Sashe 25
Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana fitowa daga wakan ɗaure da tawel a ƙugunsa ɗaya a hannun sa yana goge ruwa da ke saman kansa kuma yana ida tsane jikinsa yana kamawa ya nufi gun mirror ya je yayi shafe shafen da ya saba yana gamawa ya nufi drawer ya fito da kayan da zai saka yana saka kayan kuma yakoma nufar mirror ya ƙara ɗaukar turare ya kara feshe jikinsa da shi sosai yayi wanka da turaren kamar ba kuɗi akasa aka siya ba daga kamshi turaren zaka gane tsadadine, ya kammala shiryawa ya fita ya rufe ɓangaren su ya nufi na mahaifiyar sa
Yana shiga ya tardosu zazaune su duka harda Ali suna hira cikin farin ciki da anashuwa, suna ji ƙarar buɗe ƙofa gaba ɗaya suka dawo da kallon su gun daya ke, mahaifiyar sa tasaki wani irin ƙayatacan murmushi me ciki farin dan gani ɗan nata cikin walwala, nuni tayi masa da ya ƙara so ida take sannu ahankali yake takowa cikin natsuwa da tafiyarsa ta ƙasaita da kair ma yake ɗaga ƙafarsa kamar mai gudun jiwa ƙasa ciwo, yana ƙarasowa wajan mahaifiyar sa ya zauna gab da ita a saman capet yana mai tanƙwashe kafafun sa tare da aza kansa saman cinyarta sannan yace "Momy ina kwana antashi lafiya?"
Murmushi ta koma yi sannan tace "Lafiya lau ɗan kirki harka tashi da fatan lafiya lau ka tashi?"
"Lafiya lau Momy." AFREED ya faɗa ataƙaice
Zai koma yin magana ƙanan sa suka rigasa da cewa "Yaya ina kwana ka tashi lafiya?"
Murmushi ya saki tare da kallon ida suke yace "lafiya lau ƴan tagwayen Momy kuma kuna lafiya?"
"Lafiyar mu lau yaya." Farissa ta faɗa tana murmushi
Bata ƙarasa rufe bakinta ba Ali cike da shegantaka shima yace "Yaya AFREED ina kwana?"
Wani murmushin ni zakama iskanci AFREED yayi tare da cewa "Lafiya ta lau ɗan ƙaramin ƙanina."
Dariya sukayi su duka banda AFREED da yayi murmushi shi kuwa Ali ya game fuska
Wata muguwar harara Ali ya sakarwa AFREED tare dacewa "Kaga AFREED fita haraka ta waye karamin kaninin naka kasan da ko shekara baka ban ba duka wata biyar ne zuwa shida ka ban shine zaka ce min wai wani ƙanin ka wai ma harda ceman ƙarami, gadai ƙananun ƙannin ka," Ya faɗa ya nuna su Fariya.
Wani murmushin AFREED yayi tare da cewa "Koma dai miye ni ke babba koda kuwa second 1 na baka aidai na girmemaka."
Ali zai koma magana Momy tayi saurin cewa "Kai AFREED kanason ɓatawa ɗana raiko tashi huce muje na zuba maka abinci kayi déjeuner (breakfast) ni ka daina tsokanar min abbana."
Ba musu ya mike yanayi wa Ali gwalo tare dacewa "Ai Momy wannan abban nakine bayajin magana."
Shikuwa Ali ya cika bam ya juwo yayiwa AFREED kallon zan rama.
Tare da Momy ya ƙarasa gun cin abincin sannan ya ja kujera ya zauna ita kuwa Mom ta fara servir ɗin sa shayi ta fara haɗa masa ta miko masa cikin ladabi ya ƙarɓa ya fara sha yana lumshe shanyayun idanunsa mai nuna yana jin daɗi shahin da yake sha, Momy ta turo mai da assiette da ta gama zuba masa soyayar doya da kwai da taji wata hadaddiyar soup wani haɗaɗen kamshi ne ke tashi sai ɗayan assiette (plet) da ɗauke da ferfesun kayan cikin, bin plet ɗin yayi da kallo, sannan ya ɗaugo da kansa ya dubi mahaifiyar ta sa da alamar tausayi a fuskar sa kuma a shagwaɓe yace "Haba Momy ya zanyi da girkin nan tsakanin da Allah mom wane irin ciki ne gareni da zan iya cin wannan abincin
Kallon sa tayi da kyau sannan ta ja kujera ta zauna sai tace naji baka iya cinye sa ɗin nima ai bance ka cinye duka ba, kaci daidai cikinka ka bar sauran.
Shiru dai yayi amma yasan da koda kuwa bai cinye duka ba sai yaci rabin kowane plet gashi Mom ɗin tayi zaune tana nufin a gaban ta zai ci abincin kenan baida incin cin kaɗan ya tashi yasan da gangan ta zuba masa wannan uban abincin karmar mutum 5 zaici amma a ganinsa fah.
Yana cikin wannan tunanin Momy ta katse sa da cewa "Mi kake jira baka fara cin abincin ba?"
Da sauri yace "Zanci Mom."
"To ina jira fara cin."
Bai wani ci sosai ba yace "Momy na ƙoshi." Ya faɗi maganar kamar wani ƙaramin yaro.
"Hum ai baka isa ba AFREED maza maida hankali kaci abincin sai in nace ka daina zaka daina daya ke bai mata musu a duk abinda tace kawai sai ya mayar da spoon ɗin ya naci sannu sannu irin an takuraka in nan, sosai ya ci abincin har saida taga yana shirin amai sannan tace to shikenan ya isa ta miko masa da jus ya girgiza mata kai yana nuna ruwa ajiye jus din tayi ta miƙa masa ruwan ya sha sannan suka mike suka koma falo a tare Momy cikin zuciyar ta tana cewa ai haka zan dinga maka tunda naga bakason cin abincin.
Suna shiga falon Momy ta zauna gun kujera da tashi shima ida Mom ɗin ta zauna yaje ya zauna tare da aza kansa saman cinyarta ya kwanta tare da lumshe idon sa ita kuwa Momy tana shafa kansa."
Cike da tsokana Ali yace "Jishi ko kunya baiji goɗai-goɗai da shi ya zo ya ɗane kan ciyar Momy ya kwanta abinda ko su Fariya baza suyi ba an daiji kunya."
Murmushi AFREED yayi ba tare da ya buɗe ido so ba yace "in fitsari banza ne kaza tayi mugani."
Ali yace "Allah ya sawaƙe aini nasan na girma ba kamar kai nake ba."
Shiru baice masa komai sabida yasan jan sa ne yakeson yi don shima yana zuwa ya kwanta a saman cinyar Mom ɗin.
Ƙannan su dai da Momy sai dariya suka suke masu.
AFREED ya ɗan buɗe idonsa yana kallon Momy cikin sanyayar muryarsa yace "Momy idan Allah yaso ya yarda kuma muna cikin masu rai ranar Alhamis zamuje Maraɗi nida Ali gun Tanti Marie kuma idan muje zamu samu wata guda can insha Allahu."
Kamin Momy tayi maga Farissa tayi tsale ta dawo kusa da Momy tace "Lah Momy muma zamubi su yaya dan Allah."
Momy bata kula taba tace cewa AFREED "Allah ya kaimu ai kam naji daɗi da zaku tafi saboda kullum idan nakira ta na gaisheta sai tamin ƙorafin baka zuwa gunta kaga kama gara kaje kasauke wannan nauyin dake saman kanka."
Shikuwa Ali cewa yayi "babu ida zanje an taɓa tsara tafiya da mutum ba'a sanar dashi ba? To ba zani ba."
Wani mugun kallo AFREED ya watsa masa sannan yace "Yo kada kaje ɗin ai tafi nono fari koma an faɗa maka dole se dakai zan iya tafiya?"
Dariya Ali yayi yace Eh an daiji ba za abika ba." Shiru ya mashi baice komai ba sabida idan ya tanka masa yanzu zai cikasa da surutu.
Farissa ta shagwaɓe fuska ta koma cewa "Mom ce maki fah nayi muna zuwa dan Allah za muje maraɗi muma tunda mun dade ba muje." Shiru mom bata cemata komai ba.
Shirun da Momy tayi ne yasa Fariya itama dawowa kusa ga mom ɗin tace "Dan Allah Mom ki bari aje damu."
Waini da kuke ta tambaya ta aje daku nice zanyi tafiyar ne? Yayan kune za suyi tafiya ku tambaye su man idan zasuje daku ai shikenan."
Da sauri suka nufi wajan Ali sukace "Dan Allah yaya zakuje damu kagafa mun daɗe muma ba muje ba muna son ganin Tanti da su Khadijah," sukayi kalar tausayi.
Sunƙin nufar AFREED ne sabida sun san idan yace ba zai je dasu ba to hakane dan baya magana biyu.
Murmushi yayi tare dacewa to makaranta fah idan munje daku sai ku bar zuwa makarantar."
Da sauri har suna haɗa baki suka ce "Yaya ai hutu zamu shiga ranar mercredi."
To shikenan zamuje daku insha Allah wani ihu daɗi suka saki tare da tashi dasauri suka ɗane kujerar da Ali yake zaune suka rungume sa su duka suna murnar.
Dariya shima yayi tare da cewa "To kuma sai kuje ku bar Mom ita ɗaya?"
A tare sukace "Yaya yau fah dady zaizo."
Kamin Ali yace wani abu Momy tace "Indai nice suyita tafiya........
Suna nan suna fira su jehi jehi AFREED kesa baki sa har ya kai ya daina magana saboda har ya kaji da duk baiyi wata magana mai tsayi ba.
Kiran sallah azahar ta sasu miƙewa suka nufi ɓangaren su dan ɗauro alwala su wuce masallaci, su Momy kuwa da ƴan biyun ta sukayi sama da suma su gabatar da sallar
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Écrit
Par
*QUEEN ZEEFAT*
_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_
*Wattap@nazichou*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_
Page : 23 & 24
Yau yakama weekend babu school, al'ada gidansu AFREEN ne duk week-end yaran gidan ke aikace akacan gidan sukuwa masu aikin gidan weekend ranar hutun suce, haka kuma suke da al'adar karatun Alkur'ani mai girma duk asuba ta Allah, haka kowa ke yin karatun nan daga papa har hamida dake autar gidan amma kowa acikin ɗakin sa yake nasa ƙananun yaran kuwa ɗakin papa tare dashi suke yi har sai rana ta fito kamin kowa ya tashi yayi aikin dake gabansa suna kammalawa sai su karya su tafi islamiyya, idan kuwa ranar school ne to ƙarfe 6:30 suke rufe Alkur'ani kowa ya shirya tare da karyawa su wuce school.
To yau ma haka ta kasance AFREEN ce ke naɗe darduma da ta ƙarasa karatunta a sama ta mayar gun dayake tare da cire hijab ɗin jikinta shima ta mayar ida yake, barin ɗakin tayi baki ɗaya ta nufi kitchen dan haɗa masu petit déjeuner (breakfast).
Bata wani ɗauki lokaci ba ta kammala girkin ta tattara kayan da ta ɓata ta wanke su baki ɗaya sannan ta dauko flask din shahi ta juye ruwan zafi da tayi, ta harhaɗa komai dai zai bada haɗaɗen shahi sannan ta aza akan babban plet tare da ɗaukar kula guda ta fito dasu domin taje ta shirya dinning ɗin.
Tana fitowa ta hangi Zeinab na gyaran falon tana ƴan goge goge dadai sauransu, cikin murmushin ta ta ƙaraso kusa da Zeinab ɗin tace "Sister kema harki fito?"