← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 69

Sashe 39

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da AFREEN ta faɗa ma papa sai da yayi faɗa kamin ya amince, sannan taje ta ɗauki takarda da biro ta rubuta masa abinda suke da buƙata, da yamma KAMAL yazo saida suka hira har ana shirye shiryen kiran sallah magariba sannan ya karɓi takardar ya tafi.

Washegari wajan ƙarfe sha biyu na rana KAMAL yazo ya kawo abubuwan da ta rubuta masa a takarda gudan dayawa zakace shago guda ne ya saye duka sabida mota guda aka ciko da kayan, plower buhu biyar, wasu su biscuits, chocolats 🍫 sweet, juice, pop corner sosai aka ciko motar da su sai kace za'a buɗa wani babban shago, sannan ga rago biyu suma yace na girkin gobe, sai wata rantsatsiyar shada da wani haɗaɗen lace da ya sayar o AFREEN da Zeinab. Sosai abin ya ba wa AFREEN tsoro ganin wa'inna uban kayan da ya jibgo tsaye tayi tana kallon sa ta ma kasa ce masa koda ina yuni ne saboda tayi mugun mamakin ganin kayan.

murmushi KAMAL ya saki sannan yace "Miye abin mamaki a ciki, ni akanki zan iyayin komai koda kuwa ace Aljihu na zai zama babu komai a cikin, sabida ke da ɗiyan da zaki haifa min masu kama dake ne nake neman kuɗin nan kin ga kam dan na ɗan na kashe maki su ba wani abu bane, ni da nakeson kiyi yanda kika ga dama da Aljihu na kamin ɗiyan mu su zo su tayaki wasa da shi sabida nakune ba nawa ba ni dan ku na nema."

Murmushi AFREEN tayi tareda rufe idon wai taji kunyar maganar ta haifa masa yara da a ɗan shagwaɓe tace "Wallahi kayan nan sunyi yawa sosai, idan papa ya gani sai yayi faɗa, dama da kyar ya amince ya bari ka yi sayar hakan ma saida yayi faɗa amma babu komai bari kashiga daga ciki ai papa ma yana nan sai kayi mashi bayani."

Zaro idonsa KAMAL yayi yace "Haba dai ni ne zan shiga da wannan kayan niki niki haka, ke dama bake zaki siyo ba aka maki faɗa ina gani ai nasan ni har mari sai nasha, kuma suna iya cewa sai an mayar dasu sunyi yawa, yanzu dai yanda za'ayi ki bari a ƙarasa shiga da kayan sai ki tura Zeinab ta faɗa masu, amma nidai kam tsoro nakeji."

Dariya AFREEN tayi mai ƙara mata kyau tace "Wato kaida ke namiji ma kana tsoro ina gani mace kuma yarinya, kaga kai zai iya ƙinyi ma faɗa amma ni kam sai anyi min."

KAMAL yace "To ai shiyasa nace ki saka Zeinab ta faɗa masu shi da su maman yanda kema ba za'a maki ba dan nikam bazan iya ido biyu da papa ba cikin wannan halin."

Suna ciki maganar papa ya fito tsagar gidan tareda ƙaraso idan suke daga ita harshi ba wanda ya ga fitowar sa saida suka ji yayi masu sallama, da sauri suka ɗago a tare suka ƙaleshi sannan suka maida kansu ƙasa KAMAL yayi sauri duƙawa har ƙasa ya gaida papa, ita kuwa AFREEN tayi tafiyarta ta barsu nan, cike da kulawa papa ya amsa gaisuwar sa, sannan yace "Tashi ɗan kirki tashi haba."

KAMAL yace "A'a papa ba sai na tashi hakan ma yayi."

Papa yace "A'a tashi kaji ɗan albarka idai baso kake ni ma nayi durƙu shin ba."

Da sauri KAMAL ya miƙe tareda sunne kasan."

Papa ya ƙara gyara tsayuwar sa sannan ya ɗan musƙuta yace "To ko kaifa KAMAL, ci gaba yayi da cewa gaskiya KAMAL kayan can da ka jibgo sunyi yawa bai kamata haka ba banason maida alkairi komai ƙanƙantar sa da nasa anraba kayan can gidan biyu ka mayar da sauran kuma haka idan an mayar wanda kayi sayayyar wajan sa ya ga amshi ba daidai tun ya samu cinaki sosai, amma bai komai sedai kada a ƙara irin haka ka jiko, Allah maka albarka.

Juyawa papa yayi ya koma ciki, KAMAL na ganin papa ya shige shima ya tashi ya nufi motarsa sa ya bar gidan.

******. ******. ******

AFREED kwance ya na ta juyi sabida bacci yaƙi ɗaukar sa babu abinda yake sai tunanin ta daga ya rumtse idonsa ita yake gani ta masa murmushi ta mai kyau da kwantar da zuciya, tashi yayi zaune tareda dage kansa a fili yace "Wai ni miyake damuna ne akan yarinyar nan? Tun ranar da na fara ganinta ta rikitamin da lissafi ta mamaye min tunani na baki ɗaya, kwata kwata bana tunanin kowa sai nata, duk motsina da hankali na da komai nawa sun koma mata, miyasa take son sakani cikin damuwa? ni da ba ma sanin ta nayi ba amma ta nason wargaza min tunani da lamurana baki ɗaya, yanzu hakan ma babu abinda nakeso kamar naganta a kusa dani, na samu kollon wannan kyakkyawar fuskarta ta da murmushinta mai birgewa da ɗan ƙaramin bakinta wanda idan tana magana kamar kada tayi shiru."

A take yaji wani abu ya cakar masa zuciya da ɗan ƙarfi ga kuma faɗuwa da gabansa yayi da sauri ya dafe gefan zuciyarsa yana mai karanta lahaula wala ƙuwata illabillah, sannu a hankali ya ke sauke ajiyar zuciya yace "Miyasa ki keson takura min ne, mikike so ne daga gareni? ki taimaka ki faɗa min ko zan samu sukuni, shin ina zan ganta ko hankalina zai kwanta, miyasa na kasa daina tunanin ta ko dan ina cikin garin su ne? amma ai mu kusan barin garin mu komawa Niamey zan manta da ita ne, mais il faut que (yaka mata) kamin mu tafi na samu na ganta hankan ne zaisa hankalina kwanciya."

Komawa yayi ya kwanta tare da lumshe ido da niyyar yin bacci, amma hakan ya gagara, dan ya na rufe idonsa hoton fuskar ta ya shiga yi masa waibuwa, tashi yayi gaba ɗaya ya fara safa da marwa cikin ɗakin yarasa ya zaiyi tunanin AFREEN ya adabi zuciyarsa, a sannu ya furta "Ina zan ganta ne? dama a masallaci na saba ganinta to gashi yau asabar gobe Lahadi mukuwa zamu ɗaga daga garin ranar talata, to kodai maida tafiyar tamu nake har sai ranar wata asabar ɗin mai zuwa in Allah ya yarda ko?" Shi kaɗai ke tambayar kansa sai kuma yace "Kai nayi kewar Momy da dady gaskiya bance zan iya ƙara wasu kwanaki a nan ba gaskiya, amma dai naso naganta ko dan na tambaya ta miyasa take damun tunanina ne ko namata wani abune bansani ba?"

Yana cikin wannan halin na rashin samun bacci a kowane dare tun haduwar sa da AFREEN ya daina samun isasshen bacci kullum bacci ɓarawo ne ke yin gaba da shi, ko da hakan ta kasance yanzu, kawai sai ya mayar da tunanin de côté (apart) ya nufi toillet ya ɗauro alwala sannan ya fito yazo ya fara jero nafilfili cikin addu'ar sa kuwa fatan Allah sa ya ganta ko a hanya ne kamin ya tafi.

Ɓangaren tanti A'isha tunda AFREED yaje mata da maganar Ali da Umar tayi farin ciki sosai har da ƴar rawa ta taka, haɗa cema AFREED sai ta bashi tukuici wannan albishir mai daɗi haka, sannan ta ɗaura da tambaya AFREED kan shi wa yake so, idan yanada ita ya gabatar da ita dan a saka biki lokaci guda, amma kawai sai yayi murmushi ya kama hanya ya fita daga falon, baki tanti ta saki tana kallon sa har sai da ya b'ace ma ganinta kamin ta ke maida hankali kan wayar ta data ɗauki ruru sakin murmushi tayi gani mai kiranta ahankali ta furta "Ɗan halak kaƙi anbato." tare da ɗaukar wayar ta ƙara a kune tace "Assalamu alaikum yaya ina yuni."

Daga cikin wayar wanda takira da yaya ya amsa sallamar tare da cewa "Lafiya A'ishah ya gida ya yara."

Tanti A'ishah tace " komai lafiya lau yaya da ma yanzu nan nake cewa zan kiraka kuma sai gashi ka kira."

Anhan "To ina jinki A'ishah nasan dai da magana a bakinki tunda yanayin da naji muryar ya tabbatar da kina cikin farin."

Murmushi tanti A'isha ta komayi sannan tace "Hakane Abban AFREED wallahi wani abun farin ciki ne ya samu, yaran nan suka zo mana da magana mai daɗi Ali ne yace yana son Khadijah da aure, shi kuwa Umar Fariya yakeso, amma abinda ya rage min hanzarin shine yarona AFREED shi kam na tambaye sa ida da wada yake so ya faɗa man sannan ya gabatar da ita dan a haɗe bikin nasu baki ɗaya amma mi sai baice dani komai, sai ma tashi da yayi yana murmushi ya barni anan zaune.

Sai da dadyn su AFREED ya nisa ya saki wani ƙayatacan murmushi kamar tantin na gaban shi yace Alhamdulilah "Amma naji ɗadin wannan zance A'ishah gaskiya kinci baban tukuici ba tun yau nakeson ganin yaran nan sunyi aure ba amma suka ƙiya gashi yanzu Allah ya karɓi addu'ar mu Allah na godema, shikuwa wannan sangartacan ɗan naki ki barni dashi nasan maganin sa, dama na basu délai kan su fitar da matan aure nan da shekara guda, nayi niyyar idan basu fitar ba zan fitar masu da kaina, amma tunda su sauran sun fitar ba damuwa shi kam zan barshi har lokacin da na ibar masu ya cika idan bai fitar ni zan nema masa."

Tanti A'ishah tace "A'a yaya ba haka za'ayi ba ai shi namiji ne bai kamata a masa auren dole ba a dai barshi ya zaɓan, kuma idan Allah ya yarda kamin lakacin da aka bashi yayi zai fitar da wace yakeso, gaskiya bama son auren dole."

Hum A'ishah kenan kedai kada ku bari lokaci ya kure maku, amma auren dole har nayi makushi na gama, su ɗiyan naki da suka ceci kansu kan hukunci na, su aure nasu nan da wata shida a lokacin yaran sun gama yi exam kuma a lokacin result ta su ta fito idan tayi kyau se a gama baki ɗaya ayi walimar bikin aurensu da na makarantar su."

Tanti tace "Insha Allahu ma zamu fitar da namu zaɓin muma, kuma Allah kaimu nasu lokacin suma nida nakeso kamin nasu Ali shima AFREED ya fitar da tashi musha biki baki ɗaya."
Chapter 39 · 0% Book details