← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 69

Sashe 45

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nan dady ya kashe kiran komin minti 1 ba'a yi ba sai ga soƙon adress ɗin gidan Alhaji Sadisu ya turo masa ta whatsapp, yana dubawa sai ya kashe data ya kwanta ai yana rumtse idonsa ya fara hango photon AFREEN lokacin da ta ke kallon KAMAL tana sakar mai wani ƙayatacen murmushi ana masu hoto, da sauri AFREED ya buɗe idonsa yana sauke ajiyar zuciya batare da ya tashi daga kwanciyar da yayi ba, ya ɗauki kusan minti 5 a haka kamin yake kara rufe idon nasa amma ina hoton AFREEN tana yiwa KAMAL murmushi ya ƙi barin ƙwaƙwalwar da idon AFREED, bacci yake son yayi amma hakan taƙi samuwa, ya ɗauki dogon lokaci a haka kamin yayi shawarar shiga toillet ya ɗauro alwala dan gabatar da sallah nafila saboda samun saukin raɗaɗin da zuciyarsa ke masa.

Shima a nan saman darduma bacci ɓarawo ya kwashe shi, washegari wajen misali ƙarfe 12am AFREED da Ali suka kuno hancin motar cikin anguwar su AFREEN ba tareda sun sha wahala ba suka samu wani yaro ya nuna masu gidan Alhaji Sadisu wato maihaifin AFREEN suna kawowa bakin ƙofar gidan Ali yaja ya tsaya tareda dana hon da sauri mai gadi ya fito tareda ƙarasowa kusan motar yana tambayar su wayesu sabida bai sheda su ba kuma yaga bakuwar fuska, haka motar ma bai taba ganita cikin gidan ba.

Murmushi Ali ya sakar ma baba mai gadi danji yana tambayar sa wajenwa sukazo kuma wasu ke nema sannan Ali yace "Baba ina yuni an yuni lafiya? Ai wajen mai gidan mukazo ko yana ciki."

Baba mai gadi najin haka ya saki murmushi yace "lafiya lau yaro, aya wajen Alhaji kukazo kenan ai kuwa yana ciki kun taki Sa'a dan ina gani yau ko fitama baiyi ba amma yasan da zuwan naku ko shiyasa bai fitaba, ku bari na buɗe maku ƙofar sai ku shigo daga ciki."

Shidai Ali baice masa komai ba, sai murmushi da ya sakar masa, juyawa baba mai gadi yayi yaje buɗe masu kofar, ba tare da ɓata lokaci ba Ali ya dana hancin motar su cikin gidan, daidaita motar yayi yayi parking ɗin ta sannan suka fito har yanzu shi AFREED babu abinda ya faɗa zaki iya cewa ma baya gun, Ali ya kalle shi yace "Ɗan uwa to yanzu waye za mu aika yaje ya sanar da zuwan mu?"

Hararar sa AFREED yayi sannan yamashi nuni da ido cewa ya tambayi mai gadi, murmushi Ali yayi yana girgiza kai cikin zuciyarsa yace "Ah yau abubuwan ke bisa kai ko maganar ma ba za'a min ba."

Bai ƙarasa tunanin da yake ba yaji baba mai gadi nacewa "Ku ƙarasa daga ciki mana."

Da sauri Ali ya juyo gareshi yace "Yawa dama baba munaso a sanar dashi mun ƙaraso, yasan da zuwan mu amma bamu faɗa masa cewa yanzu zamu zoba ace masa ɗiyan abokinsa ne Sumana."

Baba mai gadi yace "Ah nagane to bari na sanar da su."

Baba mai gadi na kaiwa bakin ƙofar falon ya kwankwaso ba tareda ɓata lokaci ba AFREEN tazo ta buɗe ƙofar, tana ganin baba mai gadi ne tayi murmushi tace "Baba Barka da warhaka ku shigo daga ciki mana."

Shima baba mai gadi murmushi yayi yace "A'a ɗiyar albarka ba sai na shigaba dama Alhaji yayi baƙi shine sukace nazo na sanar da zuwan su dan haka ki koma ki faɗa ma Alhaji cewa yayi baƙi kuma sun ce ace ɗiyan abokinsa ne Sumana, abinda alhajin yace sai ki dawo ki faɗa man ina nan ina jiranki."

Jin abinda mai gadi ya faɗa yasa gaban AFREEN faɗuwa ba tareda da tasan dalilin hakan ba, haka kawai taji tanason gani ko su waye, koma yin murmushi tayi sannan tace "To shikenan bari na sanar da shi."

Ba tareda AFREEN ta jira jin abinda baba mai gadi zai koma cewa ba ta juya ta koma falon, Papa na zaune saman babba kujerar dake cikin falon AFREEN ta ƙaraso kusa dashi ta zauna tace "Papa inji baba mai gadi yace a sanar dakai cewa kayi baƙi kuma sunce su ɗiyan abokinka ne Sumana."

Papa najin abinda AFREEN ta faɗa yayi saurin ɗagowa daga kishingiɗan da yake tareda gyara zaman sa sosai a kujera sannan yace "Yima maza je kice a shigo dasu ya za'a barsu a tsaye waje kuma cikin rana," maida kallon sa yayi ga Zeinab yace "Zeinab tashi ki shigo da su, ke kuwa AFREEN kuje keda Fanna ku haɗa masu abu mai sanhi da abinci mai rai da lafiya."

Ba tareda ɓata lokaci ba duk suka nufi gun abinda papa yasaka su AFREEN da Fanna suka nufi kitchen ita kuwa Zeinab ta nufi hanyar fita daga falon inda suke tsaye ta ƙarasa tare da gaishe su cike da sakin fuska suka amsa mata sannan tace "Papa yace ku shigo daga ciki" tana faɗar haka ta juya ta fara tafiya.

Ba musu suka bi bayan ta daidai ƙofar falon suka ja suka tsaya a lokacin Zeinab har ta buɗe ƙofar tare da zura ƙafarta ta dama, amma jin sun tsaya yasata juyowa ta sakar masu murmushi sannan tace "Yaya ku shigo mana papa nanan falo yana jiran ƙarasowar ku."

Murmushi suma suka sakar mata AFREED harda lumshe ido saboda sosai yaji dadin kiransu da yaya da tayi a cikin zuciyarsa yake faɗin "Daga gani gidan nan akwai tarbiyya."

Ali ne ya fara ɗaga ƙafarsa yayi cikin falon sannan AFREED ya bi bayan sa tareda sallama a bakunan su, dam da dam AFREED yaji gabansa ya faɗi lokacin da ya tsintsi kansa a daidai shigowa falon ba tare da kawo wani abu a ransa ya yi addu'a ya ida shiga daga cikin, da fara'a papa ya taso har idan suke ya shiga tsakaninsu ya kama hannuwan su ya ida ƙarasawa dasu a cikin falon ya zaunar dasu saman kujerar daya tashi kamar wasu ƙananun yara sudai kam binsa suke a duk inda yayi dasu, sannan ya nufi kujerar dake fuskantar su ya zauna da murmushi ɗoke da fuskar sa, har papa ya buɗe baki zaiyi magana sai ya tsintsi muryar su suna gaishe shi, amsawa yayi cikin fara'a.

Sannan papa yace "Masha Allah AFREED Ali kun girma fah dan sosai na daɗe rabona da ku tun kuna yara yan shekara sha ɗaya sai kuma in an nunoku a TV, amma duk ganin da nake maku sai naga yanzu a gaba naga kunfi girma, ya kuke ya gida ya aiki dadyn naku yace man kuyi wata ɗaya a garin nan amma fah ko ya faɗa man kunanan."

AFREED yayi murmushi tareda ɗago da kai kalli papa a take ya ji mutuman ya kwanta masa yace "Lafiya lau alhamdulilah papa da fatan mun sameku lafiya, eh wallahi muyi wata a garin gobe ma zamu koma insha Allah.

Papa yace "To har zaku koma kenan nida naso ace a nan kuka sauka amma babu komai akwai wata rana."

AFREEN da Fanna ne sun fito daga kitchen rike da abinci da juice da ruwa a hannu suna tunkaro falon gaban AFREEN nata faɗuwa kuma ta rasa dalili, dan tunda taji muyar wanda ya shigo falon ta shiga cikin wannan halin sai tambayar kanta take ina tasan wannan muyar, haka take wajen AFREED ma sai faduwa gaban sa kuma yarasa dalili dan fira da suke da papa bawani jinsa yake dan hankalin ba ya wajen shi, suna gab da ƙarasowa falon wayar AFREEN tashiga ruri tana neman agaji, duba wayan tayi taga sunan data sakawa KAMAL ne ya fito sai ta saki wani irin murmushi, sannan ta juyo ta kalli Fanna tace "Sister dan Allah ki ƙarasa da kayan abinci cikin falon zanje na ɗaga waya KAMAL na kirana."

Fanna tace "To shikenan cœurly ajiye a nan idan na kai wannan sai na ƙarasa da wannan ɗin."

Murmushi AFREEN ta sarka mata sannan ta ce nagode cœurly," tayi gaba abinta ba tareda ta tsaya jin abinda Fanna zata faɗa ba."

Fanna na ƙarasawa falon tayi sallama tareda gaishesu batare da ta kalle su ba, kallo ɗaya duk suka mata sannan suka amsa gaisuwar tare da ɗoke kansu daga gareta lokaci guda sannan ta duƙa ta ajiye plet ɗin dake ga hannu ta, har ta miƙe tsaye papa yace mata "Ina AFREEN ɗin take ne na ganki ke ɗaya."

AFREED najin haka gaban ya ƙarayin wani irin lugude ya faɗi har saida ya riƙe wajen zuciyarsa, yana cewa AFREEN kuma to su anan garin basu da sunan sakawa yaransu sai wannan sunan kodai AFREEN ɗin da nasani ce? Kai ba ita bace watace daban amma ni sai naga kamar wada nasani din sunyi kama da wannan abokin dadyn bare idonsu kusan irin dayane kwayar idonta brown ne shima kuma papa nashi brown ne kodai abinda nake zargi ne idan hakane ai abin yazo man da sauƙi, anya kuwa nidai ina tantama.

Yana cikin wannan tunanin yaji muyar Fanna na cewa "An kirata a waya ne shiyasa nace ta tafi zan ƙaraso da abincin."

Murmushi papa yayi yace "Toh madala Allah maku albarka je ki ida kawo sauran."

Da to Fanna ta amsa sannan ta juya ta ida kawo sauran plet ɗin daganan papa yace "Taje ta kira masa matan nasa dan su gaisa da su AFREED."

Haka Fanna ta juya take kiran su maman AFREEN ba tare da ɓata lokaci ba duk suka haɗu a falon duk sun gaisa maman AFREEN ce ƙarshan fitowa tana saukowa daga escalier (stairs) cikin shiga ta kamala ta wata dakakiya shada irin uwar gida ta ɗoki yurin ta ɗin nan tana ƙarasowa falon ta zauna kusa da papa tana sakin murmushi tare da kallon inda su AFREED suke a zaune sannan tace "Sannu ku da zuwa yarori na ya kuke ya hanya?"

Ba tare da sun ɗago ba saboda duk kanun su a duƙe suke, Ali ne yayi magana kamar haka "Lafiya lau mama Alhamdulilah mun sameku lafiya?"

Shikuwa AFREED sai murmushi yake ya kasa cewa komai sabida lokaci guda yaji ya jin kunyar matar da wani girman da yake gani a a nan take, duk da ko fuskarta bai gani ba."
Chapter 45 · 0% Book details