← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 69

Sashe 40

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dady yace "Kanku dai akeji nikam nagama yanke hukunci." Daga nan suka ƙara gaisawa ya mata zancen sabkar Alkur'ani da za'ayi yiwa Khadijah a gobe lahadi sannan ya mata sallama tareda da katse kiran.

Da murna sa yake sanar da Momy AFREED wannan albishir da tanti tayi masa, itama cike da farin ciki take ta kwararo masu addu'a da Allah sa alkairi sosai taji daɗi har tana hango ta taci shiri tana cin bikin auren ƴayanta, kamar yanda ita take zuwa bikin ƴaƴan abukanta itama an kusan zuwa na nata ƴaƴan."

Shima Umar ya samu ya faɗa wa Fariya abinda ke ransa kuma ta amince da tayinsa dan haka soyayya ce me ƙarfi ta shiga tsakani Ali da Khadijah wada tu tanaji kunya har ta saki jikin ta suna shan soyayyar su, haka ma ɓangaren Umar da Fariya abin ba'a magana.

Washegari ya kama safiyar ranar Lahadi kuma yau ne saukar su AFREEN da za'ayi ƙarfe hudu na yamma, tunda safe gidansu su AFREEN ya cika da ƴan'uwa da abokan arziki, ana ta hidimar walimar saukar, AFREEN ce zaune cikin falon gidan nasu da waya a hannuta tana ta mayar da saƙon da ƙawayen ta ke ta turo mata wa'inda zasu samu damar zuwa da wa'inda ke faɗa mata uzurun su, sosai take chatting da kawayen da kuma annurrin zuciyarta wato KAMAL, wayar tace ta ɗauki rururi alamar kira ya shigo, wani irin farin cikin ne ya mamaye zuciyarta hada ɗan wani tsalle tayi daga zaune tace "Ma très très chère Momy jannah adoré" (my anti adorable) sannan tayi picking call din tana murmushi tare da yin sallama, kamin daga cikin wayar a amsa sallamar tace "Wayo mom na mai sona nayi kewarki sosai rabon da muyi waya tun shekaran jiya fah."

Daga cikin wayar akayi dariya mai ɗan sauti sannan wada ta kira Momy jannah cikin wata dadaɗa murya mai kamala tace "Haba my beautiful daughter irin wanan murna haka kamar dai nace gani a hanya zanzo Niger ke dai kam naga baki ƙiba kowane lokaci muna liƙe da waya nidake muna hira, to ya shirya shiryen saukar ne ana tayi ko? naso ace ina nan za'ayi wannan saukar sabida ta farin ma da aka maki ba na Niger amma ai dolene inda kin tashi aure nazo Insha Allah."

( In masu karatu basu manta Momy jannah itace ƙanwa Arahamat mahaifiyar AFREEN da kuma Ibrahim yayan su)

AFREEN tace "Haba Momy har sai zanyi aure ne zakizo, nida sai na ƙarasa karatu kamin nayi aure, ai Momy daga bakizo ba kwanakin nan muna samun hutu ni sai nazo Dubai ɗin dan nikam na matsu na ganki shekara 7 rabon dana sakaki a idona Momy tun inada shekara sha ɗaya rabon dana ganki a zahiri sedai ta waya ko indna munyi apple video ni kawai so nake naganki gani gaki Momy tu m'a beaucoup manqué (nayi kewarki sosai)."

Murmushi Momy jannah ta saki kamar AFREEN ɗin na gabanta sannan tace "Ai da zakizo ɗiyata danaji daɗi, sosai nakeson zuwan ki garin nan amma makaranta ta hanaki, kawai kuna shiga hutu ki kirani ki faɗa man ni zan kira mahaifin naki na tambaye sa zuwanki nan insha Allah."

To shikenan Momy ina yaya Aban, da ya Fujai da Inayah?"

"Duk sun fita wallahi daughter, Inayah kawai kenan bari na bata ku gaisa," bata jira cewar AFREEN ba ta shiga kwalawa Inayah kira yarinyar da bazata wuce 9years bata fito daga ɗakinta, tana zuwa uwar tace "Inayah karɓi ku gaisa keda anty AFREEN."

Inayah najin ance anty AFREEN ta karɓe wayar da sauri tana jin daɗi, sannan suka shiga yin hira itada AFREEN, sosai yarinyar keson AFREEN, sun ɗauki kusan minti 10 suna hira kamin suke yin sallama.

AFREEN na gama wayar da Momy jannah da Inayah, tana sauke wayar daga kunnanta kawai sai taji an rufe mata ido ai kuwa da sauri ta ɗan zabura sabida bataji shigowar kowa falon ba, cike da tsoro ta riƙe hannu wada ta rufe mata idon a tsorace tace waye saida ta maimaita sau uku kamin a sakar mata ido juyowa tayi da karfi da niyyar ganin wanda ya rufe mata ido, ai batasan lokacin da saki wani ihu can cikin maƙoshi ba tare da waro ido sanadin ganin Fanna ƙawarta dake Diffa a kusa da ita abin kamar almara ba tare da ɓata lokaci ba ta ƙarasa gun Fanna tare da rungumeta tana farin ciki sun kai minti biyu a haka sannan ta saketa tace "Cœurly da gaske kece yaushe kikazo, wallahi har na fida ran zuwanki naga jiya ta wuce baki zoba kuma na kiraki sedai ace wayar a kashe take, nace nasan baki samu dama ba, sai gashi kinzo amma dai ba daga Diffa kike ba ko? naga yanzu safiya ce uniform ɗin da za'a a saukar na nan kema nasa an dumka maki dama nace ko bakizo tu sai na turo makisu ta bus."

Fanna ta ƙara faɗaɗa murmushi dake fuskanta tace "Nidai ce cœurly tun jiya nazo dadare ina gidan cousine ki ta shamsiya dama nace suprise zanyi maki kuma gashi."

Ƙara rugumeta AFREEN tayi ta na murmushi sosai taji daɗin zuwan nata, suna a haka aka turo ƙofar falon aka shigo ba kuwa bace illa bancin Hasina dan haka itama idanunta suna sauka kan Fanna ta rugo ta rugumeta tace "Sis Fanna yaushe kika zo wayo Allah yaushe rabon da na ganki nayi kewar sosai."

Murmushin tayi tace "Nima nayi kewarku sosai kawai nayi niyyar yi maku bazata ne wallahi sosai naji daɗin ganin ku tare dani."

Daga nan sukayi ɗakin AFREEN, inda AFREEN kin ke ɗauke da jakar kayan Fanna har suka shige ɗakin saman gado suka baje sunata hira sun kai kusan minti talatin suna fira sai ga Firdaoussi cousin din AFREEN itama ta shigo, aiki nan suka gamu suna hira cike da farin ciki, sai wajan ƙarfe biyu da rabi na rana suka tashi da ɗaiɗaya suna shiga toillet suna yin wanka don shirin zuwa jan saukar."

Haka ɓangaren su tanti A'ishah ma anata shirye shiryen zuwa wajan saukar da za'ayi yiwa Khadijah kowa na ƙoƙarin shiri banda AFREED sabida so yake suna fita, shikuwa ya shiyar yaje masallaci inda ya saba haɗuwa da AFREEN ko Allah zaisa ya ganta cikin anguwar koda zata wuce ne, don wallahi shi idan yau bai ganta ba ana iya samun matsala, amma mi Ali ya nuna masa bai isa yaƙi zuwa saukar masoyiyarsa ba, dan haka babu wanda ya iya ya tashi ya shiga wanka dan ya shirya shima ya bisu badan yaso ba, amma ya ɗau alwashin, suna dawowa Sai yaje masallacin nan dan yau bata yiwuwa ma ya iya kwana ba batare da ya saka ta a idon sa ba, koda kuwa bazai samu damar gani fuskarta ba.

Duk sun na bakin motocin su AFREED kaɗai suke jira aikuwa sai gashi ya fito cikin wata irin dakakiyar shada Green kamar pomme (apple)🍏dumkin rigar iya kar ta bakin gwiwa da wando shima ya kamasa daidai musali da hula wanda iya ajiyar hular ma akan AFREED na daban ne, takalmin sa kalar shada ne agogon sa ma haka komai da komai dai yayi macin Masha Allah kayan sunyi matuk'ar masa kyau sosai suka ƙara fito da class dinsa ga wani uban kamshi da yake zubawa sai kace da ruwan turare yayi wanka, kannansa ma se da suka shagala da kallon sa kama tun daga Ali har zuwa ummi ya ƙaramar cikinsu, har tanti A'ishah ma ba'a barta a baya ba wajan kallon shalelen ɗan nata, Farisa ta saki murmushi a cikin zuciyarta tace "Dole ne yayana tun ba yau ne nagano cewa ka iya dressing cikin jinin ka yake ba Allah Ubangijin ya kare mana kai abin alfahari mu."

Daidai nan AFREED yaƙaraso gun, Ali ƙamewa yayi ya sara masa sai kace suna bakin aiki, sannan yace "Woow mutume na irin wannan dressing haka kamar zakaje zaɓen wanda yafi iya dressing ko kuma na kyawawa wai kaga yanda kayi matuƙar kyau kamar kaine ake yiwa saukar ko kuma kaine saurayin mai saukar."

Hararen Ali yayi ba tare da yace masa komai na ya nufi wata haɗaɗiya Prado green wada ta ɗan ciza color ɗin ya buɗe yacema tanti ta shiga su tafi sabida shi zaiyi driving da kansa dan yau yana sha'awar tuƙi, kuma haka kawai yake jinsa cikin farin cikin, batayi musu ta buɗe baya ta shiga kamin take ƙarasa rufa ƙofar Farisa ta ɗan matso da sauri ta buɗe gidan mai zaman banza ta shige, sabida tace sedai AFREED ya mata abinda zai mata amma kam ba zata shiga motar su Ali. Shima shigayayi bai ce mata komai ba ita Amal tashi gidan baya kusa da tanti A'isha ya tayar da motar , su Ali na ganin haka shima ya buɗe motar su ya zauna wajen zaman direba shima Umar ya buɗe wajan mai zaman banza ya shige, Fariya da Khadijah kuwa suka shige sannan Ali ya tada motar shikuwa AFREED har an wangale masa ƙofa ya fita Ali na binsa a baya, ƙwayen Tanti A'isha kuwa har sun riga da sunje makarantar kawai jiran tanti ne suke da kuma ita kahdijah da za'a yiwa saukar............

Muje zuwa.....😜😜😜😜😜

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit

Par

*QUEEN ZEEFAT*

_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_

*Wattpad@nazichou*

Barka barka *Mom Lalla* (sis sajida) ina tayaki murna ƙarasa littafinki mai takai ( *MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR)* gaskiya ki zuba ilimi da basira a wannan littafi yayi ma'ana sosai fiye da tunanin mai tunani Allah ya biyaki da gidan aljanna, gaskiya kin nishaɗan tar damu mun ƙaru da abubuwa sosai a ciki Allah ya yafe maki kurakuran dake keci, Allah ƙara basira da ƙarfin ido sai mun haɗu a sabon littafin ki wanda muke fatan samu kafin azumi💃💃💃💃💃💃

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*

*Page* : 37 & 38
Chapter 40 · 0% Book details