← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 69

Sashe 67

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dama ita yarinyar Momy Jannah tunda suka shigo ta nufi maman AFREEN tayi zaman ta a saman ƙafafun ta sukuwa yan mazan suka shiga gaida mutan wajen.

Nan dai basu wani jima ba Momy Jannah taje gun doctor ta karɓar AFREEN takarda sallama sannan saboda asitin mijinta ce kuma ta nuna masa katin ta na aiki saboda ita likita ce tace masa zata ida kula da ita a gida.

Shi kuwa papa tunda yaya sa Adamu yazo ya bishi suka fita tare dan haka bai masan da zuwan Jannah ba.

Daga nan suka tattara suka yi gida suna zuwa suka tarda matar yayan su Ibrahim tazo (Wato yayan su Arahamat mahaifiyar AFREEN) da ku ƙanwar mahaifiyar su wada ta riki Momy Jannah sai kuma Ufadi matar mahaifinsu da ta riga ta sadako ma duniya tunda ta aurar da Arahamat da tayi ta yimata sha tara ta arziki duk da mahaifinsu ya rasu hakan baisa suka yadata ba.

Gida dai ya cika da ƴan uwa da abokan arziki su Khairat da fauziya kusan kullum suna gida ana ta shirye shiryen biki zuwa dare wajen karfe takwas Fanna kawa AFREEN ita ma ta diro garin yau farin ciki gun AFREEN bai musultuwa, ga Hasina kawarta ga cousin ɗin ta Maryam ita da ta dawo gidan da zama har a gama biki ga Fanna kawarta da ke diffa tare da iyayen duk sun zo ga uwa uba Momy Jannah hakan yasa AFREEN ta saki ranta sosai kamar bata da wata damu daren ranar kwana sukayi hira hada Momy Jannah ta shige cikin su kamar wata yarinya, da sukayi sallah asuba sannan suka kwanta,

Washegari misalin ƙarfe 11:00 na safe AFREED ya kira AFREEN a lokacin ta na tsakan kawayenta suna hira tare da son sun mantar da ita damuwar da take ciki, tana ganin mai kiranta saida gabanta ya yanke ya faɗi, ta kalli Hasina, alama Hasina tayi tama da ta ɗaga, tana ɗagawa tare da sallama saida ya lumshe idon sa da yaji Muryar ta, sannan yace kema amincin Allah ya tabbata a gareki AFREEN da fatan kin tashi cikin koshin lafiya ya karfin jikin ki?"

"Alhamdulilah" ta furta tare da lumshe ido kamar yana gaban ta.

Yace "To madala AFREEN naji bayanin da Hasina tayi man jiya na gamsu kuma kada ki ƙara tayar min da hankalin ki kinji Allah baiyi ba zamu kasance a inuwa guda ba Allah bai saka nine mijinki ba dan haka mu ɗoki dangana ki daure ki yiwa iyayen ki biyayya Allah sa haka shine mafi alkairi amma har yanzu ina ji a jiki na ked'in tawace."

Da kuka AFREEN ta fashe masa ta kasa cewa komai, hada rumtse idonsa yayi don ji yanda kukan ta ke shigar masa zuciya,saida ya ɗan nisa sannan yace "Idan kina kuka kika kasa kwantar da hankalin ki zanyi kasa daurewa nima, kuma kisan idan hakan ta faru komai zai iya faruwa dani ko?"

Da sauri AFREEN ta tsaida kukan ta sannan tace "Toh shikenan Allah ya baka wada ta fini amma nidai kai nakeso babu wani bance zan iya zama da wani wanda ba kai ba."

"Hakane AFREEN ni banji ina iya zama da wata bayanke ba Ni nasan sedai na mutu banyi aure ba."

AFREEN tace "Dan Allah kada kaminhaka."

AFREED da zuciyar sa ke neman karewa yayi saurin katse kiran gudun kada taji shima kukan yake.

Gidan su AFREED anata shirye shiryen biki wanda AFREED kullum yana cikin ɗaki yana jiyar zuciyar sa dake masa ciwo, kuma shi ma bai taɓa kawowa a kansa cewa hada shirin bikin sa ake yi ba kawai ya ɗauka shirin auren Ali da Fariya da Farisa ake yi ba dan kuwa itama Farisa ta samu nata saurayin wanda accounter ne dake aiki a wani babban banki dake Maraɗi wani aiki ne ya kawo sa Niamey suka haɗu ita kuma har su asaka ranar nasu auren tare da na su Fariya.

Kwanci tashi babu wuya a wajen Ubangiji yau ya kama saura kwana biyu ɗaurin aure AFREEN, da kuma na su Ali da Fariya, turare kala kala irin iri masu wani irin nagartacen kamshi ake ta yiwa AFREEN gyara da su saboda maman ta haɗa kallan na ta mama mahaifiyar Fanna da ita kanta Fanna da sun haɗo nasu saboda nasun ba kallar na kowa bane wai kusan dai yanda barebari suka iya haɗa turaruka masu mugun kamashi da kwantar da zuciya sun kawo mata shi kalla yafi a ƙirga, sannan ga na Momy Jannah irin na larabawa kai AFREEN sai tayi Hai huwa goma turarukan da aka haɗa mata basu kare dan mugun yawan dake gare su.

Momy Jannah da Maryam yayar alhaji Sadisu da maman Hasina sun tafi Niamey tun ga jiya dan yiwa AFREEN gyara ɗaki, wani irin tangajejen gidane kuma haɗaɗe da mahaifin AFREED ya gina ma Ali da AFREED irin ɗaya kuma liƙe da juna gidajen sun haɗu iya haɗuwa Masha Allah, mahaifin AFREEN ba ƙaramin kuli ya kashe mata gaskiya komai na gidan kalan pink ne daidai yanda painting gidan yake ɗaki biyar ne da kitchen da dinning da kuma ɗakin matsa jiki da falon biyu na saman si keda ɗaki biyar na kasan ɗaki uku da kitchen da dinning da gun motsa jiki shima.

Ranar da yake saura kwana uku ne aka lefen AFREEN Akwati 28 duk makil da kawa masu mugun tsada ko ba'a faɗa ba kana kallon kayan zaka gane valeur din su Masha Allah, wanda duka kayan mahaifinsa ne ya bama mahaifiyarsa kuɗin taje kasashe daban-daban ta haɗa su ba tare da shi yana san mi suke shiryawa ba dan kuwa har yanzu basu faɗa masa.

A na gobe ɗaurin aure akayi walima idan aka shirya amarya cikin wani haɗaɗan matériel red 🍒 mai mugun idan tayi wani sihirtacen kyau sai wani irin kamshi ke tashi a jikin ta wanda ko ke mace sai ya birgeki bare namiji ai shi sedai ya rikice an sha hotuna

Su alhaji Sumana da docter Inusa da mahaifin Ali da danginsa AFREED da abokansa da Ali sun zo don abukai guda gare su kuma sun zo a kan ɗaurin auren Ali dan dukan su babu wanda yasan za'a yi auren AFREED har Ali, ida uwayen amaren da angayen suka amince da a ɗaura auren yaran duka a ƙofar gidan Alhaji Sadisu hake ce kuwa ta kasance.

Washegari da misalin ƙarfe takwas na sake aka daura auren *ALI DA KHADIJAH DA KUMA UMAR DA FARIYA SAI FARISA DA ISMA'IL DAGA KARSHE A KA DAURA AUREN AFREEN DA AFREED* akan sadaki 100000 ko wane aure auren da ya tara duban mutane dan gayin yawan suma bana baki ce,

kowa yayi mamaki cewa hada AFREED aka daura wa aure bare ma abokan sa dan shi yana cen yana waya bai maji an daura aure da shi ba wani abokin sa da mamaki ya gama cikashi ya je idan a ya tsabtace yana amsa waya ya warce wayar yace "Dakata malan da wata wayar ka ta munafurci ashe hada kai za'a daura wa aure shine ka ki sanar damu sai hidimar na Ali kawai mukeyi shiyasa ana shirin ɗaura naka auren kashi ga yin wata wayar karya to Allah ya toni asirin ka.

*Kuyi hakuri da kurakurai*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit

Par

*QUEEN ZEEFAT*

_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_

*Wattpad@nazichou*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*

_*Fin*_

*Page*: 65 & 66

AFREED da bai gane inda ya dosa ba yace "Aure ni?" sai ya bushe da dariya "Auren Ali da kannaina dai."

"To rai na min da hankali AFREED idan baka so ne mu sani sai mi." Abokin na sa yayi fushi.

Zai juya AFREED ya rike shi yace "Wai mikake nufi ne mu zai sa na ɓoye maku aure na ne wallahi banda ni."

Haba AFREED yanzu naji an daura maka aure da kunnuwa na naji sunan ka da suna wata mai irin naka sunan sannan kuma kacemin ba haka bane to mai dani ƙaramin yaro... Kamin AFREED ya yi magana sauren a bokan su kayi ƙaraso sunana ta masa masifa, shi dai kansa ya kulle ya rasa gane inda suka dosa AFREED da idonsa suka fara cenza kalla ya ɗago ya kalli Ali da alamar tambaya, shi Ali ɗaga masa kai kawai yayi dan shima yana cikin shok kwata kwata iyayen nasu basu sanar dasu hada AFREED a daurin auren ba, shima sai yanzu nan yaji abakin dady bayan har an daura auren yake tambaya sa abinda yaji gaskiya yace masa hakane ba ƙarya ko ɗaya a ciki.

Dan kiɗimewa AFREED kasa magana yayi ya nufi motar da ya zo da ita ya shiga ya yi tafiyar ba tare da ya tankawa ko ɗaya daga cikin abokan nasa ba, Ali yake fahimtar dasu cewa shima baiwa labari kamin sun hakura da masifar da suke masa.

Yana parking baki ƙofar gidan Aunty A'isha ya sauka ya wuce ɓangaren da suka sauka ya ɗauki kayan sa sai filin jirgi, za'a tayar da jirgin ya tura Ali test cewa shi ya koma gida ya zo filin jirgin ya ɗauki motar makulin na ga wani ma'aikacin jirgin zaman abokin sa yake babu inda aka diresa ya Niamey ya zuwa kuma bai nufin gidan su ba dan yanada bukatar hutu da tunanin makomar wanan auren dolin da aka yi masa.

AFREEN tunda aka daura aure take kuka har da suma sau biyu da an tambaye ta sai tace ita batason ta bar gida da khair Momy Jannah ta samu ta lalaɓa ta ta fara yi mata nasiha da kuma ƙara mata karatu kan zaman aure ta yi ta koya mata yanda ake zama da miji ta kowane fanni komai AFREEN an nuna mata tayi komai na kula da miji tunda Momy Jannah ta dawo daga Niamey dan tace ita zata raka ɗiyar ta ha ɗakin miji bazata tsaya cen ba har sai an kai mata amarya ita zata zo ta ta fi da ita, take ta aikin rarashin AFREEN tare da yi ma nasiha.
Chapter 67 · 0% Book details