← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 69

Sashe 3

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AFREEN tace tanti bari naje kada nayi lati tare da saka takamin a kafarta Tanti tace yi maza ki fuce naga har 2:50 tayi amma yau AFREEN ki ban mamaki yada kika yi magana da yawa haka AFREEN tasaki murmushi tare da bari cikin dakin tanti na biye da ita a baya tace tanti wai ina anti khairat tunda nazo ban ganta ba Maman ki ta aiketa gidan yayar ku amma yanzu ta dawo nasan dai sai kin dawo zaku hadu tanti ta fada AFREEN tace to Tanti dan Allah ki fada ma maman cewa nafuce sabida nayi lati kamin na je saman stairs nayi mata salama lokaci zai kure ta fada tana me murda kofar falon tafita Tanti na mata Allah kiyaye hanya ta amsa da ameen tare da ficewa daga falon gaba daya
Wajen parking space ta nufa tac ciro makulin motar tareda nufar motar da tashigo da ita dazu ta bude ta tashiga ta tada motar tare da barin cikin parking space din ta nufi kofa mai gadi na ganin haka ya wankale mata kofar ta fita a guje sabida latin da tayi tafiyar minti 10 yakai ta makarantar parking space taje ta paka motar ta fito ta kule ta yin hanyar ajin nasu da aka riga aka shiga tsaya wa tayi bakin kofar ajin ta taba hannu daga ciki aka amsa da oui rentre(yes enter) tashiga da salama tare da gaida malamin ta nemi waje ta zauna malamin binta yayi da kalo har ta zauna kamin yaci gaba da explaind din lesson daya ke.

Karfe shida daidai suka fito daga ajin nasu ita da wata farar yarinya da bazata wuce shekarun AFREEN ba tsayisu yaso ya zo daya sai dai AFREEN ta fita da kadan itama kyaukyauwace yarinyar ba lafi sanye take da riga da sket na Atanfa sunyi matukar yi mata kyau sanye take da dan karamin hijab da baikama ta gwiwa ba, yarinyar tace AFREEN wai yaushe zanga fuskar ki dubi fah tun lokacin da muke dake, har gidan ku nasha zuwa baki taba bari naga fuskar ki ba basan ko sabida miyasa kike boyemin fuskar ki ne wai idan ma kin boyema kuwa ai ni bai kamata ki boyemin ba duba fa kiga yanda yanzu ko a hanya nagaki bazan sheda kiba inba tafiyar ki nagani ba AFREEN tace hasina kenan wlh ba abinda yasa ni ke boye wanan fuskar ta waba saida dalili babu wani dalili AFREEN idan dai kin dauke ni a matsayi kawa to ki nuna min fuskar ki yanzu ba se anjima ba gaskiya yanzu ai zanji kunya idan aka tambaye kamanin kawata nace ban saniba ai za'amin dariya ace du kawancan dake tsaka nin muma basanki ba AFREEN tace kiyi hakuri dan Allah kawata wlh watarana zan nuna maki fuska ta amma yanzu rishin ganin fuskata a gareki shine mafi alkairi a'a ni wlh bazan taba yarda ba gaskiya wata muguwar kama ce gareki daza kice wai rishin ganin fuskar ki shine mafi alkairi ka mardai wata aljanah
AFREEN tace wlh hakan da fada maki gaskiya ne hasina a'a kedai ki nunamin don wly idan baki nuna min yau ba kuma yanzu wlh bana shiga motar kiba kuma kawancan mu daga yau ya kare haba hasina meyasa zakice haka nan hasina tace kindai ji abinda nace ai ko to kinga ma tafiya ta da sauri AFREEN ta riko hannuta tace yi hakuri kawata muji mota sai na bude fuskar ki gani haka hasina ta bita suka nufi idan motar take tabude motar ta shiga hasina ta bude wajen me zaman banza ta shiga ta rufo kofar AFREEN nagani tashiga tayi saurin wiwa motar key tare da barin cikin makarantar hasina na mata masifa amma ko kulata ba tayi ba, bata tsaya ko'inaba sai kofar gidan su hasina, hasina na ganin ta tsaya takai hannun jikin kofar zata bude ta fita taji ta a kule fuska a matukar daure ta juyo daniyar masifan ce AFREEN lokaci guda tasaki wata irin kara hade da furta wa innahu suleymanu wa innahu bismilahir rahamin rahim, inna lillahi wa inna illaihi raji'un la'illaha illah anta subhanaka inni kuntum mina zalumin a tatare ta jero wa yanan adu'o in gaba daya a lokaci guda sanadiyar arba da tayi da kyaukyauwa fuskar AFREEN.

Ganin yanda ta firgice tana kokarin bude motar ta fita yasa AFREEN sauri bude mata motar da sauri ta fice daga motar ta shige gidan su kamar wada tayi wani mugun gamo da abin tsoro mafi tsoratawa a fadin duniya.

Commenté

Et

Partager

Comment

And

Share

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

ECRITE:

_PAR_

*QUEEN
ZEEFAT*

Yar
Mutan
Niger

Wattpad@nazhabibou

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM

Page 3

AFREEN ta aza kanta saman steering din motar ta ce ga abinda nake gudu ya faru yanzu bansan yaza ta doki abin
ba da ban bude mata fuskan ba kuma tace ban doketa a matsiyin kawata ba dana bude mata fuskar kuma nasan yanzu ma gudu na zatayi wai wane irin kyau ne dani wanda mutane basu iya jure ganisa kodai wata kama gareni mai ban tsoro wada ni ban ganin ta sai na tare dani tare ta jero ma kanta wa'inan tambayoyin da taga batada mai amsa mata su yasa ta mayarda nikaf inta ta tayar da motar ta nufi gida,tana zuwa gida bayan mai gadi ya bude mata get ta shiga tayin parking motar a parking space tafito ta nufi cikin gidan ta na shiga falo da salama ta tarar da mahaifiyar ta dake zaune tana kalo gaida ta tayi sanan ta karasa kusa da ita ta zauna a saman carpet mahaifiyar ta ta amsa tace AFREEN yanzu dinma kin jima a makarantar injin dai lafiya

Lafiya lau Maman AFREEN ta fada a takaice tana mai cire nikaf din fuskar ta maido da kalon ta tayi wajan mahaifiyar tata cike da damuwa kamin takai ga magana Maman tace lafiya ki AFREEN naga kama akwai abinda ke damunki dubi fuska na Maman wai ni kyau gareni ko muni wace irin munmuna kama ce dani da duk wanda ya kaleni ya ke firgita alhali ni banga abin firgita a cikin tsarin halita na taba ko kama nike da mutanan boye ban saniba kodai da gangan mutane kemin hakane tunda ni ban ga abin tsoro a tatare dani ba AFREEN ta tambayi mahaifiyar ta ta da hawaye kwance cikin idon ta da alamun damuwa a tatare da ita Maman tace ko alama ba ko daya daga cikin abinda kika zayana a tare dake AFREEN maza mayar da hawayen ki kada kiyar da su zubo dole ne mutune su ringa firgita da irin kyau da Allah ya maki ba wani ba ma ko ni dake mahaifiyar ki mamakin wanan baiwar kyau da Allah ya maki nake AFREEN.

Yan magana nace wada yayi fari ya gama kyau amma ni tuni na karyata wanan magana tunda Allah ya azurta ni dake tunda kinga kedai ba za'a saki a layin farare ba haka ma ana bakake babu ke a ciki sedai asaka ki a tsakatsakiya amma kinga duda haka Allah ya miki kyau irin wanda baza'a iya musilta shi ba dan haka godiya ya kamata kiyi wa ubangiji da yabaki baiwa kala kala ba wai butulce mashi ba.

Kuma ina me gargadin ki da kada kiyi anfani da kyau da Allah ya maki wajan saba masa ki zamana me kyautatama sa komi rantsi duda banda shaku a kanki amma yanzu zamani ya canza kawaye ma na iya sauya ma mutun tarbiyar da iyayensa suka mashi dan haka ki kula AFREEN kisan irin kawayen da zakiyi mu'amala dasu ba kowa ake kawance da shiba.

Dan haka ki fida damuwa a ranki sabida kyau ki ba me tsoratarwa bane kawai dai dole ne ya firgita mutane bama karma a bazata mutun ya ganki, tunda wasu za su ringa tunanin cewa kedin munmuna ce shiyasa baki yarda aga fuskar ki wasu kuma suce kyau ne dake shiyasa amma baza su taba tunanin kyau naki ya kai haka ba wasu zasu ce ra'ayi ne da ganin dama ko suce da gangan ne yasa kike saka nikaf ba mai taba zaton dalili ki nayi haka kinga Maman ni yanzu harma na saba ban iya fita babu nikaf sabida dana fita mutane sai su dinga min kalon kurila wasu ma har guduwa suke wasu kuma mamaki nake basu kamar dai babu wanda ya fini kyau a duniya Maman kinsan a kawai masu kyau sosai wanda suka fini nesa ba kusa ba amma kuma nawa kyau se yadinga firgita mutane ga laraba wa da indiyawa nasan da cikin su a kwai wanda suka fini kyau nesa ba kusa ba amma su ba'ayi mamakin nasu ba sai nawa, hum AFREEN kenan bazaki ganeba ne kefa naki kyaun na daban ne indiyawa ko larabawa suma nasu kyau daban yake bama yanayin ki guda dasu kinga su a cikin suma za'a iya samun wanda kyau su zai iya firgita mutane fiye da naki to kinga ke yanayi kyau naki ne yake firgita mutane da basu mamaki badan wai ba za'a iya sami me kyau fiye danaki ba ne a'a ke hada baiwa da Allah ya baki me sa du wanda ya ganki yake ganin annuri da kyau suna karuwa a fuskar ki fiye da yada ke kike gani

Dan haka ki kula kiji tsoron Allah ki guji sabama ubangijin ki dan bai cancanci haka daga garemu ba Allah abin bauta ne dan haka mu bauta masa fiye da yanda ya umurce mu idan har za muyi ma kan mu adalci ma halicin ya cancanci mu kadaitashi ko dan rayuwa da ya bamu sadakar yi aiko ubangiji mu ya gama mana komi Allah dai ya kara mana imani da tsoron sa a ciki zukatan mu ya bamu lafiya da kwonciyar hankali mai daurewa ya tsare mu kuma ya kare mu daga duk wani iftala'i da sharin duk wani mai shari Allah yamana kyaukyauwan karshe yasa mugama da duniya lafiya.

AFREEN ta amsa da ameen Maman zata sake magana Maman ta katseta da cewa kada kikara ce wa komi AFREEN.
Chapter 3 · 0% Book details