← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 69

Sashe 42

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da AFREED ya ji muryar AFREEN na gabatar da kanta da sauri ya ɗago harda ƴar zabura yayi jin muryar da ba zai taɓa mantawa da ita ba a tarihin rayuwar sa, sosai yayi mamakin ganinta yurin nan, dan sosai ya gane ta duk da tana cikin niƙaf, lokacin ɗaya yaji wani sanhi ya ziyarci zuciyarsa, murmushi yayi can ƙansa zuciyarsa yace "Ashe anan ne zan ganta, daban zoba dana yiwa kaina."

Bai an kara ba yaji zazaƙa muryar ta ta fara addu'a buɗe taro, sosai ya nutsu yana sauraran yanda zazaƙa muryar ta ke fitar da sautin lafiyayar ƙira'a mai daɗi sauraro, duk mantawa yayi da wajan mutane suke kawai shi gani yake shi ɗaya ne a gun kuma shine kaɗai ke sauraran dan haka ya shagala sosai da kallon ta ko kyafta idon sa baiyi, har ta fara karatun Alkur'ani tana kuka sosai ba har muryar ta na shaƙewa, wani mungun tausayin ta ne ya ɗari a zuciyarsa ba tare da ya an ƙara ba yaji wasu ruwa masu ɗumi sun sauko masa a fuska, bai kai ga shafe hawayen da suka zubo masa ba yaji muryar Ali nacewa " woow broh ban taɓa jin wani na karatun Alkur'ani ya birgeni naji kamar kar ya daina irin yarinyar nan sosai ƙira'ar tayi daɗi zakace wata balarabiya."

Sai a sannan ya tuna da gun sauka ne suke da sauri ya share nasa hawayen dan kada Ali ya gani, sabida yasan idan ya gani iskanci zai masa, sai kuma ya fara yan wange wange yana kallon mutane gurin duk sai yaji duk baiji daɗin ba ganin idon mutane akanta kowa ita yake kallo sai yake jin inama ace yana da ikon da zai je yace ta dakata da karatun nan ta tafi gida, haka dai ya dingajin ba daɗi a zuciyarsa duk da cewa bawai ganin fuskarta ake ba amma hakan ma ji yake inama ace kowa zai daina sauran muryar nan a barshi shi ɗaya ya saurara haka kawai yaji zuciyarsa na masa zafi.

Yanata zancen zuci har AFREEN ta kammala karatun ta koma gurin zaman ta, kowa na ta santin karatun sai ji kake ana macha Allah, papa baki ya ƙi rufuwa sai jin daɗin yake sosai nan daga bayan shi ya ji yasu mutane nace "Allah yayiwa iyayen wannan yarinyar albarka da suka sakata a islamiyya da kuma ita karan kanta yarinyar" sosai papa yake jin wani farin ciki na shigar sa, sai ya juya yace Amin nagode, sukuwa harda tambayar ko shine mahaifinta sabida kamar da suka gani sunayi sai papa ya amsa masu da eh daga haka suka fara masa fira harda masu karɓar number sa sukace dan ayi zumunci, sannan da ɗaya ɗaya ɗaliban da ake yiwa saukar suka fara tashi suna yin karatu har duk suka kammala karatun, sannan aka shiga raba kyaututtuka wa ƴan saukar.

Har yanzu dai AFREEN ce farin bawa kyauta, ga lasipika babban malamin yace "Alhaji Issa ɗan canjin shine zai bawa AFREEN kyauta (Alhaji Issa ɗan canji shine mijin tanti A'ishah wato tantin AFREED).

Alhaji Issa ya miƙe yana gyara malumalu dinsa ya ƙarasa ida AFREEN take tsaye kusa da kyaututtukan, ya ɗoki kyautar da aka tanada dan ita yana murmushi ya miƙa mata sannan ya saka hannu sa cikin Aljihu ya fitar da jika Talatin (50000) yamiƙa mata, risinawa tayi ta ƙarɓa tare dayi masa godiya, kafin Alhaji ya koma inda yake zauna, wani shima ya fito ya bawa AFREEN rafar ƴan 1000 da baisan iya adadin suba ya bata sannan yace "Allah maki albarka yarinya kiriƙe halinki kada ki canza shi."

Ta amsa da ameen tana godiya, haka mutane sukayi ta tashi suna bata kayauta har saida taji bazata iya rikesu a hannu ba dama wasu ta riga da ta ajiye a ƙasa, anty Khairat ce ta taso ta ƙara so inda AFREEN take tsaye da kyaututtuka kamar zasu rufe ta, tana ƙarasowa tace "Sannu ƴar ƙanwata."

Da mamaki ta juyo tana kallon Khairat amma ta kasa mata maga, kollon yaushe tazo garin ne take mata "Khairat na ganin haka ta lumshe idonta sannan ta buɗe su tace "Maida hankalinki wajan ƙarbar kyaututtukan ki daga baya nayi maki bayani." ba musu ta juya ta ci gaba.

Sannu a hankali AFREED ya tashi daga gun dayake zaune ya nufi idan zai sada dashi da AFREEN da takunkumi a fuskar sa gudun kada mutane su sheda ko shi waye, Ali ya zuba masa ido yana kallon sa da tambayar ina kuma zaije, yana ƙarasawa gun AFREEN da Khairat da babban malamin da su suke tayaya karbar kyaututtukan ya je gab da ita ya tsaya ya fido da key ɗin mota da sheck na miliyan ɗaya CFA ya miƙa mata sannan ya gusa sosai gab da ita yayi magana cikin wata muryar mai kama da ta raɗa yada babu wanda zai jiyoshi yace "Yakamata ki bar gun nan gaskiya sabida idon kowane gardi akanki yake duk da niƙaf ce a fuskar ki hakan bai kamata ba kowa na kalleki, sannan kishiyar hajin bana hadake duk da nasan kin taɓa zuwa dan na tsinkayi haura Makkah a bakin ki kwanaki nan da muka haɗu, ina tayaki murna malama AFREEN Allah ya riƙa Allah sa aci anfanin abin, sannan Allah bada ikon anfani da abinda aka sani, ga kuma kujera huɗu daban sai ki zaɓi wanda zaki bawa dan kuje hajin a tare." yana gama faɗar haka yajuya ya bar gun.

Dam da dam haka AFREEN taji gaban ta ya faɗi lokacin da AFREED ke mata magana, ɗago da idonta tayi ta bishi da kallon har sai ya kai gun zamanshi ya zauna, ya mayar da duban sa kanta, suna haɗa ido ya kashe mata ijiyarsa guda da sauri ta ɗauke kanta daga gareshi tare da sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya. Babban malamin makarantar tayiwa bayinin kyautar da AFREED yayi mata dan haka ya dauki lasipika ya fara dacewa, "Jama'a mungode Allah saka da alkairi yarinyar nan AFREEN ta gode da kyaututtukan da duk aka bata dan ta cancanci hakan, yarinya ce da samun irinta wannan zamanin sai an tona, masha Allah ta samu kyaututtuka masu dama, wani bawan Allah ya bata kyautar kujera maka biyar da mota da sheck na miliyan ɗaya sannan wani ya bata babur biyu da 100000 da sauran su an gode an gode Allah saka da alkairi KAMAL ma ya bata mota da 300000 da sauran wasu abubuwa, duk wanda ba a faɗi tasu kyautar ba suma angode kyaututtukan ne da yawa tsayawa faɗa kyautar da duk mutane suka mata bata lokaci ne.

Sosai AFREEN ta gane AFREED duk da yasa abin rufe hanci da baki, ƙara ɗagowa tayi ta kallesa, ai kuwa suka haɗa ido sabida shima ita yake kallo dan ya kasa daina kallon ta da sauri AFREEN ta kauda kanta shikuwa ya saki murmushi.

Yana gama faɗa aka shiga kiran sauran ƴan saukar ana basu nasu kyaututtuka da 100000, dan sosai alhazzan Maraɗi sukayi wasa da salla wajan bawa ɗaliban kyauta cikin kuwa da mahaifin AFREEN da maman ta Arahamat, ana kammalawa AFREEN ta ƙara rufe taro da addu'a wannan karan da kyar muryar ta ke fita sabida kuka da tasha haka yanzun ma wasu hawayen ne ke ƙara bin kuncin ta, idon AFREED na kanta dan haka duk sai take jita a takure, ta kammala addu'ar, suka fara ɗaukar photo ita da ƙawayen ta na makarantar ida suka matsa mata cewa yau dai kam sai ta fida niƙaf a masu photo babu yanda ta iya sai da ta cire niƙaf ɗin aikuwa kallo ya kuma gareta mutane na ta mamakin kyau irin nata, sosai wasu ke zuwa a masu photo tare kawai dan ta birgesu wasu kuwa dan su aza a status a total kuri, wasu kuwa dan gulma, aka fara mata tare da ƴan gidan su da su Fanna da Hasina suna ta arerewa abinsu suna farin cikin, haka wajan su AFREED suma ana ta masu photo tareda Khadijah da ƙawayen tanti A'ishah shi kuwa AFREED hankalin sa bai ma wajen su yana ida AFREEN ke tsaye tare da ƙawayenta suna photo dan ƴan gidansu sunyi tafiyar su.

Sosai ya shagala da kallon ta yana cikin kallon nata ya tsinkayi KAMAL wajenta yaje yace ƙawayen nata dan Allah su bashi aronta dan za'ayi masu photo ita kuwa AFREEN bata iya yi masa magana ba kuma ba ta ɗago ba ta kallesa ba, da su Hasina sukaga ha sai suka bar masu gun, ɗan duƙawa yayi yace "Yau ko ga gayar dani ba za'ayi ba kuma kinwani buɗe man fuskar ki sai kallon ki ake to kizo muje daga can ayi mana photo ko biyu ne kinji."

Ba musu ta bishi ida mai daukar hoto ke tsaye yana jiransu har suka ƙarasa wajen mai daukar hoton ba tace dashi komai ba, suna zuwa mai hoton ya fara masu, ana cikin yi mai hoton ya ɗauka yace madame ki kallesa sai kiyi ɗan murmushi sai a ɗauka hankan zaiyi kyau sosai, aikuwa haka ta faru, ta saki wani tsadaden murmushi tana kallon KAMAL daidai lokacin da hakan ta faru akan idon AFREED aikuwa zuciyar AFREED tashiga wani irin motsawa tana wani yin sama tana dawowa sosai zuciyarsa kemasa zafi dalilin gani KAMAL da AFREEN da yayi an masu hoto hada murmushin ta mai tsada take sakar masa, a cikin zuciyarsa yake cewa "Wanene wancen da har ya samu wannan damar, miye haɗinsa da ita, kadai saurayin tane? Dam dam dam gabansa ne yayi wata muguwar faduwa har sai da ya riƙe zuciyarsa sai yaji ba KAMAL ba har AFREEN ɗin haushin ta yakeji kamar mi, sai kuma ya koma yace "To koma waye ɗin tane mike ruwana a ciki."

Taku har kullum mai kaunar ku💖
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit

Par

*QUEEN ZEEFAT*

_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_

*Wattpad@nazichou*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*

*Page* : 39 & 40
Chapter 42 · 0% Book details