← Book details Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 69

Sashe 54

Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani ɗan ƙaramin murmushi Khairat tayi sannan tace "Kina mamaki ina nasani ko alors que toi tu n'a rien dit à personne (ke kuma gashi baki faɗawa kowa ba) to bari na faɗa maki hali na idan kin manta ki sani duk abinda na saka ma ido to sai na nemo cikin da wajen shi ina ga ki manta ko wacece Khairat shiyasa kike mamakin abu nan da ya fito daga baki na, to ki ma daina mamaki komai zan iya bincikowa inda har na damu dashi ko kin manta abinda na karanta ne, amma ki samu ki ɗanyi bincike kema zaki gano abinda na gano, waini bana ce tayin wani abu ba, amma nasan da akwai *ZAMBA CIKIN AMINCI* a lamarin ta kuma nasan watarana zaki ce na faɗa maki."

Shiru dai har yanzu AFREEN ta kasa cewa komai dan abun yayi mugun ɗaure mata kai sai can ta ɗan nisa tace "Anty bari naje na ɗan watsa ruwa sai na fito muje jardin (garden) muyi fira ko da yake ashe ke baki fita zan dai dawo."

Tace "To ƴar ƙanwata sai kin dawo."

Ba tare da tace mata komai ba ta fice daga ɗakin direct ɗakin maman tayi tana shiga ta tardo tana saka kayan da aka goge ma ta a wardrobe tayi sallama ta ƙarasa shiga ɗakin tace maman sannu da hutawa."

Maman wada tun shigowar AFREEN da tayi sallama ta ɗago tana kallon ta tace "Yawa AFREEN daga ina kike ɗazun na tura Zeinab kiranki tace man baki nan."

"Eh wallahi maman ina ɗakin anty Khairat."

"Ah ok to shikenan mi Khairat kin keyi yanzun."

"Babu abinda take na bari ta a zaune amma ta yiyu yanzu ta shiga wanka tunda naga gommage ɗin dake ga jikinta ya bushe, maman bari na tayaki mayar da kayan." AFREEN ta faɗa tare da tashi daga saman gadon ta nufi mahaifiyar ta."

Aa barshi AFREEN jeki ki huta kinji ko."

"Maman ba fa abinda nayi bare ace inda na gajiya naje na huta."

Eh duk da haka ki zauna ki huta ke da kullum ba kison kina hutawa sedai aiki ai rai nason hutu, yanzu kam na hutar dake ɗanewar ki kan gado ki kwanta ki ɗan huta koda kaɗan ne, kin ga ma na kusa ƙarasawa kingin abu huɗu na ƙarasa gyaran."

AFREEN tace "To shikenan maman bari naje nayi wanka sai na zauna na huta." AFREEN ta faɗa ta na ƙoƙarin miƙewa ta bar ɗakin mahaifiyar ta.

Maman tace "Aa ba sai kin koma ɗakinki ba shiga toillet ɗin na kiyi wankan ki tunda kina da kaya a nan sai ka canza idan kin gama shirya wa sai ki kwanta ki huta."

"To maman." AFREEN ta faɗa tare da tashi ta nufi toillet ɗin."

Ba wani jimawa tayi a toillet ɗin ba ta fito ta yi shirin ta cikin wata doguwar riga mara nauhi tare da ɗanewa saman bed ɗin mahaifiyar ta ta yi kwancin ta ba tare da ɓata lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita.

Ali na gama wanka ya shirya tsaf ya fito daga ɗakin ya nufi na AFREED ya shiga tare da sallama, ya na zaune bakin bed ɗin ya faɗa duniyar tunani dan bai ma san shigowar Ali ba har saida ya dafa shi, da sauri ya ɗago yace "Broh har ka fito?"

Ba tare da Ali yace masa komai ba ya nemi guri kusa dashi ya zauna sannan yace "Broh ka fah san doctor ya hana ka yawan tunanin amma kaƙi daina hankan zai iya ƙara saka maka wani ciwon dan Allah ka daina ya ƙa faɗa man abinda ke yawan ɗaga maka hankali har haka sai mu nemi mafita tare da taimakon Ubangiji sai kaga komai ya daidai ta."

Wata naunauyar ajiyar zuciya AFREED ya sauke tare da juyowa yana kallon Ali sannan yace "Wallahi broh ina cikin matsala ban ma san daga ina zan fara faɗa maka abinda ke damuna ba."

Ali yace "Fara daga inda ya dace ɗan uwa."

AFREED ya ƙara sauke wata ajiyar zuciyar sannan yace "Broh ina wata yarinya wada sunanta yake kaman ce ceniya da nawa ana ce mata AFREEN idan ba zaka manta ba ita ce ta buɗe taro a lokacin saukar su Khadijah, wata ƴar doguwa ba zakace mata fara ba kuma ba zaka ce mata baƙa ba teint café au lait dai (chocolat color ) Kai tana da ma haske dan gaskiya ga wani ba za'a cema chocolat color, ba zaka iya cewa ma ba fara bace don gaskiya teint (fatar ta) ɗin ta tana da fari se dai ba can ba, ban san ko ka gane wada nake nufi ba, don ita ce damuwa ta."

Ali ya ƙurawa AFREED ido yana kallon sa yace "To ina jin ka na gane yarinyar wata mai zazzaƙa muryar kamar sucre yarinyar ta birgeni sosai ai seda nayi enregistrer (saved) ɗin muryar ta lokacin da tana karatun Alkur'ani, amma kai miye haɗin ka da ita da har ta zame maka matsala?"

AFREED yace "Babba matsala ma kuwa saboda ba a nan muka fara haɗuwa da ita ba don mu san juna tun kamin zuwa gun saukar nan, nan dai AFREED ya kwashe tun farkon haɗuwar da AFREEN ya faɗa masa har abinda ya keji game da ita da duk abinda ke saka shi cikin halin rashin lafiya duk a kanta babu dai abinda ya ɓoyewa Ali komai ya sanar da shi.

Ali da AFREED ya gama zayana masa komai da komai ya tsaya yana nazarin ɗan uwan nasa na kusan minti biyu, kuma daga bisani ko mi ya tuna sai ya kwashe da dariya yana tayi sosai har saida ya yayi mai isar sa."

A lokacin har ya ƙula da AFREED ya ɓata ran shi sannan ya miƙe ya bar gun ya koma wajen window yana kallon farfajiyar gidan, Ali na ganin haka ya tashi ya nufi gun AFREED yana gumtse dariya sa yace "Broh dan Allah yi hakuri zo zauna muyi magana."

A ɗan fusace AFREED yace "Naƙi na zauna ɗin ya zan faɗa maka matsala ta, amma ka zauna kana min dariya yau ga mai abun dariya naga da wasa ma ka ɗauki lamarin."

Ali yace "Wallahi ba haka bane ɗan uwa ke ɗin ne ka ban dariya, amma kayi hakuri zo muje muyi shawara samun yanda zamu bulowa wannan lamari a sauƙaƙe, komai zai daidaita da ka faɗa man da yuri da duk haka bata faru ba, amma insha Allahu yanzu komai ya zo ƙarshe."

AFREED naji abinda Ali ya faɗa ya bisa suka koma bakin gadon suka zauna, Ali ya ɗan saki wani ƙayatacen murmushi sannan yace "An zo wajen wai yaushe ɗan uwana ya faɗa soyayya banida labari har ta kai ga yi masa mummunan kamu haka, har take neman sa ɗan uwana ya rasa ranshi, wallahi yaya AFREED ban taɓa tunanin zaka so wata ƴa mace ba, har soyayyar ta tayi maka wannan kamun wa na kama, gaskiya a jinjina wa wannan yarinya da tayi nasarar sace min zuciyar ɗan uwa na abinda ban taɓa tunani ba, mutuman da ko kallon mace baiyi bare har a saran zai mata magana, yanda ƴan matan Niamey ke rububun ka amma basuyi nasarar samuka sai ƴar maraɗi, kai gaskiya matan maraɗi sun ciri tuta ya kamata a jinjina masu."

AFREED yace "Kaga nifa ba dan kayimam iskanci bane na faɗa maka idan kana bani shawara da zata anfane ni to ka faɗa man ni banson iskanci, ko faɗawa soyayya haramun ne ko kuwa ni kaɗaine hakan ta fara faruwa da ni ne."

Ali na ganin ransa ya ɓace yace "Haba yi hakuri broh ba wai dan wani abu bane na faɗi haka ba kawai kaban mamaki ne par surprise na ji zancen (a bazata) dole na ce haka, amma ina da wata mafita idan ta maka to matsalar nan ta kau."

AFREED ya wani haɗe fuskar kamar ba yason jin mafitar a dakile yana wani shan magani yace "Ina jinka."

Murmushi Ali yayi yace "To saki fuskar man kana wani yimin yanga kamar baka son jin abinda zance."

Shidai AFREED bai ce masa komai basai fido wayar sa da yayi ya shiga dan nawa kamar bai sauranran shi."

Ali ya ƙara yi wani murmushi dan yasan halin mutum nashi ba tanka masa ba zai yi sannan yace "Mafitar da na samu itace zan shiga in fita in sama maka number ta daga nan sauran ya rage naka sai kasan abin yi."

Ɗan ɗagowa AFREED yayi daga kallon wayar sa ya dubi Ali da yaga Ali shi yake kallon sai yayi saurin maida idon sa ga wayarsa dan kar Ali yaga damar sa, amma a zuciyarsa sai da ya furta "Alhamdulilah."

Ali ya yi murmushi yace "Hum ba ma ko zaka godeman ba to na fasa nemo da number tata sai kayi ai." Ali na faɗar haka ya tashi ya fice daga ɗakin."

AFREED ya bi bayan sa da kallo har sai da ya fita, yana ganin Ali ya rufo masa ƙofar yace "Allah nagode ma nan ba da jimawa ba zan fara waya da farin ciki na, broh ai nasan ka faɗa ne zaka nemo man number ta alhamdulilah."

Shi kuwa Ali ya na fita ya nufi ɗakin sa ya zauna ya na tunani ta ina zai fara neman number AFREEN, can cikin tunanin ya tuna ashe makarantar su ɗaya da Khadijah, kawai ba tare da ɓata lokaci ba ya fido wayar sa da ga aljihu ya nemo number Khadijah yayi lancé appelle (ya turo kira) tare da karawa a kunne, sai da kiran ya kusan tsinkewa a ka ɗaga wayar tare da sallama.

Ali ya amsa sallama sannan yace "Hubby yau ko dai laifi nayi ban sani ba naga ba'a ma son daukan kiran nawa."

Murmushi mai sauti Khadijah tayi sannan tace "Wallahi Hubby ba haka bane bana kusa da wayar ne na shiga wanka ina fitowa na tarda wayar tana ruri da ba ma zan ɗaga ba, kawai idona ya sauka akan sunan da nasaka maka ne ke yawo saman screen ɗin sai nayi saurin ɗaga dan kada ta katse."

Ali yace "Ah kane ya faru to shikenan na maki uzuri ya kike ya gida ya su tanti da tonton injin dai kowa lafiya?"
Chapter 54 · 0% Book details