Sashe 46
Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Can suka tsintsi muryar maman nacewa "AFREED da Ali Macha Allah kun girma kamar dai ba ku bane mukaje bikin ku nida papan su Fauziya lokacin ina amarya bayan wata shida kuma na koma ni ɗaya wajen bikin Ali lokacin papan su baya gari Allah sarki Ali Allah ya jikan mahaifiyar ka Allah mata rahama kuma yasa aljana ce makomar ta ameen, ina mahaifiyar taku Hajiya Falmata da fatan tana lafiya?"
Da sauri AFREED da Ali suka ɗago suna kallon maman jin yanda ta kama sunan su kuma take ɗan bada ɗan ƙaramin labarin rayuwar su, dam da dam AFREED yaji gabansa yayi wani wawan faɗuwa lokacin da yayi tozali da fuskar maman wada yake kallon kamanin AFREEN shinfiɗe a fuskar ta ƙara waro idonsa yayi sannan ya lumshe su tare da maida kansa ƙasa.
Yana cike da mamaki suka amsa mata cewa "Tana lafiya."
Kuma kamar an tsayar dasu sai suka yi shiru shikuwa AFREED na tunanin zuci na cewa "Shin itace mahaifiyar ta ko kuwa kama ce dai suke, ko dai gizo ne yarinya nan keyi min da duk wanda na kalla a gidan nan yake min kama da ita? Ya Allah ka samamin mafita ka ƙara haɗani da yarinyar nan kamin na bar garin nan."
Can dai ya daina tunanin da yake ya dawo da hankalin sa wajen su suka ci gaba da fira su tanti sai washe baki ake anji cewa AFREED shine ministan tsaro a ran ta tana cewa inama ace Hamida ta isa aure da na baya ita ya aura ko ta halin ƙaƙa ne."
Sune basu bar gidan ba har sai ana shirye-shiryen sallah azahar suka masu sallama sun tashi zasu tafiya maman tace "Ku tsaya na baku saƙo ku kaiwa mahaifiyar ku." Ba tare da maman ta tsaya jin abinda za su ce ba tayi saman escalier (stairs) bata jima ba ta sauko ɗoke da wata leda ta basu tace "Ku kaima ta kuce nace ina gaisheta tunda yanzu ta yarda ni bata zumuncin dani."
Murmushi sukayi sannan Ali ya ƙarɓa suka bare falon, papa ya rakosu har bakin motarsu yana tajin daɗin zuwan su kuma sai yaji ma kamar kada su tafi, haka suka shiga mota suka tada suka bar gidan papa na ɗaga masu hannu tare da masu fatan Allah ya tsare har sai ya daina gani su sannan ya koma ciki.
Su AFREEN kuwa ana can anata waya da KAMAL.
*Agurguje*
Yau wata uku kenan da su AFREED suka bar Maraɗi kuma a cikin wannan watan uku abubuwa dayawa sun faru kamar fasa auren KAMAL da AFREEN dalilin mahaifiyar KAMAL da tashiga ta fita ta wargaza abin sabida so da take KAMAL ya auri wata ɗiyar ƙawarta wada ɗiyace a wajen gouverneur (governor) kin Zinder, dalilin haka ba karamin shiga tashin hankali AFREEN da KAMAL sukayi ba amma ya zasuyi haka suka haƙura, bayan KAMAL ma tayi wasu samarin har guda uku, amma duk suna rabuwa komin suka ɗaɗe da mutun to da an fara maganar aure sai abin ya lalace.
Wajen AFREED kuwa tunda suka koma gida ya ƙasa sukuni soyayyar AFREEN da bai taɓa zata ba tayi masa mugun kamu wanda har sai ya sashi ya kwanta rashin lafiya, kullum cikin tunani ta yake har yana ji a ransa idan bai sami AFREEN to zai iya rasa ransa amma kuma yaƙi faɗawa kowa cikin kuwa harda Ali dan har lokacin da ya kwanta asibiti likita ya sheda masu cewa tunani ne da damuwa suka masa yawa idan bai daina ba kuwa zai iya kamuwa da rashin lafiya dan sosai yake rashin lafiya yanzu hakama ba koda yaushe ya zuwa office ba sabida rashin ƙarfin jiki.
AFREEN saboda yawan samun matsala da fasa aurenta da akeyi yasa ta daina kula samari ta maida hankalin ta ga karatun ta.
A yau ne ya kama saura sati uku auren Anty Khairat yayi daidai da saura wata biyu da sati ɗaya auren Ali da Umar tare da ƴan matan su Khadijah da Fariya.
Duk da abin nan dake damun AFREEN na yawan fasa auren ta da akeyi ba tare da sanin dalilin da yasa hakan ke faruwa da ita ba, hakan yasa idan ta keɓe ita kaɗai a ɗakin, ta kanci kuka sosai har sai ta godewa Allah sannan take fitowa ta ci gaba da harkokin ta na cikin gida, kuma hakan bai hanata shiga cikin daginta ba aka shiga shirye shiryen auren ƴar uwar ta.
AFREEN tayiwa kanta alkawarin ce wa daga RAHIM ba zata sake yin wani saurayi ba zata zauna hakanan ba sai tayi auren ba tunda haka Allah ya tsara mata rayuwa akan duk mutuman dake da niyyar aurenta sai ya fasa,tashi tayi daga kwanciyar da take ta koma gaban mirror tana kallon kanta daga sama har ƙasa ta juya ta ƙara juyawa sannan ta koma duba kanta cikin mirror tace "Babu inda Allah ya rageni, saboda ina da kyau irin mugun kyau ɗin nan da yake yawan tsorata mutane da basu mamaki ina da diri iya diri haka ƙirjina a cikin yake masha Allah no banga abin makusa ba a jikina ba da maza ke yawan fasa aurena banga inda na raguba duk da ƴan magana sunce mutun tara yake bai cika goma, duk ni dai banga aibu na ba kodai inada wani hali mara kyau ne ban sani? ya Allah kayaye min duk wata damuwa ta Allah ka shiga lamarina ka duba halin da nake ciki ka fitar dani kada ka ƙara bawa kowane namiji damar wulakanta."
Kawai sai ta fashe da kuka ta koma saman bed ɗinta, ta shiga rera kuka mai cin zuciya idan kaga halin da take ciki dole ka tausaya mata, tana cikin kukan ne wayar ta ta kama ruri har kiran ya katse bata ma san an kirata ba sabida tana cikin tashin hankali.
Haka kullum take fama da zuciyarta duk ranar da ta kasa hakuri da abinda ke damun ta to zata fashe da kuka ita ɗaya a ɗaki tayi tayi har sai ta ƙoshi dan gaban kanta tayi shiru, yau ma haka ce ta kasance ta shiga ɗaki yin Sallah azahar kawai sai abin ya faɗo mata a rai sai tashiga tambayar kanta shin wai miye aibunta da kullum sai za'a aurenta a fasa ko dai ita haka Allah ya yi mata tata ƙaddarar tanayiyuwa ma ba zata taɓa aure ba a rayuwar ta, haka dai tayi ta zancen zuci ita ɗaya a ɗaki wani abin ta masa kuka wani tayi murmushi.
Daga nan saman darduma bacci yayi awon gaba da ita, a cikin bacci da take ne tayi mafarkin wani mutum na mik'o mata hannu tare da cewa *"AFREEN ki taho mutafi duk faɗin duniyar nan bakida miji da ya wuce ni dan haka ki daina ba ma kanki wahala, sabida ko gobe idan kikayi wani sabon saurayi sai kun rabu sabida ba mijin ki bane ni daine mijin ki kuma ina nan zuwa in tafi dake, dan haka ki tausaya min ki daina zubar da hawayen ki saboda wasu, dan wallahi kukanki na ci min zuciya, ko kinason nayi kuka ne?"*
Batasan lokacin da ta shiga girgiza kai ba cikin bacci tana ƙoƙarin share hawayen, kallon ta yayi yace "Koke fah to yimin murmushi ko zanji sanhi cikin zuciyata dan Allah banason ganin ki cikin damuwa ni ma duk sai naji bana cikin natsuwa."
Aiko sai ga AFREEN na sakin murmushi cikin bacci, shima murmushi ya saki tare da matsowa kusa da ita yana cewa "Ko ke fah yanzu dana ganki cikin farin ciki nima sai dana naji wani irin farin cikin ya ziyarci zuciyata dan Allah kada kiƙara min asarar hawayen nan naki masu tsada kinji ma femme ?"
Ɗaga kai tayi alamar to sannan yayi murmushi tareda cewa "Je t'aime beaucoup beaucoup (ina sosai da sosai)."
Harta buɗe baki itama ta fara da cewa "Moi......
Sai taji an fara tashin ta daga bacci Khairat ce ke tashin ta tana cewa "AFREEN tashi man bacci ya isa haka kije kiyi sallah har ƙarfe biyar tayi."
Firgigit ta tashi tana salati tareda cewa "Subhanallahi!!! soeurette ya akayi nayi bacci mai tsayi haka har lokacin sallah la'asar ya wuce ni inna lilahi."
Ba tare da ta jira mi Khairat zata faɗa ba ta tashi ta shige toillet bata wani jima ba ta fito ɗaure da alwala ta koma saman darduma ta tayar da sallah ba tare da tabi ta kan Khairat ba da ke saman bed ɗin ta tana saka mata murmushi.
Tana ƙarasa sallar ta juyowa ta kalli Khairat tace "Kai yau antyn nayi bacci sosai daga fah nayi sallah azahar sai na ɗan gincira shikenan nan fah sai bacci ya kwashe ni, wallahi duk banji daɗi ba da lokacin sallah ya wuce ni wannan wane irin bacci ne nayi haka?"
Dariya Khairat tayi sannan tace "Hum bacci kam mai daɗi kikayi tunda na tardoki kina ta murmushi da magana ƙasa ƙasa cikin baccin naki nasan wani mafarki ne kikeyi mai daɗi shiyasa ko, to bani labarin nasha."
Saƙe AFREEN tayi tana kallon Khairat na Kusan minti biyu sannan ta buɗe baki har zatayi gardama cewa batayi ba kawai sai mafarkin da tayi ya faɗo mata a rai da sauri ta waro ido waje tace "Anty Khairat da gaske nayi magana cikin bacci duk ana jin abinda nace?"
Da sauri Khairat tace "Dakata little sister kwantar da hankalin ki gayaman mike faruwa shin kinji tsoro ne a mafarkin naki ko kinga wani abin mamakine? amma da alamu mafarki ya maki daɗi tunda tsintar kinayi kina murmushi cikin bacci naki kowa ya ganki yasan mafarki ya maki daɗi." Khairat ta faɗa tana murmushi.
Shiru AFREEN tayi tana tunanin mafarkin da tayi tana mamakin ina tasan wannan fuskar Ita dai ta sanshi amma ta kasa tuna ida tasan shi ɗin.
Juyowa tayi ta kalli Khairat tace "Ni nakasa ma tuna mafarkin anty." Ta faɗi haka ne saboda idan tace ma Khairat ta tuna mafarkin to fah zata dameta ne da sai ta faɗa mata ko wane irin mafarki ne amma ita kuwa gaskiya ba zata iyawa faɗa wa anty Khairat wannan mafarkin ba ta mata dariya.