← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 69

Sashe 20

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har AFREEN tabud'e baki zatayi magana, sai Khairat ta rigata dacewa "Kinajiko AFREEN zuwa nayi muyi wata shawara, tun jiya da dadare naso muyi maganar nan tunda inasa ran zakizo d'akina kina ki kwana sai najiki shiru har nayi bacci."

"Eh wallahi karatu nayi har kwana ya kwashe ni a ida nayi karatun sai dana farka sallar dadare naga ashe saman darduma na kwana."

"Ok to shawara nakeso kibani kinji k'anwata sabida wataran kin fini tunani da hagin nesa."

"To Anti ina jinki Allah bani ikon baki ta k'aurai."

"Ameen, AFREEN kinsan sati uku da suka wuce na tab'a ce maki nayi wani saurayi Abdul Majid ko?" Khairat ta tambayi AFREEN tare da kallon ta, kad'a kai AFREEN tayi alamar eh.

Sannan Khairat ta ci gaba da cewa "To kinsan ban bari yazo gidan nan ba bare har yazo ya gaida papa sedai muyi waya da shi kuma kulum matsamin yake akan yanaso yazo ya ga gidamu sannan ya gaida papa da Maman, amma naki amince wa sabida ni idan yazo gidan nan basan ya zancewa papa ba alhalin yasan da zaman Ahmed to idan nace yazo ya gaida su papa, papa cemin zaiyi ko na b'ata da Ahmed ne yasa na kawo masa wani gashi kuma kowa yasan cewa Ahmed yazo yanemi aure na a wajan papa idan na kawo wani kuma za'ayi tunanin mun b'ata ne, gashi kuma shi Abdul Majid ya matsamin so yake yazo ya gaida su papa sannan idan papa ya yarde masa nan da sati biyu iyayensa zasu kawo kud'in aure, to ke Soeur ya kike ganin wanan lamarin zai kasance?"

Saida AFREEN tayi gyaran muryan sannan tace "To Soeurette (yar uwata) yanzu wanan lamari gyaran shi yana wajan Allah kuma ya wajan ki kuma wanan matsalar kece kike da ikon magani ta ba kowa ba sabida ragamar lamarin nan tana hannu ki kuma ba wata matsala babba ce, mai saukin warwarewa ce amma idan kin so hankan ko ba gaskiya ba."

Khairat tace "Ban gane mikike nufi ba iman da wara wara ko zan gane dalilin da yasa kika fad'i haka."

"To sis abin dubawa anan shine shi dai Ahmed saurayin kine dan kukai kusan shekara uku kuna tare kowa yasan ku tare shi kuwa Abdul Majid duka ko wata bakuyi da had'uwa ba dubara ta rage taki ki fida wanda kikeso cikin su sannan kada ki manta da abinda papa zaice idan har kika k'ara kawo masa wani alhalin sun ajiye magana da iyayen Ahmed akan idan kika k'arasa makaranta zasu kawo kud'in auren da sa rana baki d'aya kinsan mi papa zaice? Girgiza kai Khairat tayi alamar a'a, "To cewa zaiyi baki isa kisa ka shi ma magana banza ba ko kuwa shi zaki kunyata ko ki maida shi k'aramin mutum sabida wanan lamari da kika d'auko har k'ananan mutanece, amma in tambayeki man shi baki son Ahmed kin ne har kike k'okarin kawo wa su papa wani?"

A'a inason shi mana amma kuma nafara son Abdul majid shima."

To ça veux dire que kina iya barin Ahmed ki koma ga abdul Majid tun da har kika fara tunanin kawo shi gun papa, to walahi anti idan baki cikin hankalin ki to tun wuri ki dawo hayacin ki anti Khairat sabida idan kika bar yaya Ahmed bazaki tab'a samun kamar shi ba sai wani ikon Allah bare idan cin amanar sa kika yi Allah zai kama ki walahi Anti yaya Ahmed mutun ne na gari ga addini da sanin yakamata dubi yanda yake girmama iyayenki kamar nasa walahi samin irin shi sai an tona bare yanzu da duniya ta lalace, banson kije kiyi abinda kuma daga baya zai ki koma dana sani dan haka kaki ma fara walahi," AFREEN ta fad'a tare da kallon 'yar uwartata.

Kai sister walahi duk kin sarar min da gwiwa walahi amma duk da nace haka ba yana nufin zan daina kula Ahmed ba ne sabida inason sa har yau amma idan na bawa Abdul Majid damar yazo yaga su papa ba wani abu bane idan cikin su biyu wanda yariga kawo kud'in sa gidan mu sai ayi dashi, amma tunda kince haka gaskiya zan rabu da Abdul Majid dama ba wani son sa nake ba zan fad'a masa gida an riga da an min miji shikenan sai murabu lafiya sabida gaskiya nasan idan na auri wani wanda ba Ahmed zan iyasa shi cikin wani hali amma Ahmed shi ne ya dace dani ni da kaina na sani kuma ina nema zab'in Allah, bari na barki ki tashi kiyi shirin école (school) lokaci na tafiya ni ma dai ranar lundi (monday) zan koma ga karatuna yi maza ki shirya ki fito muyi kari," Khairat ce tayi wanan maganar tare da mikewa ta fita daga d'akin.

Tana fita AFREEN ta tashi ta kintsa d'akin sannan ta shiga wanka a gagauce ta fito sabida ta lura da ta kusa yin retard (lati), tana fitowa ta shirya cikin wata had'ad'iya dokuwa riga bak'a batada kwaliyar komai amma ta had'u bare da tasaka ajikin ta sai ta k'ara fito da kyayon rigar masha Allah, sab'o zunbulelan hijab d'in tayi tasaka tare da rike nik'af a hannun ta ta saka takalmi mai dan tsini sannan ta fito tayi yanda ta saba saida ta nufi d'akin kowa ta gaida shi a d'akin tanti ne ta d'an jima sabida kulum idan ta shiga gaida ta to za bata wata zumuwa tasha sannan ta kad'a mata wani magani cikin madara ta bata, duk wanan abin da Tanti ke bawa AFREEN idan ta shiga d'akin ta AFREEN bata tab'a gayawa uwarta ko wani kuma bata tab'a tambaryar Tanti ko maganin miye take bata ba sai ita Tanti idan taji bata tambaye ta saitace "Wai AFREEN miyasa bazaki tambaye ko maganin miye nike baki ba, sedai da na baki sai ki karb'e ki shanye idan ma na cutarwane ke dai kin sha kenan nan ya cutar dake d'in babu ruwanki?"

Sai AFREEN tace "Kai tanti ai nasan bazaki cutar dani ba miyasa kuma zan tambayeki? kamar dai ban yarda dake ba."

Itama Tantin sai tace "A'a AFREEN yana dai kyau kisani sabida gudun zarki."

Zarki kuma Tanti? Kamar dai bansan ki ba haba dan Allah ni walahi nayarda da ke d'ari bisa d'ari nasan bazaki cutar dani ba ni ko maman ban gayama bare har naji zargin a zuciya ta."

"A'a aini dad'ewa na fad'a mata AFREEN sabida banson abinda zaije ya dawo ayi dibin cutar dake zanyi walahi nikuwa maganin bakine da na tsari nike baki sabida lura da nayi mutane na yawon samiki ido da nuna maki bakin ciki k'irik'iri ko bakin umma kad'ai ya isheki ga yanda take nuna maki k'iyayya k'irikiri ba'asan abinda mutun zai iyayi ba duniya ba gaskiya, Allah dai maki maganinta."

AFREEN tace walahi ni tanti umma ko ganin ta banyi sabida nasan duk abinda take wata rana zata daina walahi ko kad'an ban rik'eta ba koda na minti d'aya ne bare har ya zama nasaka ta a zuciya ta kulum ina fatan Allah sa tagane, ko da kuwa ace ta tsaneni nasan da wata rana zata so ni kuma nasan da k'inane kawai take bata nufana da wani shari sai dai fatan Allah sa tagane."

To ko yanzu da AFREEN ta shiga d'akin tantin haka ce ta faru suna ta irin wanan firar har lokacin da tanti ta jefoma AFREEN tambayar cewa "Wai AFREEN kulum kina min firarki ta makaranta ko kuma ta k'awayenki ko kuwa ta wani abu dai haka amma baki tab'a yimin firar saurayin ki ba ko miyasa ko baki son na sanshi ne na'aza mukai lokacin da ba zaki iya boyemin wani abuba ko dan nabaki shawara?"

"Lah tanti walahi har kinsa ma naji kunya dama tanti har zakiyi tunanin akwai abinda nake boye maki wanda nake zaunawa muyi fira dake muyi shawara ko da Maman ba mayi haka, tanti nifa karatu nake yanzu samari basa gabana walahi babu wanda nake kulawa karatuna kawai nakeyi."

"A'a AFREEN wajan karatu daban kuma yin saurayi daban to zaunawa zakiyi har sai kin gama karatu sannan ayi batun aure a'a to ko alama gaskiya ki daina saka wanan nik'af d'in sabida kowa da ya ganki sai yayi dubin matar aure ce gashi Allah yayi maki kyau amma kina boyeshi to gaskiya da sake ni surikina nakeson gani ah to."

Da gudu AFREEN ta baro d'akin tana dariya tare da cewa "Walahi tanti kinsa na daina shigo d'akin nan naki."

Wani irin murmushi tanti tayi tace "Hum zaki dawo ga hanya yarinya muje zuwa dai."

AFREEN nafita daga d'akin tayi hanyar barin falon gaba d'aya sabida tayi lati bama zata iya tsaya wa yin kari ba ta nufin motar ta ta shiga ta kuna tare da barin gidan ta nufin makaranta.

K'arfe shad'aya na rana AFREEN ta dawo daga makaranta, tana shiga falon gidan ba kowa a cikin direct d'akin ta nufa tare da rage kayan jikin ta shige toilet tayo wanka juma'a sannan ta fito k'ara shiryawa tayi cikin wata dogowar riga vert (green) mai ratsi jaune (yellow) ta saka hijab green da takalmi green sannan ta d'auki nik'af ta bar d'akin tare da shiga d'akin Khairat da sallama Khairat ta amsa mata sallamar sannan AFREEN tace "Anti kin shirya ne mu tafi masallaci kinga fah har 12:30 tayi sabida ke d'aya zan iya tsaya ma dan ko su zeinab idan basu shirya ba sedai su wuce tare da papa sai mu dawo tare gaskiya bana son k'arfe 1:00 tayi ban tafi masallaci ba."

Al'ada gidan su AFREEN ce duk ranar juma'a 'yan gidan gabad'aya kan babba kan yaro mace da namiji har mai gadi kowa da kowa dai a gidan harta iyayen su mata tafiya masallaci suke dan yin sallar juma'a, a baban masallaci cin juma'a na sahaba dake cikin garin Marad'i.a

AFREEN ke d'auka yaran a mota su tafi Khairat ma ta tafi a motar ta idan kuwa taga dama sai bi AFREEN su shiga tata motar tare da yara su tafi masallaci, shikuwa papa ya kwashi matan sa su tafi tare, Fahad kuwa ya d'auki motar sa su tafi shida Imran sabida makaranta ma tare suke zuwa.
Chapter 20 · 0% Book details