Sashe 52
Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Page* : 47 & 48
Doctor ya koma cewa "To na sallame ka tunda dai baka ce komai, amma kuma sai ka rage saka kanka a damuwa kaji my son komai yayi tsanani yana tare da sauki idan kayi hakuri komai zai zo ya wuce, idan kuwa ƙaga abin yafi karfin tunanin ka to ka nemin ɗan uwan ka kuyi shawara idan baku samu mafi ta ba ku nufi iyayen ku da maganar sai kuga komai ya zo da sauƙi, sabida ƴan magana sun ce duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutse ba zai hango ba, duk abinda ya shige maku duhu ku fara kai maganar ga manya sai kuga Allah da ikon sa ya sa an shawo kan matsalar."
"Insha Allahu dady hakan bazata sake faruwa ba." Inji AFREED
"In ta ƙara faruwa kuma fah ya kakeso na maka?"
"Ba ma zata faru ba dady." AFREED na faɗin haka duka ɗakin suka kwashe da dariya jin yanda yayi maganar kamar karamin yaro, banda Ali daya game fuska shi a dole fushi yake da AFREED.
Ba tare da ɓata lokaci ba suka yiwa doctor sallama tare da gangama kayansu suka saka a mota Ali ya nufi motar da yazo asibitin da ita inda AFREED ya riga da har shiga Ali kawai yake jira, Ali na shiga ya zauna mazaunin direba ba tare da ya ko kalli AFREED ba shima AFREED bai kulla sa ba sabida lura da yayi yana ta cin magani, Ali ya tayar da motar ya bar hararbar asibitin haka dady shima ya tayar da tasa motar wada momy da ƴan biyu ta ke ciki suka kama hanya, har suka ƙara so gida babu wanda yayi wa wani magana tsakanin AFREED da Ali kawai dai sunyi tafiyar kurame ne, Ali nayin parking ya fice daga motar ya nufi hanyar ɓangaren su da kallo AFREED ya bisa yana tunanin shin mi yake damu Ali yake wani share shi a zuciyarsa yace "Ko dai fushi yake dani ne to mi na masa ko dai wani ya taɓo sa shida bai fiya yin fushi ba ko miye aka masa nasan babba ne, idan kuwa ni yake ma fushi na san da an jimawa zai daina ba saboda bai iya fushi dani."
AFREED na cikin mota yana wannan tunanin baisan lokacin da su momy suka shigo gidan ba sai da yaji dady yana ce masa "Mi kake yi a cikin motar?"
Da sauri AFREED yayi firgigit ya juyo tare da cewa "Babu komai." Sannan ya buɗe motar ya fito shima ya nufi ɓangaren su, su momy suka tsaya suna kallon sa har ya shige sannan suma sukayi nasu ɓangaren, Ali dake tsaye ta window dakin sa yana kallon AFREED yana hamdala da godewa Allah da ya bawa ɗan uwansa lafiya ganin AFREED ya nufo ɓangaren nasu yasa shi komawa ya zauna bakin gadon sa ya na tunani.
AFREED na shiga ɓangaren na su shima ya nufi nasa ɗakin ya tare da rage kayan jikin sa ya nufi toillet ya saka ma kanshi ruwa ta tare da ya jima ba ya fito ya shirya cikin kayan bacci ya ɗane gado ya shiga yin bacci har sai da aka kira sallar azahar sannan ya farka ya nufi toillet ya sake yin wani wanka tare da ɗauro alwala ya fito ya shirya cikin fara doguwar rigar sallah ya fito daga ɗakin da niyyar tafiya masallaci a bakin ƙofar fita daga falon nasu ya haɗu da Ali na ƙoƙarin buɗe ƙofar ya fita shima ya ƙara so ko kallon inda yake Ali baiyi ba bare yasa ran zaiyi masa magana, Ali ya buɗe kofar ya fice, mamaki sosai ya kama AFREED wai shine ya ke share wa haka to mi ya masa?" Yana cikin wannan tunanin yaji an tayar da sallah da sauri ya rufe kofar ya nufi masallacin, kusa da Ali yayi sallah saboda yana son idan sun dawo tare ya tambaye sa ko lafiya yake ta share shi haka, ana gama sallah kamin AFREED yake gama addu'oi déjà Ali ya ƙarasa tasa ya tashi ya fice daga masallacin yayi tafiyar.
Da mamaki AFREED ya ƙarasa nasa addu'oi shima ya nufi cikin gidan ɓangaren momy ya shiga a nan ya tarda Ali yana ta wasa da dariya shida su Fariya, yana ganin sa ya gimtse fuska har abin yaso bawa AFREED dariya sedai bai dara ba kawai sai ya nemi guri ya zauna ya na jiran saukowar momy.
Momy na saukowa ta nufe su da dariya tana masu sannu da shigowa su kuwa suka gaida ta ta amsa tare da nufar dinning, ita da Farisa suka ɗauko abinci daga saman dinning suka yo dashi falo, saman kafet suka ajiye suka jera komai nan kowa ya sauko ƙasa suka zauna suna jiran dady, shima ba tare da ɓata lokaci ba ya sauko sannan momy tayi servir ɗin kowa daga nan sukayi Bismillah suka fara cin abincin bakajin ƙarar komai sai na cokali suna gamawa AFREED ya mike yace "Momy zanje na kwanta na ɗan huta."
Murmushin manya momy ta sakar masa sannan tace "To a huta lafiya ɗan momy."
Daga nan ya nufi mahaifin da ya sunbace shi sai mahaifin na sa ya sha masa kai yace Allah maka albarka da Amin ya amsa sannan ya fice."
Da AFREED ya fita momy da dady da Ali da su Fariya suka shiga fira har firar auren su akayi, AFREED tun yana jiran shigowar Ali har bacci ya kwashe shi Ali bai shigoba, kuma shima Ali ya na sane ya ƙi shigowa saboda yasan yana can yana jiran sa.
Ali shine bai fito daga ɓangaren momy ba har saida aka yi kiran sallah la'asar kan suka fito shida dady dan zuwa masallaci a hanya suka haɗu da AFREED shima zai tafi masallaci sai suka jera suka tafi tare bayan AFREED ya gaida dady haka ana gama sallah suka jero tare, su nufo gida suna kawowa daidai ida zasu nufi ɓangaren su suka yiwa dady sallama, suka nufi nasu ɓangaren babu wanda yayiwa wani magana har suka shiga falon su, AFREED yaka Ali baida niyyar tsayawa suyi magana dan ganin da yayi ya nufi hanyar ɗakin sa yasa shi dakatar dashi ta hanyar cewa "Ɗan uwa inason magana da kai." cak Ali ya ja ya tsaya ba tare da ya juyo ba kusan minti biyar babu wanda yace wani abu daga cikin su Ali na ganin haka ya ɗaga ƙafarsa har zai fara tafiya, AFREED kuwa har ya kawo inda yake a tsaye kamo kafaɗar sa ya yi yace "Kazo ka zauna muyi magana."
"Ba zan zauna ba ka faɗi duk abinda kakeso ka faɗa ni inada abun yi."
"Dan Allah ka zauna maganar ba zata yiwu daga tsaye ba."
"To shikenan tunda kace dan Allah sedai ka yi sauri ka faɗi ko miye ni akawi abinda ke gabana."
Murmushi kawai AFREED yayi ya karasa suka zauna ɗaya daga cikin manyan kujerun dake falon, sai da ya nisa yace "Lafiya Ali naga kana ta share ni mi nayi maka haka mai muni da har bakason ganina, ko kuwa rashin lafiyar da nake kake so na koma, in baka gama jinya ta bane sai naji."
Da sauri Ali ya ɗaga kai ya kalle sa bai ce masa komai, AFREED ya ɗaura da cewa "Sai wani guduna kake ko dan ban da lafiya ne ko kuwa wani abu doctor yace inada wanda idan ka ci gaba da yi min magana ko kulani kai ma zaka kamu da shine ban sani ba."
Da wani irin sauri Ali ya ɗago ya kalli AFREED kallo irin na har akwai abinda zai same ka na guje ka ne, kamar AFREED ya san abinda Ali ke tunani yace "Ah to dole na faɗi haka rabon da kamin magana ko kamin sannu da jiki tun muna asibiti da na farka tunda ka taimaka min na shiga bayi na fito baka ƙara koda yiman magana Ali ba dole na faɗi haka ba."
Wanda Ali yaga damuwa ƙarara a fuskar AFREED waga alamun ya marairaice da gudun kada damuwar da ya shiga yanzun ta ƙara je fasa cikin wani ciwon ya sa shi saurin buɗe baki ya fara magana kamar haka "Haba AFREED a tunanin ka akwai wani da zai sameka na kujeka ko da kuwa abin ya fi ƙarfin tunanin duniya baki ɗaya duk faɗin duniyar ban da mahaifi na da Momy da dady ganin ka ina da wani da ya fika a rayuwa ta ne kenan baka san son dana kema maka ba da har zaka kalle ni ka faɗa min wannan zancen da mai hankali ba zai ɗauka anya kuwa kama ɗauke ni wanda na ɗauka kuwa ni kallon wanda muka fito cikin ɗaya nake maka wanda banida kamar sa a rayuwar nan, amma ina ga kai wanjan ka ba haka ba ne."
"Ni ba dan komai nan ke fushi da kai ba sai dan ka zauna har wata damuwa ta dameka har ka saka kanka a mugun tunanin da ya ke neman rayuwar ka wai ka kasa faɗa min idan ni ne ba zan taɓa boye ma komai ba, duk da nasan halin na rashin son magana da miskilanci da kuma zurfin ciki bai kamata ace ni ka kasa gayamin damuwar ka ba ko kana ganin bazaka iya faɗa ma su momy ba sai ka faɗa min idan muka kasa shawo kan abun sai mu san hanyar da za mubi mu faɗawa su momy, su sai su sa ma mana ma fita idan ta wajen su ba'a samu mafita ba, sai su taya mu gayawa Ubangiji lamarin da, samun abin yi daga, haka har asamu ma fita kasan ance addu'ar iyaye bata faɗuwa ƙasa banza."