← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 69

Sashe 14

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi tayi daga gun Ufadi ta koma cuisine (kitchen) tana hawaye cikin zuciyar tace najawa uwata zagi baiwar Allah dake can cikin k'abari bata masan abinda ake ba, niko wace irin d'iya mai jama uwarta zagi, kara fashewa tayi da wani kukan mai tsanani abin tausayi.

Mahaifinta na dawo Ufadi ta nufe shi da maganar ta kara hada abinda bata ji ba kuma ba tagani ba ta k'ulla makircin ta.

Rai b'ace mahaifin nata yace " Jeki ki kikara min ita" fita tayi tana murmushi ta shiga d'akinta tace ubanki na kiranki ko jiran abinda zata cewa batayi ba ta fice daga d'akin.

Tashi tayi hankalin kwonce ta nufi d'akin mahaifin nata sabida tasan tana gaya masa yanda abin yake zai yarda, da sallama ta shiga sannan ta sami guri ta zauna kusa da mahaifin nata tace "Abbu sannun da gida."

Kallon ta yayi sannan yace "Yawa Arahamat, Ufadi tazo man da wani zance da bangane inda ta dosa ba shine nace ta kirawo man ke naji gaskiyar maganar a bakin ki."

Saida ta sauke ajiyar zuciya sannan ta shiga labarta ma mahaifin nata abinda ya faru sannan tace "Wallahi abbu ni ban ma sansa ba a hanya na had'u dashi kuma na nemi ya taimaka min, gudun kar na dawo nace wa Ufadi an sabce kudin ta dokeni amma shine daga baya da ta sami labari tace zina nayi aka bani su kuma ma yace zai dawo ya k'arbi saura kud'in idan ba gaskiya na fad'a ba idan yazo a tambaye sa."

Lokacin da ta fad'i zina mahaifin nata ya runtse idon sa har saida ta yi shiru kan nan ya bud'e yace "Shikenan tashi kije idan yazo karb'a kud'in nasa ki ce yazo ina neman sa.

To tace sannan tashi ta bar d'akin a bakin k'ofa ta tarar da Ufadi rai b'ace sanadin jin duk abinda suka tatauna ita da mahaifin ta alhalin ba haka taso ba...

Gaisuwa mai tarin yawa ga duk wani mai kauna ta da kaunar litafin nan ina ma kowa fatan alkairi.........💖💖💖💖💖💖
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

ECRITE:

_PAR_

*QUEEN ZEEFAT*

Yar
Mutan
Niger

Wattpad@nazhabibou

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_

Page: 11 & 12

Sanadin gigitaciyar k'arar da Arahamat ta saki yasa 'yan cikin d'akin suka fitu da gudu har suna bangazar juna kowane na k'ok'arin k'arasa ida take a yashe babu alamun numfashi a tatare da ita, suna k'arasowa tashin hankalin da suke ciki ya k'ara nin kuwa, a tare suka durkusa gaban ta suna kiran sunan ta su girgiza ta, sabida tsanani tashin hankalin ko lura da namijin da ke rik'e da ita yana girgiza ta basuyi ba, wanda shine bak'on da yayi sanadiyar firgicin ta har ya kaita ga suma.

"S'il te plait ma soeur reveille toi dan Allah il ne faut pas partir me laissé(Please my sister wake up dan Allah you must not leave left me)" Bak'on ya fad'a yana mai k'ara girgiza ta.

Duk da maganar da yayi hankalin su bai kai garesa sunata Arahamat, tanti Fatima ce tayi hausar tafiya ta d'ebo ruwa, tana zuwa ta zuba mata ruwan, wata atishawa tayi da k'arfi tare da sauke ajiyar zuciya mai k'arfin gaske, sannu a hankali tafara bud'e idonta har ta sauke su kan tanti Fatima da kiran sunanta tana mai jero mata sannu.

Tare da cewa "Lafiya Arahamat miya firgita dake haka har kika suma mu mun fito ba muga komi ba."

Da sauri ta mike zaune tana mai zubar da hawaye, tace "Tanti wallahi yaya Ibrahim nagani ya shigo ta k'ofar gidan nan dan Allah kada kuce man ba shine ba Kar kuce man mafarki ne nake."

Da sauri Tanti Fatima ta juya ta na kallon k'ofar shigowa gidan, shima da sauri ya matso kusa da Arahamat dake zubar da hawaye har yanzu yace "Nine k'anwata ba mafarki kike ba zahiri ne."

A tatare suka juyo daidai saitin da suka ji muryar shi ta fito suka tsura masa ido suna kallon shi baki sake, kowa ya kasa magana, da sauri Arahamat ta fad'a jikin sa tana kuka sosai tare da cewa "Ashe yaya zan kara ganin? kulum sai nayi kukan rashika a tare da mu ba kad'an mukayi kewarka ba, ashe dai yaya kana raye ka manta da mu? Mu kuwa babu ranar da ba zamuyi hirarka da Abbu ba, amma kai kana can kana jin dad'i ka manta da mu se mune muka damu dakai kasan cikin tashin hankalin da muka shiga kuwa sabida rashinka a tare da mu......." kasa k'arasa maganar tayi dalilin kuka da ya ci karfinta.

Sukuwa su Tanti Fatima kasa magana sukayi suna ta kallon shi cike da mamaki shine kuwa ko wanine me kama dashi, tare da tambayar kansu lokacin da ya shigo gidan da ta inda ya fito?

D'ago ta yayi daga jikin sa yana cewa "Dan Allah kuyi hakuri soeur (sister) wallahi ninan nafi ku damuwa sabida ku nan kuna ganin juna nikuwa ni kadai ne a can ba wanda nasani, kumin uziri mana tunda ba kusan abinda ya hanani zuwa gareku ba."

Sai a sannan Tanti Fatima ta sami damar magana tace "Oh Allah Ibrahim ashe kana raye? munan har mun sadak'ass muyin tunanin ka koma ga mahalicinka ashe Allah yayi zamu had'u gaskiya naji dad'in dawowar ka duk da ba kyauta ba shekaru aru aru aru ka tafin ka bar dangin ka da iyayen ka, to muna son muji abinda ya hanaka dawowa sai yanzu kuma daidai wanan lokaci."

Sai da ya sauke naunau yar ajiyar zuciya ya gyara zaman kamin yace "Tonku zauna sai na fad'a maku." suna zaunawa san ya fara da cewa "Tunda zan tafi dama banso tafiyar nake ba Abbu ya dage sai naje, dalilin shin nason nunamin mahinman cin karatun da zanje nayi zai min anfani tunda baiga anfanin zamana nan ba sabida ko na zauna babu abinda zanyi sai zaman banza yace naje nayi karatu shine mafi alkairi a gareni, ta haka na tatara na tafi ba dan raina yaso ba. To muna zuwa saida muka sha wuya kamin muke samin gurin zama karatu ya kankama watan biyu da zuwa guzirin danaje dashi ya k'are sai wani abokina da muke zama d'akin guda muke maneji da nashi guzirin shima muna da wata shida nashi ya k'are, amma dayake baban shi mai rufin asirine sai ya kirasa aka k'ara turo masa da kud'i, nikuma tunda na bar garin nan Abbu baida waya nima kuma banda ita kuma ban tafi da number kowa ba ko da kuwa cikin abokai nane tunda nima ba wayar ce dani, bansan ya zanyi na neme ku ba, haka muka tayin maneji da kud'in da ake aiko ma abokina har mukayi shekara guda aka bamu hutun wata biyu muka nuna muna son muzo ganin gida manyan da muke tare dasu acan, se a sannan suke fad'a mana cewa ai inda gomnati ta kawoka karatu kasashan waje to sai ka kamala shekarun da zakayi na karatu sannan zasu iya maido sa gida, inko har mutun nason zuwa ganin gida sedai iyayen sa su biya masa kud'in da zaizo ganin gida sannan su biya masa na komawa idan an koma makaranta. Daga jin haka kawai sai na sadak'ass nasan nida dawowa gida kuma sai wani lokaci in tak'aice maku ranar dai har hawayen bak'in ciki saida suka zubo man, sabida nasan ko ina da hanyar da zan nemi Abbu ba kud'in turo min ke garesa ba ko wanda zanci abinci ne bare har na jirgi, haka ina kallon abokina da muke d'aki d'aya ya shirya kayan sa dan zuwa gida har yake cemin ni ba zani gida ba nace masa a'a anan zan zauna haka ya shirya yayi tafiyar sa ya barni, wanda 'yan kud'in da ya barmin ko sati bayi da tafiya ba suka k'are, ya zamana kulum da yinwa nake kwana nake tashi har zuwa kwana biyar a lokacin na kamu da rishin lafiya da yasa aka d'aukeni aka kaini asibiti cikin mayan da muke tare dasu, a asibiti ne suke sheda masu cewa yinwa ce ta min yawa daga nan suka min aiki muka dawo gida wanda ya kaini asibitin ya sayo man abinci mai yawa ranar dai yini nayi ina cin abinci."

Sannan ya d'an nisa yace "Ke Arahamat ba sallah ce zakiyi ba Nagan ki kina alwala?" Kai ta girgiza masa alamar eh sannan ya koma cewa "To tashi kije kiyi sallah kowa maje yayi sallah idan kuka gama sai na k'arasa baku labarin."

Arahamat ta mike ta kakab'e jikin ta sannan ta kalle shi tace "Yaya amma dai ba wayo kamin ba ko? kada naje na shiga d'aki yin sallah ka koma tafiyar ka barmu."

Murmushi yayi yace "Ko can ba barin ku nayi ba nesa dai ne nayi daku kuma insha Allah nazo gida kenan ba zan sake komawa ba ina nan a tare daku duk rintsi duk wahala."

Murmushi tayi itama sannan ta juya ta d'oki buta ta koma sake alawa tana jin ta yau cikin wani irin farin cikin mara musultuwa a haka har ta gama alwala ta tashi ta nufi d'aki.

Yana gani ta shiga d'aki ya tashi shima ya nufi wani d'aki wanda yake malakinsa tun yana gidan ya bud'e ya shiga d'akin wanda kulum Arahamat sai tashiga ta share ta gyara masa shi sabida duk ranar da taji kewar yayanta ya mata yawa d'akin nasa ma take kwana da yaga ko ina tsatsab ya saki d'an murmushi, yasan ba wanda zai wanan aikin sai Arahamat, cikin farin ciki ya shiga ya rage kayan da ke jikin sa sannan ya fito ya d'ebi ruwa ga bokiti ya shiga wanka.

Arahamat na gama sallah ta fito ta nufi d'akin yayan nata cikin farin ciki da anashuwa ta tardo bashi nan sai kawa tashiga k'ara gyara d'akin sabida taji lokacin da yake d'iba ruwan tasan yana doushe (toilet).
Chapter 14 · 0% Book details