman kansa tare da fad'in oh mon dieu (oh my god) ya duk'e tare da aza hannayan sa da kan sa a saman table d'in dake gaban sa.

Ali dake bakin k'ofar tare da garde-corps ya kalesu yace "biyun da suka saba tsayawa a bakin k'ofar su tsaya ku kuwa sauran kuje kuyi wanda kuka saba har a nemeku da sauri suka sara masa tare da cewa d'accord monsieur (ok sir) biyu suka tsaya sauran sukayi gaba shi kuwa ya fad'a cikin bureau (office) d'in AFREED tare da rufo porte (door) d'in yaje ya zauna cikin d'aya daga kujerun dake fuskantar AFREED.

Kalon AFREED ya tsaya yanayi na tsawon minti biyu kamar wanda keson gano wani abu kamin ya d'an nisa yace "Wai fréro (broh) mike damunka ne tun fah jiya da dadare bayan mun dawo daga gun dady naga kamar baka cikin walwala na tambaye ka Kuma kamin shiru dan Allah yanzu dai ka fad'a min kwakwata nima ka saka hankali na ya k'i kwanciya duk na damu walahi bana son ganin ka a haka."Ali ya fad'a da damuwa k'arara a fuskar sa.

A hankali AFREED ya d'ago ya kalli Ali tareda sakin boyayar ajiyar zuciya sannan yace "Fréro ( broh) mi kake ganin zai dameni da ya wuce abinda dady ya mana magana akan shi jiya."

Wani k'ayatacan murmushi yayi sannan yace "Dama nasan babu abinda zaiyi mugun daga maka hankali kamar wanan maganar da dady yayi amma miye abin d'aga hankali kan abu me sauk'in irin haka."

Wani uban harara AFREED ya narkawa Ali kamin yace "Mike me sauk'i a cikin abinda da dady ya fad'a ko ka d'auka da wasa yake ne, ko dai dan kai a shirye kake ne sabida kasan duk fad'a a kaina aka sauke kai banda kai shiyasa kake wani cewa sauk'i ne da shi."

"Hum AFREED kenan banga miye abin tada jijiwoyin wuya abinda wanan abin sauk'i ne dashi kamar yanda na fad'a maka kasan ko miye sauk'i shi?"

Girgiza kai AFREED yayi alamar a'a.

D'an nisawa Ali yayi tare da gyara zama sannan yace "AFREED abinda ya kamata kayi ana shine kayi gagawar fitar da matar aure tun kafin dady yayi maka auren da bakaso, wato ya zab'a ma matar da kanshi ga mata nan iri iri sunna kawo kansu gareka amma baka kulasu ka darje kawai ka zab'i d'aya a cikin masu kawo maka hari, dubi fah wanan farin jinin da Allah ya maka yanda mata da kansu suke kawo maka talar kansu amma kana sharesu, gashi babu inda Allah ya rage ka AFREED kayi niya kamin lokacin da dady ya iba mana ya k'are."

"To wai kai Ali da kake tacewa nayi niya nayi niya tayaya kana ganin ni ko secrétariat ta (My secretary) ban ida tantance ta ba itada kulum tana shigowa office d'in nan fiye da so goma a rana to ko ita akace yanzu na gwadeta to wallahi a saramin babban aiki to tayaya zan kalli wata harnaji inason ta gashi kuma na fison na fida mata da kaina tun kan dady ya zab'a min gashi kuma ni bansan daga zan fara neman matar da zan aura ba, Kuma kai Ali dakake cewa mata masu cewa suna sona tun kamin ni na furta mata masu kalamar so ai har abada ta kayar da darajar ta gareni haba yo ina ajin na mata duka ta zubar to ni mizanyi da mace marar aji da kamun kai kuma wanibi irin matan da suke Nuna ma namiji suna sonsa tun kamin shiyace yanason su to fa'aksarin su ba son gaskiya suke masa ba kawai dai dan wani abu ne da Allah ya yi maka to ka ga irin matanan ba irin matan da yadace ya zauna dasu bane indai yana son samin mata ta gari dan haka babu wace zan zab'a a cikin su." AFREED ya fad'a

Ali yace "Hakane to taya wai zaka sami matar kaida ba kulla su kake ba kasan idan har lokacin da dady ya ibar mana ya k'are bamu fitar da matan aure ba wallahi zamuga b'acin ransa sabida zai iya aikata abinda yace zai aikata a kanmu sabida dai kasan shekara guda ba kwana guda bace bai kamata ace shekara guda da ya d'ibar mana har ta k'are baka fitar da matar aure ba don gaskiya dady ba zaiji dady ba ni wallahi kai nafi tausayi ma sabida baka iya kallon mace bare har kace kana sonta nidai kaga inada wada nakeso ko yanzu dady yace na gabatar da ita to zan gabatar masa da ita kai fah da ko secrétariat ta baka sani ba da kai kawo daga office inka zuwa nata har yanzu baka tantance ta ba to Inama zaka samu damar sanin wata."

"Nima fah shine nike tunani Ali amma Allah zai shige man gaba insha Allah zan samu wada tayi daidai dani kamin dady ya fitar min da mata ina neman zab'in Allah, ina fatan Allah bani mata ta gari ni wallahi inba dan dady ya matsa ba ni babu aure a gabana yanzu duk nawa nake da za'a matsa sai nayi aure."

"Kam wallahi AFREED baka jin kunya kai ne zakace a nawa kake shekara 30 da kakeda itace a nawa kake wanda gashinan har ma kazama tuzuru Ali ya fad'a tare da tuntsirewa sa dariya."

Dariyar shima AFREED yayi sannan yace wallahi Ali kayi mugun rainani ma yanzu shekara 30 kince zaka wani cewa na zama tuzuru to wallahi ka kiyaye ni idan na zama tuzuru to wallahi kaima tuzuru ne tunda dai ba girme maka nayi ba."

Koma dai minene to kaji dashi wajan wata biyar ka bani da haihu ko da kuwa second guda ne ai dai ka girme min don haka yanzu dai nasan kana da ayuka da yawa a gaban ka ka d'auka ka fara ni kaga tafiya ta zanje na dawo."

Murmushi AFREED yayi sannan yace sai ka dawo to ai kasan yau da wuri zamu tashi."

D'aga masa kai Ali yayi sannan ya juya ya fice daga office d'in."

Sai mun had'u a next page💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃

Alhamdulilah...

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

ÉCRIT

PAR

*QUEEN ZEEFAT*

Ƴar
Mutan
Niger

_Wanan page taki ce my kawa my Aminiya ta_ *Rida* *Chou* _que le bon dieu te protège kawar arziki ina yinki irin sosai ɗin nan_

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan
-niger-111773560677003/

_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_

*Page* : 19 & 20

Ƙarfe 12:00am Ali ya shigo office ɗin AFREED tare da ƙaraso kusa da table ɗin AFREED yace "Ranka ya daɗe kataso mu wuce gida lokacin tashi daga aiki yayi, kuma naga kamar da aiki a gaban ka baka kamala ba, kaga kuma ni yinwa nakeji inason naje gida naci abincin don nasan yanzu momy tagama mana spécial, amma dai zan zauna har ka ƙarasa sai mu wuce."
Chapter 21 · 0% Book details