← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 69

Sashe 62

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

AFREEN tana ƙarasawa ta ɗoki lait ɗin tasha da ruwa ta bar juice🥤 ɗin, sannan ta kalli maman tace "Na ƙoshi."

Maman tace "To bari naje na ɗauki hijab ɗina da key na mota na mu wuce asibiti."

Kamin ta tashi AFREEN ta riƙon hannun ta tace "maman dan Allah ki dai na maganar asibitin nan wallahi na daina jin ciwon kan ya rage dama inaga yunwa ce tasa ya ki daina min ciwo amma ina ci yanzu ya rage kuma nasan zuwa anjima zai daina min ciwo gaba ɗaya."

Ɗan hararan ta maman tayi tace "To sarki kin tsoron alura da magani na yarda kada muje asibitin amma da sharaɗin yanzu zaki kuma shan magani."

Da sauri AFREEN ta ɗaga kai tare da cewa "Eh." Dan ita da ayima ta alura karama ta sha maganin duk da shima ba ƙaunar shan sa take ba."

Murmushi maman tayi da jin ta amince dan Kada a aje asibitin sanin irin tsoron alura da AFREEN keyi.

Ba ƙaramin tashi hankalin AFREED yayi ba ganin ya kasa samun AFREEN, babu kiran da bai mata ba shiru, haka maganar da yayi mata a whatsapp tafi a irga amma sai yaga tunda safe wajen ƙarfe bakwai da ta sauka ba sake kuma online ba haka yayi mata text message shima babu amsa daga ƙarshe ma idan ya kirata sai ace wayar ta kashe take saboda tunda AFREEN ta samu labarin miji da papa ya mata ta kasa ɗaga wayar sa dan bata masan mi zata faɗa masa ba daga ƙarshe ma ta kashe wayar da niyar zata canza number saboda inda ya daina samun ta a waya dole zai hakura, kuma tana gudun kada ta barshi yayi ta sonta alhalin ba auren sa ba zata yi gara dai ta fara nesa da shi gudu kada ta masa brisé coeur.

A ranar kwana ma gagara sa yayi sai da ya yi sallar asuba kamin ya samu bacci ɓarawo ya sace shi.

Tanti na fita daga gida ba ta tsaya ko ina sai gidan anti hawa ku ta shiga tarda yayar ta ta ta shirya kawai bai su tsaya komai ba suka ka ma hanyar gidan kawar tanti don tun jita sun sanar mata cewa yau akwai tafiya gidan boka, dan haka suna fita cikin motar da tanti ta zo da ita direct gidan Hajiya lubabatou suka wuce sun tarda ta shirya su kaɗai take jira basu wata wata ba suka ma hanya yini ranar a gidan bokaye dayan tsubo suka ƙare shi amma amsar guda suke samu cewa "Wannan auren na AFREEN sai anyi saboda rantsatsen aure daga Ubangijin dama ko cen da tayi ta ɓata ma ta auren saboda su wa'in cen din ba bu mijinta a cikin su ko da bata zama silar ɓata auren to zai lalace kamin tayi hakan amma dan wannan fa dai anyi sai idan anyi a hana su zaman lafiya da miji har ya sake don gaskiya idan AFREEN ta zaman ta yaron nan to ta gama dace da miji kuma zata ɗaukaka sosai da sosai.

Hankali a tashe suke barin gidan ko wane malami, gidan na ƙarshe da suka fito tanti ta aza hannun ga kai ta fashe da kuka tace "Na shiga uku ita wannan yarinyar da wace irin sa'a tazo duniya ne wai da gaba ɗaya ta ki tamnuwa ta ki haɗu to bata isa ba ni sai nayi maganin ta."

Anty hawa ta kamo hannuwan ta sauke su ƙasa, Hajiya lubabatou dafa ƙafaɗar ta tayi tace "Kawata kin kwantar da hankali ki ita ɗin banza miye ita, duka wajen malami biyar ne fa muka je ni ban kaiku wajen nawa bokan ba mai aiki kamar yankan yuƙa, shi kam idan muka je gun sa ta ƙare dan haka yanzu mu koma gida na shi da ke kusa muyi sallah azahar da la'asar tunda muka fito muke tangarara a titi ko sallah ba muyi ba gara muje mu sake nauhin ta daga nan sai muka hanyar daƙoro (Wani ƙauye ne dake cikin jahar maraɗi) idan zan haɗa ku da wani shahararren boka ƙasurgumin matsafi na tabbata nan ba makawa buƙatar ki zata biya."

Ba musu suka bi shawarar ta tare da nufar gidan Hajiya lubabatou suna ida sallah suka suka ɗauki hanyar daƙoro tanti ke dreving, awa biyu sukayi a hanya suna shiga a ana kiraye kirayan sallah magarib, gidan waya ƴar uwar Hajiya lubabatou suka tsaya sukayi sallah Hajiya lubabatou na sanar da ƴar uwar ta cewa wajen mutumen suka zo bari su ƙara sa, sannan suka ɗauki hanya da zata sada su da wani daji wadan shine ida bokan yake, suyi tafiya ta kusan minti arba'in kamin sukai gun bokan da cikin wata matsiyaciyar buka idan ka ganta ba zaka ce akwai mutun a ciki ba sannan ga layin mata da suka tardo gashi kuma har ƙarfe 8:30 na dare yayi dan tanti ta nayi ta duba montre gudun ka papa ya kai ga kiranta idan yaga dare yayi ba ta zoba 9:00 nayi hankalin ta in yayi dubu ya tashi ga shi har yanzu layi bai kawo kansu ba, ta dubi anty hawa tace nashi ga uku Aunty wallahi idan Alhaji ya gane bana cikin gidan nan har zuwa warhaka da nasan yanzu su na shirin fara dinner to wallahi Allah kaɗai zai rabani da shi don wallahi ba ya son muna fita har dare yayi ba mu dawo gida ba."

"To kinga dai ko aikin ga ba mu samu ba hasali ma layi ko kawowa gare mu baiyi ba sedai in hakura zakiyi mu juya sai ki faɗa masa rashin lafiyar nawa ne ya yi tsanani shiyasa baki samu kin dawo da yuri ba."

"Haba anty har mun kai waraha ka kuma zan ce zan hakura da aikin a dai nemi wata shawarar ba wannan ba ai da kinga na koma to wallahi mun gana da bokan nan."

Hajiya lubabatou tace "hakane gaskiya bai kamata ba ace kin hakura da abin nan tunda ga mu a wajen in dai ba ke zaki tafi ba ki bar mu nida Aunty sai mu gaya maki yanda ake ciki idan mun koma, ko kuwa ki kira shi alhajin ki faɗa masa jikin Aunty yayi tsananin shiyasa baki samun dawo wa tunda ke ce zaki zauna da ita a asibiti."

"Eh ke ma kin ce wani abu amma wani hanzari ba gudu ba kada na ce muna asibiti ya ce zai da safe ya zo yaganta ko kuwa yanzu."

"Sai kisan abinda zaki faɗa masa idan yace hakan, amma idai ba hakan ba zaki ce sedai ki tafi ki barni Ni da lubabatou sai mu yi masa bokan bayani dan ba nida matsala miji na bai nan ni yarana tun muna saman hanya na kira su nace sau muyi dare kamin na dawo."

Hajiya lubabatou tace "nima nawa mijin ya yi balaguro yaran kuwa suna kidan kakan nin su dan haka hankali na a kwance ke dai da matsala."

Tanti tace ai dakin ga na bar gun nan na samu ganin mutumin nan na fi son a komai gaba na bari na koma daga cen na kira shi."

Tanti ta tashi ta ɗan yi gaba takira papa ta sheda masa cewa ita ce zata zauna gun anty hawa jikin ya yi tsanani ga su ma a asibiti nan papa yace mata ba damuwa shi bai ma gari yana madarunfa (shi wani kayane dake cikin garin maraɗi), wani abu ya taso masa na gaggawa Arahamat kaɗai ya kira ya sanar ma kan ta sanar da su sai zuwa jibi zai dawo sannan yai mata fatan Allah ya ba anty hawa lafiya.

Wani farin ciki ya luluɓe ta jin bai ma garin amma kuma ta ji haushi da yace wai Arahamat kaɗai ya sanar mawa kenan su bai da lokacin sanar da su.

Ta katse kiran ta ja wani uban tsaki, sai ko taji an mayar mata da tsakin cikin wata irin gawurtaciyar muyar aiko da sauri ta shiga wage wage cikin tsoro ta yi saurin barin gun tana waigawa har ta dawo inda ta barsu Aunty hawa, ta dawo tana basu labarin ashe papa bai ma garin da ta sani da bata ma kira sa ba, sannan kuma take sanar da su cewa wai Arahamat ƴar gaban goshin sa kaɗai ya sanar da ita ta fiyarsa wai ita kuma ta sanar masu ai dole ma ta tashi tsaye a kan su."

Ƙarfe 10:30 suka samu shiga wajen bokan da ko kyau gani bai da idan ka cika kallon sa ha amai zaka iya yi ma, amma su dayake zuciyarsu ta ƙeƙashe ba ma su ganin haka ba tare da ɓata lokaci ba tanti tashiga zayana masa abinda ke tafe da ita.
Chapter 62 · 0% Book details