← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 69

Sashe 34

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya Hasina ta sauke tace "Wallahi har naji dadi besty, dan gayawa papa wannan mai sauƙi ne, kawai tanti zaki faɗa mawa sai ta faɗa masu baki ɗaya sabida nasan da itace kaɗai zaki iya faɗa ma."

AFREEN tace "Hakane duk na ruɗe narasa ya zanyi shiyasa ma na manta da na faɗa wa tantin."

Hasina tace "To ai yanzu na tuna maki."

Wata nauyaya ajiyar zuciya AFREEN ta sauke tace "To muje muci abinci, muna ƙarasa wa sai naje na faɗa wa tantin, sannan muje na faɗa wa maman da papa zanje gidan ku tunda yau bazamu makarantar yamma ba."

Fita sukayi a ɗakin sannan suka nufi dinning inda su Zeinab ke zaune suna jiran fitowar su ba tare da ɓata lokaci ba aka zubawa kowa abincin sannan suka fara ci, suna ƙarasa cin abincin AFREEN da Hasina suka nufi ɗakin tanti, suka tardo ta tana ninke kayan ta sallama sukayi tare da nufar gefen bed ɗin suka zauna AFREEN tace "Tanti sannu da gida kikawo na ƙarasa nike maki kayan."

Murmushi tanti tayi sannan tace "Yawa AFREEN, kibar shi ai nama ƙarasa AFREEN, tanti ta faɗa tare da dawo kusa da su ta zauna tana cewa "AFREEN faɗamin mike faruwa naga alamun da magana a bakinki."

Murmushi AFREEN tayi tareda sade kanta ƙasa sannan tace "Tanti dama.....dama." sa kumai tayi shiru ta kasa gayin abinda tayi niyar faɗa."

Gaban tanti ne ya wanke ya faɗi har saida alamun tsoro ya bayyana a fuskarta tana addu'ar Allah yasa ba abinda take tunani bane, kamin take basarwa tace "Gayamin mana ma fille tsakani na dake babu wannan kunyar."

Saida AFREEN ta ƙara duke kanta ƙasa sannan tace " Tanti dama..... Wanine yace zaizo ya gaida ku, dam dam gaban tanti ya faɗi da ƙarfi a lokacin AFREEN har ta riga da ta fice daga ɗakin dan kunya sai ta jin abin gashi banba rakwai wai itace saurayi zaizo gunta."

Hasina ta dawo da tanti daga duniyar tunanin da lula a lokacin da take cewa " Tanti shine takeson ki faɗa wa papa dan ita ta kasa yanzu ma da kyar na taso ta gaba da ta faɗa maki."

Murmushi yaƙe tanti tayi sannan tace "Aiko AFREEN akwai kunya nima wai dan muna yawan fira ne da ita har ta iya faɗamin insha Allah zan faɗa masu shi da maman ta Allah kawo sa lafiya wane lokaci zaizo?"

"Bayan sallar isha'i." Hasina ta faɗa a taƙaice.

To shikenan babu damuwa sosai nayi farin ciki da jin haka na kusa shan bikin ɗiyata Allah nuna min lokacin nan da alkairi."

Murmushi Hasina tayi sannan ta tashi ta fita tabi bayan ƙawarta. Tanti na zaune a inda suka barta kusun minti 10 tana zaune tana saƙa da warwara sannan ta tashi ta nufi ɗakin maman, tana shiga suka gaisa sannan ta faɗa abinda suka tattauna tsakanin ta da su AFREEN cikin da farin ciki take faɗa maman abinda AFREEN ta faɗa mata. Murmushi Maman tayi sannan tace "Hum AFREEN sarkin kunya to kije ki faɗa wa mahaifin nasu kamin ya fita dan yasan dazancen."

"A'a maman Fauziya mi zai hana ke ki faɗa masa." Tanti ta faɗa tana kai duban wajan maman.

Maman tace "A'a ki daije da kanki waka abakin mai ita tafi daɗi sabida ke a ka baiwa saƙon kuma kunfi kusa keda d'iyar taki."

Dariya tayi tace ƙwarai kuwa bari na tashi dama wannan saƙon farin ciki nidai ce ya kamata na faɗesa." Sannan ta miƙe ta bar ɗakin ta nufi ɗakin papa, ta tardo shi zaune cikin falon sa yana karatun jarida kujera da ke fuskantar sa ta zauna ta fara koro masa da bayani.
Cikin ƙanƙanan lokaci farin ciki ya bayyana a fuskar papa yace "Masha Allah AFREEN ta fara hankali da har iya kula wani har ta bashi damar zuwa gidan nan wannan wane mai sa'a ne haka? To Allah kayosa lafiya."

Da ameen tanti ta amsa sannan ta tashi ta koma ɗakin ta, ita kuwa AFREEN har sun tsufa gidan su Hasina maman Hasina taji daɗi ganinta har tarasa ma ina zata saka ta dan farin ciki, bayan sallar la'asar AFREEN tayi masu sallama ta tafi gida bayan Hasina ta nuna mata yanda zata karɓi KAMAL idan yazo sabida ita sabon shiga ce a wannan fannin."

Bayan sallar isha'i AFREEN tayi wanka ta shirya cikin wani haɗaɗen ɗumki na atanfa da aka mata doguwar riga sosai rigar ta kamata ta mata mugun kyau ba kwalliya tayi ba sai kwali da tasha wanda ya ƙara fito da hasken idonta wanda suka bada wani irin kala mai kyau maron ɗin cikin su sai wawalniya yake ko kai kewa ka kalleta dolene ka ƙara kallon ta. Amma gabanta sai faɗuwa yake tana tunanin ya KAMAL zaiyi idan yaga fuskarta kadai yaje shima ya tsorata da ita shikenan ya daina sonta bayan kwana biyu nan dayake kiranta suna gaisawa yasa ta fara sakin jiki dashi, kada yaje ya mata kallon aljana kamar yadda kowa kemata idan suka ga fuskar dan wasu ma har guduwa suke.

Tana zaune tana saƙa da warwara taji wayar ta ɗau ringin aikuwa sai gabanta ya yanke ya faɗi har saida ta riƙe daidai gun da taji ya buga din, addu'a tayi sannan ta ɗauki wayar takara a kunne tare da yin sallama, daga cikin wayar aka amsa sallamar tare da cewa "Sarauniya ta gani a ƙofar gida."

Da To ta amsa sannan ya katse kiran, tashi tayi ta fita ta tardo Zeinab da Safina zaune a falon suna kallo kusa da Zeinab taje ta zauna tace "Zeinab tashi kije nayi baƙo a waje ki shigo da shi."

"To anti." Zeinab ta faɗa sannan ta miƙe ta fice.

Maida duban ta tayi ga Safina tace "Sister tashi kije ki faɗa wa su papa gashi nan ya ƙaraso."

Itama miƙewa tayi ta nufi ɗakin papa sannan AFREEN ta koma ɗakinta ta zauna......

Zeinab na fita ta tardosa zaune cikin motar yana dana waya ƙarasa wa tayi gun motar tayi sallama sannan tace "Ina yuni yaya ance ka wucike daga ciki."

Kallon ta yayi sannan ya saki murmushi yace "Lafiya lau ƙanwata, to shikenan bari na fito."

"A'a yaya da ka shigo da motar a ciki mana"

A'a ƙanwata Bama sai na shigo da ita ba tunda ba jimawa zanyi ba."

"To ba damuwa yaya." Zeinab ta faɗa tare da juyawa zata koma ciki.

KAMAL yace "Ah ƙanwata ki bari mu shiga tare man, ya faɗa tare da ƙoƙarin fitowa daga motar, tsayawa tayi sannan ya fito daga motar, masha Allah KAMAL fari ne dogo mai ɗan kakabran jiki kyakkyawan gaske ajin farko. Ƙaraso yayi inda take cikin ƙayataciyar tafiyar sa sannan yace " Mutafi."

Jerawa sukayi suka shiga gidan suna kawowa ƙofar da zata sada su da falon ya ja ya tsaya Zeinab ta juyo ta kalle sa tace "Yaya Lafiya naga ka tsaya."

Murmushi yayi sannan yace "Lafiya lau mu shiga ."

Buɗe ƙofar Zeinab tayi tashi ga da sallama shima haka ya shiga kansa aka kasa yana kallon ƙasa da sallama ɗauke a bakin sa, papa ne zaune a falon ya ɗago ya kalleshi tare da amsa masa sallama sannan yace "Ƙaraso mana yaro."

Ƙarasawa yayi tare da zubewa kasa saman kafet tare da gaida papa kansa a ƙasa ya ƙasa ɗagowa ya kalli sirikin nasa, sannan papa yace "Tashi ka zauna mana ya ka zauna a ƙasane nan fah gidanku."

Murmushi KAMAL ya saki da har yau kansa a ƙasa sannan yace "A'a papa nan ma ya isa."

Murmushi papa yayi a cikin zuciyarsa ya na faɗin wannan daga ganinsa yaron kirki ne, amma a fili sai yace "To shikenan."

Ba tare da ɓata lokaci ba aka cika masa gabansa da ƙayan ciye ciye da lashe lashe sannan papa yace masa "To bismillah."

Girgiza kansa yayi alamun a'a, papa yace "To kodai bakasan yanzu nan yazama gidanku ba kaima ka cire kunya mana ni kamar mahaifi nake a wajan ka, saki jikin ka yaro."

Murmushi KAMAL yayi sannan ya ɗauki kofi ya tsiya juice ya sha sannan ya ajiye."

Sannan papa ya kallesa ya fara masa tambayoyi kamar haka............

Ina sonku irin sosai ɗin masoyan wannan littafi........

Bon Mardi 💖💖💖💖

Happy Tuesday💞💞💞
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit

Par

*QUEEN ZEEFAT*

_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_

*_Teemah_* ina jinjina maki game da ƙoƙarin comments sosai nake jin daɗin idan naka comment ɗin ki sannu ki da ƙoƙari Allah saka maki da alkairi.

*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_

*Page*: 31 & 32

A nutse papa ya dubi KAMAL yace "To yaro mi sunan ka sannan inane gidan ku kuma mike tafe dake a game da yarinyar nan AFREEN?" papa na kaiwa nan yayi shiru.

KAMAL ya gyara zaman sa da kyau sannan ya ƙara sada kansa kasa yace "Papa ni sunana KAMAL mahaifina Alhaji Aminu mai gyaran TV, gidan mu kuwa yanan cikin anguwar buzu ɗan zambaɗi wajen shagon Sagir mai ƙarfuna, ni kuwa ina aiki a baba ma'aikatar ƙera leda dake cikin garin Maraɗi ta wajan hanyar anguwar ƴan belbelu, sannan inada shagon biyu cikin grand marché ( babba kasuwa) kuma inada shago biyu a ƙaramar kasuwa wanda nikeda yara masu tsare min su, kuma duk ina sami lokacin ina zuwa Dubai wajen sayo kaya kamar lace, antafa shada da dai sauransu, kuma abinda ya kayo ni gun AFREEN shine aure🙈 papa wallahi ban zo da wassa ba da aure nazo, kuma nutsuwar ta kamalarta da addini ta ya ja hakalina gareta ba dan wai na taɓa ganin fuskarta ba ɗan ko yanzu dana ke maka maganar ban taɓa ganin kamanin ta ba a whatsapp sai nayi nayi ta turoman da photon ta amma taƙi, duk da haka banji haushin ta sedai ma da tayi hakan birgeni tayi, kuma ni ko ya take to naji nagani inason ta a haka.

Papa yace "To masha Allah KAMAL duk na gamsu da bayan nan ka, kuma na yaba da hankalin ka sannan duk garin nan babu wanda baisan mahaifin ka mutuman kirki bane dan haka nidai na baka AFREEN, sai kaje ka sameta dan ku daidai ta kanku."

Wani farin ciki ne😊 ya sauko wa KAMAL, baisan lokacin da ya furta "Nagode papa Allah saka alkairi."
Chapter 34 · 0% Book details