← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 69

Sashe 59

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata ranar asabar da dadare ya kama sati uku kenan da ɗaura auren Khairat bayan ƴan gidan su gama cin abincin a dinning baki ɗaya suka koma falo, suna ta fira hada mai gidan wato mahaifin su AFREEN a nata wasa da dariya, sai papa ya miƙe ya masu saida safe ya nufi saman shi da yake maman su AFREEN ke aiki bayan kamar minti goma sai ita ta mike ta bi bayan shi, sannan AFREEN itama ta nufi nata ɗakin., Haka da ƙaɗan kaɗan kowa ya watse ya nufi ɗakin shi a ka bar falon tsit tunda kowa ya kama gaban sa.

Maman na shiga falon papa ta sameshi a saman kujera a zaune yana nazarin wani abin ya yi tagumi, da sallamar ta shiga ya ɗago ya dube ta sannan ya amsa sallamar tare da sauke ajiyar zuciya, kusan shi ta zauna tare da riƙo hannun sa ta saka cikin nata hannun tace "Mijina na lura da akwai abinda ke damun ka kasa faɗa min dan na lura da maganar da kake son faɗa nice kake son gayama amma kaki samun courage ɗin sanar dani, kasani babu abinda muke boyewa juna koma miye kada kaji shaƙar sanar dani komiye saboda a ƙarƙashin ka nake kuma kana da iko dani gara ka faɗa dan tun yuri musan abunyi idan kuwa umarni zaka bani duk wannan ka cenci haka, saboda tun bayan auren Khairat na lura da akwai magana a bakin ka Alhaji na ka daure ka sanar dani ko nima hankali na zai kwanta."

Saida papa ya sauke wata ƴar gajeriyar ajiyar zuciya sannan yace "Allah kuwa kamar kin shiga zuciya ta ɗan ina shaƙar sanar dake abinda ke raina gaskiya, amma ba komai yanzu tunda kince haka bari na faɗa maki," sai da ya gayar zaman sa sannan yace "Ba wani abu bane nakeson sanar dake ila ina son faɗa maki cewa nayi wa AFREEN miji wato ɗan gidan injiniya Sumana in ba zaki manta yaron sun taɓa zuwa gidan shida ɗan uwan sa wanda lokacin haihuwar sa kema kin halarci sunansa in bazaki manta to shine nakeson sanar dake narasa ta kowace hanya zanbi dan Kada kice na yanke hukuncin aurar da ɗiyar mu, ban sharwace ki ba dan maganar da nake maki har mun saka rana auren sani da yaya na Adamu da Dr Inusa se kuma shi mahaifin yaron Alhaji Sumana mun tsayar da wata biyu, ida yau yayi saura wata ɗaya da sati ɗaya, dan kuwa tun zuwan su bikin Khairat mu ka saka wannan ranar idan ki ka yi lissafi zaki ga hakane."

Maman seda ta ɗauki kusan minti biyar bata ce komai ta tsurawa papa ido tana nazartar sa sannan ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah ya sa haka shi ne ma fi alkairi, tsoro na ɗaya shi ne in ba mijina ne ya fara nemawa ƴarsa auren ɗan su ba dan gudu ka su dinga mata kallon matar cushe, kuma kada ace ganin ana ta saka ranar aure ta ana fasawa ya saka shin yin haka ko a ganin shi ba zata samu wani wanda zai aure ta ba amma in dai babu ko ɗaya a cikin to ni ina farin ciki da hakan, kuma Kanada incin zaɓawa AFREEN miji sabida ɗiyar ka ce kai keda hakki da ita ba wani ba."

Murmushi Alhaji Sadisu ya yi ya ƙara riko hannun ta dake cikin nashi kamin yace " Allah maki albarka Allah ya biyaki da gidan aljanna sosai har yau har gobe bani da kamar ki a cikin mata na Allah ya biya ki da mafificin alkairi, sannan batun na cusa masu ita ko tunani zata rasa mijin aure ko ɗaya babu hasali ma shi ya fara kawo man magana kan yana son a yi haɗin zumunci, dalilin ganin AFREEN da yayi lokacin da tazo kawo mana ruwa ga ranar da suka zo ya nuna min yana son yaron da ita. Da wasu hujoji da ya sanar min ya saka na amince."

Itama murmushin ta mayar masa sannan tace "To shikenan Alhaji na Allah ya sa alkairi ku ka haɗa sedai ku sanar masu dan Kada ku shiga hakkin yaran ku dan ita dai nasan ba zata ƙi yi ma biyayya ba."

Papa ya amsa da ameen tare da cewa insha Allahu zuwa gobe zan sanar mata dama abinda yasa ki kaga banyi saurin faɗa mata ba na bari ne har muyi shawara dake ne, sannan na ɗan sama ta ido naga ko akwai wanda take so ko zata iya faɗa ko dai a ga wasu alamu haka to banga ko ɗaya ba inda bata boye bane."

Maman tace "To Allah tabbata da alkairi bari naje ɗaki na na dawo."

Tanti dake laɓe bakin ƙofar falon Alhaji alamu ta gama jin komai da suka tattauna tayi gudu ta ɓoye cikin wata ƴar coulouwar (corridor) dake bayan wajen dan itama tunda ta lura da akwai magana a bakin mijin nasu take ta son taji ko miye kuma ya ki faɗa masu idan suna su duka zaune waje guda tun a lokacin ta san cewa da Arahamat yake son faɗa wa ita ɗaya dan ta lura hada soyayyar da yake matane ta shafi waccan bakar yarinyar AFREEN mai kama da ita.

Maman na shiga ɗakin ta tanti ta fito daga laɓan da take da sauri ta sauka daga saman benan tayi shige ɗakin ta da sauri hankali ta a mugun tashe ta buɗe baki ita ɗaya cikin ɗaki ta fara magana kamar haka "Wane yaron za'a haɗa da AFREEN garde corps (Bodyguard) ɗin ministre (ministan) ko ministre ɗin gaba ɗaya shi ne zai aure ta, kai gaskiya baza ta saɓu ba wallahi da sake ace duk abinda nake ya tashi a banza kam, to ai ko garde corps ɗin ne bazan bari ayi auren nan ba bare a ce minister ne da kan shi da wallahi sai in da ƙarfi na ya ƙare bari na kira anty hawa na gaya mata."

Nan take ta dauki wayar ta nemo number ƴar uwar ta ta tura kira ta kara a kunne ringing ɗaya biyu aka ɗaga, hankali a matukar tashe ko gaisawa bata bari sunyi ba tayar ta na ɗaga tace "Aunty kinji kuma abinda suka ƙara jayo wa ko, wai aure za su ma wannan shegiyar yarinyar da duk burin mutan gidan ya na kanta, duk faɗi tashin da nake dan na hana ta aure har karshen rayuwar ta bai hana suka ƙara hango wanda zasu haɗata da shi kuma abin haushin ma kin san kowa?"

Yayar Wada suke kira da anty hawa da tayi shiru tana sauraran ta tace "A'a sai kin faɗa ai zan sani ko?"

Tanti tace "Wai ɗan gidan aminin Alhaji wannan injiniyan da nake baki labari cewa yaron sa ne keyin ministre de dépenses et de sécurité har nace da hamida ta isa aure da zanbi duk hanyar da zanbi in ga ya aure ta, amma ku inaso ko da ta biyu yayi da ita bayan nan da wasu yan shekaru, amma ina yanzu naji suna wannan banzan zancen bara digi naji yace uban yaron ne yake son a haɗa auren ba shi ba, amma bansan wane yaron daga ciki yake nufi ba tunda akwai yaron da ƙanwar matar sa ta muta ta bari tun yana jinjiri suka amshe shi suna kula da har ya girma a hannun su kusan yan sa'a guda ne shi ministan, shi ne ma garde corps (Bodyguard) ɗin ministre ɗin to shine nake tunanin wa ne daga ciki wanda za'a haɗa ta da shi, don gaskiya babu wada zan yarda daga cikin su yarinyar nan ta aure indai ina raye ko babu na zai kare sai na cika buri na na ganin yarinyar nan ta wulakanta, in bata auri nakasashe mugun matsayin ta tagayara ta zama abin tausayi wanda sai an taimaka mata ba, gaskiya hankali na ba zai ta taɓa kwanciya ba, ba dai sunce ita ta gaban goshi ba yaran mu duk kamar photo suke a gidan abinda AFREEN tace tana so shi ne ake yi a gidan nan ko da kuwa cikin mu ne iyayen muka ce bama so, anty ya kike ganin za'ayi?"

Sauke wata irin ajiyar zuciya Aunty hawa tayi sannan tace "Lale zama bai sameki ba ke a ganin zasu haɗa ta aure da wannan yaron da matsayin sa bodyguard ai sedai ministan shida zata huta girki ma sai anyi mata komai yi mata za'ayi ko da ruwa takeso a bata za'a ta, wa ya gayama ki za su kai ta inda za ta sha wahala, dan haka idan kina bada himma wajen ganin kin maida komai akan ɗiyar ki to idan kuwa ba haka ba kina nan kina kallon ruwa kwalo ya maki ƙafa, dan wallahi ki na kallo yarinyar nan zata nasara kanki ke kuwa ki faɗi warwas dan haka gobe tun safe ki zo mu koma gun mutumin nan wallahi tun kan yurin ya ƙare maki, kawai ƙaramar yarinya ta zame maku annoba ga gida, ita ce duk gidan nan a ka fi so ita ta fi kowa ilimin addini da boko ita ga shegin kyau kamar aljana ke wallahi idan bakiyi da gaske ba wannan kyau fuska da kyau ƙira da na hali da na komai duk ita ɗaya, wallahi wata rana ba minister ba shugaban kasar gaba ɗaya za'a ace ta aura ko sarki ke zaki kiji ma ance an zo neman auren ta daga wata ƙasar waje idan bakiyi da gaske ba, ke kuwa dake da ƴar tillon ɗiyar ki kun shiga uku, kinga likita babu kalar da bamu gani ba an ce babu ke babu ƙara haihuwa, haihuwar Hamida ma da yaya kika sameta saidai muka kashi kuɗi sosai kamin ki samu cikin, mu so ki haifo mana namiji ki ka samo mace a haka ma mungode, sannan kuka zama kamar wasu tsitacin mage a gidan."
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit

Par

*QUEEN ZEEFAT*

_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_

*Wattpad@nazichou*

*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*

*Page* : 57 & 58
Chapter 59 · 0% Book details