← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 69

Sashe 51

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanin cewa AFREED idan ya riga ya furta ya ƙoshi to komai za'a yi masa ba zai ƙara cin komai ba dan haka Ali ya miƙo masa ruwa ya ƙaraba ya sha sannan ya ɓalo maganin ya mika masa da wasu ruwan marasa sanhi haka ya ƙarba ya sha duk abinda ke faruwa akan idon Dr Inusa, yana ganin AFREED ya kammala duk abinda aka saka shi ya sakin murmushi ya ce "Masha Allah yarona Allah ya ƙara baka lafiya." Sannan ya ƙara tambayar abinda ya keji yace masa baijin komai sannan ya fita ya bar ɗakin.

A lokacin AFREED ya kamo hannu Ali yace "Ali ka sa dady ya rubuta mana takardar sallama na ji sauki babu abinda ke min ciwo yanzun, nagaji da zaman asibitin.

Ɗan hararen sa Ali yayi yace "Naƙi na saka ya bamu sallamar bancin kaje kana wani banzan tunani ka kana shirin hallaka mana kanka."

"To nace ban iya zaman ka saka a sallame mu ko na tashi nayi tafiya ta ba tareda....."

Bai kai ga ƙarasa sa abinda yayi niyyar faɗa ba aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, Momy da dady su ka shigo da murmushi ɗoke da fuskar su ganin AFREED zaune har yana magana sallama sukayi tare da da ƙaraso wa gun da gadon da AFREED ke kwance da sauri momy ta riƙo sa ta masa sannu tace "Ɗan albarka na ka farka, Allah na gode maka da ka tashi ka faɗun wannan yaro, yanzu mike maka ciwo?"

Murmushin ƙarfin hali AFREED yayi sannan yace "Momy ina yuni da fatan kin yuni lafiya, dady sannu da zuwa anzo lafiya, dady yaushe kazo."

Farin ciki ne ya mamaye zukatansu baki ɗaya sannan momy tace "Lafiya lau ɗan momy ya jikin naka?"

Kamin AFREED ya bata amsa dady ya kamo hannu sa ya shiga shafa kansa da hannu sa na dama yace "Yau nazo yarona momyn ka tayar mana da hankali ba dole nazo ba shiri ba, ga yanda nazo na tarar da kai na'aza ma rasa ka zamuyi amma kaga Allah da ikon sa ya tashi ƙafaɗun ka cikin ƙanƙanan lokacin naga alamun har gida zaka iya tafiya ma ko ba haka na tara kana faɗa wa Ali ba."

Murmushi AFREED yayi tare da duƙe kansa ƙasa, nuni yayiwa Ali da yazo ya taimaka masa yayi Sallah haka Ali yazo ya kamasa suka nufi toillet ya shiga ya ɗauro alwala sannan ya fito Ali ya kamasa ya kawo sa har gun darduma da Momy ta shinfiɗa masa ya fara gabatar da sallah azahar da ya kammala bai bar saman darduma ba ana suke ta fira shida dady, momy, Ali, da kuma Fariya da Farisa suna nan a zaune akayi kiran sallah la'asar dady da Ali har da AFREED mara lafiya suka nufi masallacin da ke cikin asibitin saboda yace zai iya takawa da kan sa har masallacin dan kuwa yanzu ya daina ganin jirin da ke diɓarsa tun farkawarsa haka kuwa suka tafi masallacin a tare, idan kaga AFREED sai kace wani cikakkin mai lafiya dan lafiya lau yake takawa ba wani tangaɗin marasa lafiya, Momy kuwa da ƴan biyu suka gabatar da tasu sallah a ɗakin da suke jinyar AFREED.

Ba'a ɗauki wani lokaci ba su dady suka shigo cikin ɗakin wannan karon su huɗu ne suka shigo har da Dr Inusa, AFREED ya nemi gurin ya zauna bakin gado da ya tashi, duk suka ƙara so bakin gadon suna kallon sa, Dr Inusa ya kalli momy yace "Madame naga yaron naki ya warware ko dai gida yake da buƙatar zuwa tunda yayi saurin korar rashin lafiyar."

Kamin momy tace wani abun AFREED yayi saurin cewa "Eh dady wlh naji sauƙi zan iya ta fiya gida ko da kaina ne."

Duk ƴan cikin ɗakin suka kwashe da dariya suna masa dariya shima ɗan murmushi yayi ya sune kansa.

Dr Inusa yace "To madala yaro na amma duk da haka sai gobe insha Allahu zan baka sallama, dan na ƙara ganin yanayin jikin ka, zuwa goben yanzu ka yi shiru ka rage magana amma kada kayi bacci, kai Alhaji biyoni office akwai abinda zamu tattauna."

Murmushi dadyn AFREED yayi sannan yace "To muje."

Suna fita AFREED yace "Gaskiya ni momy ban ce zan iya bacci a nan ba a barni naje gida goben da safe idan Allah ya kaimu sai na dawo a dubani."

Wata ya ƙaramar harara momy ta sakar masa tace "Wato ni daka raina zaka faɗa wa wannan banzar maganar shi Dr Inusa da dadyn naku da suna nan mi ya hanaka faɗa masu haka to babu inda zaka a nan ɗin zaka kwana, in badan ma Allah yaga tausayin mu ya ga halin da muka shiga ya taimake mu ya baka lafiya, da a lokacin da muka kawo kane, ka ga halin da kake ciki ko iya magana kanayi shasha kawai maza imani shiru ai kaji abinda doctor yace."

Badan yaso ba AFREED ya kame bakinsa ya yi shiru gudun kada ya ƙara magana ya ɓata ma mahaifiyar sa da rai, dan haka babu yanda ya iya ya jingi na da abin gado ya shiga tunani.

Bangaren dady da Dr Inusa kuwa suna shiga bureau ɗin doctor suka nemi gurin zama suka zauna a wata haɗaɗɗiyar ƙatuwar kujera dake cikin office ɗin, sannan suka sake gaisawa, tare da ɗan taɓa fira sannan Dr Inusa yace "Yawa abokina dama abinda yasa nace ka biyo ni wata shawara nakeso muyi akan AFREED." Sai kuma ya ɗan yi shiru.

Ganin yayi shiru yasa dady cewa "To ina jinka doctor saida Dr Inusa ya gyara zaman tare da yin gyaran murya yace "Alhaji ya kamata a yiwa AFREED aure hakan ne zaisa ya rage duk wani tunani da yake yawan damun sa har yake ƙoƙarin saka masa ciwon zuciya, kuma idan ka bincika bai wuce dalilin mace ne ya shiga wannan halin da yake ciki ya kamata asamu ma fita, ku tuntuɓe shi idan har yanada wace yake so ya fitar da ita sai ayi gaggawar zuwa neman aurenta gidansu saboda AFREED ya kai mizanin aure yanzu, yana da buƙatar wace zata ringa taimaka masa da shawarwari da kuma lamura na yau da kullum."

Sai da dady ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Hakane doctor nima abinda nake tunani kenan wallahi kamar ka shiga zuciyata wallahi, amma maganar cewa saboda mace ne ya shiga wannan halin gaskiya ina tamtama, abinda kuwa yasa nace haka shine AFREED bai kulla mace, kada a kai ta nesa ma kasan ko cousins ɗin sa mata bai cika kulawa ba bare har ya kulla wata a waje."

"Duk da haka abokina yanzu ba zaka taɓa gano bakin zaren ba sai ka bincika zakasan ko daga ina matsalar take, idan kuma kasan da babu wace ya ke so to kawai ka nema masa mai hankali da nutsuwa ko cikin cousins ɗin sa ne sai ka aura masa ko da bai sonta zai sota daga baya."

"To shikenan babu damuwa insha Allahu zan je na duba mashi wada zata dace dashi sai kawai a haɗa su."

Doctor yace "A'a ba hakanan ba za'a yi sai ka fara tuntuɓar sa kaji babu wace yake so kannan sai ka yanke hukunci."

Ok Insha Allahu haka za'ayi yanzu sai da safe za a sallame shi ko."

"Eh sai da safe insha Allah."

Bayan haka suka ciga ba da fira tafiya bikin auren Khairat ɗiyar Alhaji Sadisu yayar AFREEN, daga bisani kuma suka bar office suka nufi dakin da aka kwantar da AFREED.

*Washegari*

Da safe wajen ƙarfe 10 na safe AFREED ne kwance kan gadon asibiti yasha wasu ƙananun kaya masu masifar kyau wanda su Fariya su kawo masa tun jiya da yayi wanka yau ya saka bayan ya fitar da na bacci da ya kwana dasu, idan ka ganshi zakace bashi ne mara lafiyar ba, shi ne ya yiwa mai jinya rakiya sai wani game fuska yake shi a dole ya gaji da zama asibiti, Ali na lura da hakan shima ya game ta sa fuskar dan ba ƙaramin zafi AFREED ya ke ji ba, shi a ganin sa sabida min zai ki faɗa masa damuwa sa da har ta kai sa ga rashin lafiya, Ali gani yake da ya faɗa masa abinda ke damun sa da damuwar bata kai ga saka masa ciwon zuciya da sun haɗa kai sun shawo kan matsalar ko kuwa su nemi mafita kamin haka ta faru, amma shine ya ki faɗa masa, dama akwai abinda AFREED zai iya ɓoye masa kenan?

Ali na cikin wannan tunanin dady da doctor suka buɗe ƙofar ɗakin tare da sallama a bakin suka shigo, da ma momy da ƴan biyu suna daga gefe suna fira Ali ne ke kusa da gadon AFREED ɗin ya na dane dane a waya sa shikam fushi ma yake da AFREED ɗin dan ganin ya samu lafiya kuma ya ƙi sanar dashi damuwar sa, su dady na shigo wa doctor ya dubi gun da su momy suke a zaune ya buɗe baki da niyyar zai magana ƴan biyu suka katse sa ta hanyar gaida sa cike da kulawa ya amsa sanan yayi wa momy sannu da gida tare da tambayar mai jiki. Sannan ya juya wajen AFREED.

Yana ƙarasawa bakin gadon shi da dady AFREED ya tashi zaune ya gaida shi cike da sakin fuska suka amsa sannan doctor ya kama hannun sa na dama yace "My son ya ƙarfin jiki."

Ɗan murmushin yaƙe AFREED ya saki sannan yace "Jiki da sauƙi dady ai na ma warke yanzu babu abinda nake ji."

Murmushi doctor ya saki sannan yace "Ah yarona irin wannan zuba haka dan ka nuna min kaji sauki saboda ka matsu ka tafi gida to sai gobe, takarda sallama da nazo maka da ita ma bari na koma da abita."

Murmushi AFREED yayi tare da sun ne kansa yana susa kai wai irin yaji kunyar nan dan shi kam babu abinda yake so yanzu kamar ya ganshi gida.

*_Kumin afuwa masoyansa ZAMBA CIKIN AMINCI kwana biyu banada dama ko yanzu ma kokarin ne nayi wa jan gani na faran ta maku.....*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit

Par

*QUEEN ZEEFAT*

_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_

*Wattpad@nazichou*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*
Chapter 51 · 0% Book details