← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 69

Sashe 47

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khairat najin haka tasan bata son faɗa mata ne kawai sai tayi murmushi tace "To shikenan ƴar ƙanwata kada ki damu tashi kike kiyi wanka sai ki fito kirakani gidan su Maryam na kai mata katin gayata aure da goro kinji."

AFREEN tace "Kai anty yamma tayi fah mu bari har gobe mana in Allah ya yarda."

Sai Khairat tace "A'a gobe inda zamuje da yawa suke, ki shirya kawai mutafi yanzu, kamin magariba mun dawo."

"To shikenan anty bari na shirya." Ba tareda da jiran jin abinda Khairat zata ce ta faɗa toillet.

Tana shiga ta tsaya tunanin mafarkin ta cikin tunanin ne ta hango fuskarsa yana mata murmushi, da sauri tace "Nagane shi wallahi shine na taɓa haɗuwa da shi masallaci cin sahaba kuma da gun saukar Alƙur'ani da nayi, to miya ke nufi da shine mijina, wai miye ke shirin faruwa dani ne miyasa yake bibiya ta?"

*BONNE FÊTE*

*HAPPY SALLAH*

*BARKA KU DA SALLAH*

*MASOYANA*

*MASHA ALLAH.......*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit

Par

*QUEEN ZEEFAT*

_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_

*Wattpad@nazichou*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_

*Page*: 43 & 44

Tana shiga ta tsaya tunanin mafarkin ta cikin tunanin ne ta hango fuskarsa yana mata murmushi, da sauri tace "Nagane shi wallahi shine na taɓa haɗuwa da shi masallaci cin sahaba kuma da gun saukar Alƙur'ani da nayi, to miya ke nufi da shine mijina, wai miye ke shirin faruwa dani ne miyasa yake bibiya ta?"

Ta ɗauki lokaci tana zancen zuci kamin daga bisani tayi watsi da zancen ta fara wanka, ba tare da ɓata lokaci ba ta ƙarasa ta fito, a gaggauce ta shirya cikin wata haɗaɗiya doguwar rigar atanfa sannan ta murza mai ba tare da ta saka ko lips ba ta zaro hijab ɗin ta da niƙaf ta fito falon gidan a nan ta saka hijab ɗin sannan ta ɗaura niƙaf ta fice daga falon sabida ba kowa a falon kuma anty Khairat na waje bakin mota tana jiranta.

Tana ƙarasowa inda Khairat ke tsaye ta sauke wani ɗan gajeren lumfashi sannan tace "Anty na tsayar dake ko? To dan Allah kiyi hakuri, kisan halin shirina."

"Karki damu ƴar ƙanwata karɓi key ɗin motar ke zakiyi conduire (driving) ɗin mu dan ni gajiya gareni."

Ba musu AFREEN ta ƙarɓi clé (Key) ɗin ta kewaya ta shiga mazaunin direba ita kuwa Khairat ta shiga ta zauna wajen mai zaman banza, sannan AFREEN ta tayar da motar suka bar gidan.

Daga gidan su Maryam abikiyar Khairat suka wuce gidan anty Fauziya, suka sha hira, sai bayan sallah isha'i suka dawo gidan.

***************************

Ɓangaren AFREED kuwa har yanzu abu yaƙi yin baya sai cigaba yake, kwance yake idonsa a lumshe kamar mai bacci amma ba bacci yake ba da hannunsa na dama dafe daidai saitin zuciyarsa yana jin yanda take masa raɗaɗin ciwon son AFREEN, sosai yake mamakin kansa cewa wai shine yau yake son wata daba tama san yana son taba, shida bai taɓa soyayya ba amma gashi ya faɗa tarkon wata Wada ko a kashe shi yanzu bai san ina zai gan taba sosai yayi nadamar zuwan sa maraɗi dan gani yake ida baje ba da bama zai haɗu da itaba bare har yayi ta rashin lafiya sabida ita.

Yana cikin wannan tunanin ne ciwon nashi ya tashi, ya fara kakari amai ke nan Ali ya faɗa ɗakin da sauri ya ƙarasa gunshi ya kamusa a lokacin har ya faɗo daga saman gado, daidai lokacin da Ali ya riƙosa kawai sai ya fara aman jini saman jikin Ali, ai kuwa hakalin Ali yayi mummunan tashi da ganin ɗan uwansa cikin wannan halin bai taɓa tunanin abin nasa ya kai haka ba, tsananin ruɗewa da Ali yayi sai jijiga shi yake ya ma rasa ta ina zai fara basa taimakon gaggawa, cike da tashin hankali yake cewa "S'il te plaît AFREED relax (please afreed relax)."

Da ya ga haka sai ya ƙara fita hayacin sa yasa kawai sai ya fita daga ɗakin a guje ya kira direba gidan ganin Ali cikin tashin hankali yasa shima Ilya direba tada hankalin sa yana cewa "Mai gida lafiya kuwa."

Ina Ali baida ko bakin maga sai nuna masa ɓangaren su wake ai Ilya na ganin Ali ya kwasa aguje shima ya bi bayan sa a guje suka faɗa ɗakin AFREED a lokacin ciwo har ya ci ƙarfin sa dan har ya suma, Ali na taɓasa ya ga alamun babu numfashi a jikin sa ai baisan lokacin da ya kwala wata uwar ƙara bayana kuka sosai kamar mace da AFREED riƙe a jikinsa yana "Faɗin dan Allah ɗan uwa ka tashi kada ka mutu ka barni inna lilahi."

Yana cikin wannan tashin hankali yaji Ilya direba nace masa "Mai gida kama shi mu kai shi asibiti tana yiwuwa suma yayi."

Sai a wannan lokacin ne Ali ya tuno cewa shima da yaje kiran Ilya direba dan ya kama ma AFREED ɗin ne suje asibiti ai da sauri ya ciciɓi AFREED shida Ilya direba suka fito da shi da sauri suka saka sa a mota Ilya direba na ƙoƙarin shiga motar Ali ya dakatar dashi ta hanyar cewa "Kaje ka sanar da Momy cewa mun tafi asibiti."

Batare da ya tsaya jiran jin abinda Ilya direba zai faɗa ba ya fizgi mota a tsiyace ya ɗo hanyar asibiti cikin ƙenƙanan lokaci ya ƙarasa ba ma gun da ake yin parking ba yayi parking ya fito a guje ba tare da ya ma tsaya rufe murfin motar ba, ba'ayi minti biyu ba sai gashi ya dawo tare da nurses maza da gadon aza marasa lafiya a guje suke tafe da sauri suka za'a AFREED saman gadon suka tura sai cikin asibitin emergency room akayi dashi cikin gaggawa likitoci suka rufa kanshi, Ali nada bakin ƙofar ɗakin ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai kawo yake, hawaye sai zubowa suke saman kumcin shi yana ta addu'a a cikin zuciyarsa.

Ba ayi minti 5 da shiga da AFREED Momy da ƴan biyu suka shigo cikin asibitin a guje suna ta waige waige sai can suka tsinkawo Ali na kai da kawo bakin ƙofar wani ɗaki da gudu suka ƙarasa hankali a tashe momy ke riƙe da Ali tana tambayar sa miyasa mi AFREED mike faruwa sukuwa ƴan biyu kuka kawai suke suna kallon sa suna jiran jin abinda zai cewa momy, amma ina shima ya kasa magana sai kukan yake ya shige jikin momy yana kuka suma ƴan biyu na ganin haka gaba ɗaya suka faɗa jikinta suna kuka tana tayasu an rasa mai bama wani haƙura ko magana sun kasa, sai Ali da ke cewa "Momy dan Allah ki faɗawa AFREED kada ya mutu ya barni banida wani ɗan uwa da ya wuce shi bani da abokin hira banida abokin dariya, shine abokin na na wasa na faɗa na rigima kuma shine ɗan uwana na komai ma Mom ko ke bakinsa tsakanin mu ba, to in ya mutu da wa zanyi daga ni har shi ba wasu abokai garemu ba , mu dai ne abokan juna mu yanzu ya zanyi?"

Momy ma sai hawaye take zubar wa tarasa mi zata cewa Ali duk sun kama sun riƙe ta suna kuka, ɗago su tayi gabaki ɗaya ta shiga share masu hawaye sannan ta fizgo magana da kair cikin dangana tace "Kuzo mu nemi guri mu zauna mu daina zubar da hawaye a banza muyi masa addu'a samun lafiya yanzu ita AFREED ke buƙata gun mu ba kuka ba."

Zaunawa sukayi saman kujeru dake gab da ɗakin da AFREED ke ciki kowa nata addu'a amma har yanzu hawaye basu daina zuba ba daga idanuwan Fariya da Farisa ba shi kuwa Ali idanu sun mashi ja kamar gauta, momy ta juyar da fuskar ta cen tana ta share hawaye saboda bata son su ga ita ma ba ta daina kukan ba dan kar ta ƙara ɗaga masu hankali amma duk inda hankalin ta yake a tashe yake saboda gudan jinin ta abu ma fi soyuwa a gare ta na kwance kan gadon asibiti ba lafiya, rashin lafiya da basu ma san halin da yake ciki ba, a cikin zuciyarta tace "Ya Allah ka tashi kafaɗun wannan yaro nawa Allah ka yaye masa damuwar da ke tattare da shi ka bashi damar cinye wannan jarabawar."

Tsam Ali yayi ya miƙe kamar an tsilike shi ya dawo bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da AFREED ya konkwasa yace "Kai wai mi kuke yiwa ɗan uwa na ne da ba zaku fito da shiba wallahi zan karya ƙofar nan idan baku fito man dashi ba, idan kuwa kuka yarda kuka kashe min ɗan uwa wallahi sai nayi kashe ku kuma."

Su Fariya na ganin yanda Ali ya zare yana gayi abubuwa irin na masu taɓin hankali suka sake ƙare fashewa da wani sabon kuka, suna ganin kamar idan likitocin sun fito zasu ce masu AFREED ya mutu ne.

Momy na ganin haka tayi saurin tashi ta kamo hannu Ali ta zaunar dashi sannan tace "Haba ɗana ɗan albarka miyasa zaka dinga irin haka zaka ƙara tayar mana hankali ne idan muna ganin ka cikin wannan halin idan kaida ke namiji baka sa juriya ba mu mata ya kakeson muyi, dan Allah kayi hakuri kayiwa ɗan uwan na ka addu'a Allah ya tashi kafaɗu sa, narasa wace irin soyayya ce ke tsakaninun haka, na tabbata ko kaine a cikin wannan halin AFREED zai iya shiga tashin hankali fiye da haka ma inada tabbacin cewa yan da shima yake ƙaunar ko su Fariya bai ƙauna hakanan, sosai wannan haɗin ƙan naku da soyayyar dake tsakanin ku ke matuƙar birgeni ni kuma take faranta min rai har yasa nale jin daɗi mara musultuwa dan nasan ko bayan raina Ali ba zaka taɓa kukan rashi uwa ko dangi ba, wannan haɗuwar kawunan naku kesa ni manta cewa akwai wata wada ta tsuguna ta haifeka bani ba, dan wallahi mantawa nake da cewa kai ɗin ɗan yar uwata ne, ni a kullum kallon ka nake a matsayin wanda na duka na haifa kamar AFREED da ƴan biyu, ina fatan Allah ya ƙara haɗa min kanku ɗiyan albarka na ta na faɗa tana share hawaye.
Chapter 47 · 0% Book details