Sashe 17
Zamba Cikin Aminci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Oh Allah ba haka nake nufinufi ba ai d'an halak bai manta alkairi kaga kenan idan na manta ka ai na manta da aikairin da kamin, kuma nazama butulu kenan fah!! Kaga ko gaisawa ma bamuyi ba, ina yuni ka yuni lafiya?"
"Lafiya lau alhamdulilah da fatan kina lafiya, ya kwana biyu."
"Lafiya lau nake, kwana biyu sai alkairi bari nashi na karb'o ma kud'in ka Abbu ya ce kana dad'e."
"Abbu na ciki ne?
"Eh yana ciki."
"Shine kuma baza ki man tayin naje na gaidashi ba ko dai rowar baban zaki min?"
"Ko d'aya wallahi manta wa nayi shima Abbu d'in yace idan ka dawo karb'a cikon ka nace ya neman ka manta wa nayi."
"Woow!!! Har kin ba Abbu labarina ashe kema kina ciki?"
"Ina ciki kamar ya?"
"Share kawai, ko baki ciki to ni nagani kuma na k'aisa yi sauri kije ki sanarwa da Abbu zuwana."
Arahamat da ta kasa gane inda kalaman sa suka dosa kawai sai tasa kai ta nufi cikin gida ta nazuwa ta sanarwa Abbu cewa wanda ya taimaka mata da kud'in ne lokacin da a ka sabce nata ne ya zo. Abbu yace taje ta shigo dashi.
Komawa tayi ta gaya ma sa sok'on Abbu kannan suka dawo tare, da sallama ya shigo gidan, aka amsa masa lokacin Abbu na tsakar gida tare da uwar gida Ufadi sunna d'an tab'a fira k'asa k'asa duk yawan maganar Ufadi k'orafi yafi yawa.
Haka dai ya shigo ya samesu kansa duke durk'usawa yayi ya gaida amsawa sukayi cikin sakin fuska, Abbu yace "Bismillah yaro ga guri zauna" tare da nuna masa tabarmar da yasa Arahamat ta shinfid'a tashi yayi daga tsugun nin da yayi koma kan tabarmar ya zauna kansa na kollon k'asa ita kuwa Arahamat tana kawo tabarmar ta shigewar ta d'aki.
Gyaran murya Abbu yayi sannan yace "Yaro mi sunnan ka?"
Ba tare da ya d'ago ba yace "Sadisu?"
"Masha Allah Sadisu kana lafiya?"
"Lafiya lau."
"To madalah Arahamat ta zo da kud'in ranar nan tace kaine kabata wane dalili ne yasa kaba ta alhalin baka santa ba kuma tana yiwu ma baka tab'a ganin taba?"
"Eh wallahi nine naba ta sanadin ganin ta da nayi tana kuka sosai a hanya a lokacin gaskiya tausayi ta bani shiyasa natsaya na tambaye ta miya faru tace kud'in ta aka sabce kuma idan ta dawo gida tace sun b'ata f'ada za'a mata shiyasa sai na taimaka na bata kud'in to har neman canjin tayi da bata samu ba ta bar kud'in idan aka aike ta, kuma saida nayi nayi da itama ta rike sauran canji ta ki shiyasa nace ta nuna min gidan idan ta karb'o saura kud'in sai nazo na karb'a, amma baba a zahirin gaskiya yanzu ba karb'a kud'in nazo b...........
Bai k'arasa zancan ba Ufadi ta katse shi da cewa "Ji min munafinkin yaro to mika zoyi in ba karb'a kud'in ka ba, ko ka zo ne ka k'arasa lalata ta a cikin gidan uban ta kai malalaci wai wane taimakon kayi? ka b'ata yarinya yanzu wake taimako dan Allah ai sai dai bani in baka, ka lalata yarinya ka bata kud'i muku ma kace mana wai gani kayi tana kuka dan k'arya, ni dama tunda na ganka nasan ba d'an kirki bane diboka kayi kama da malal............
Bata k'arasa fad'in abinda zata fad'a ba a tsawa ce Abbu yace " Yiman shiru Ufadi wa yasaka ki acikin maganar nan ko kinji an kira sunan ki ne a cikin zancan nan ne."
"Ah to malam ga gaskiya sai naki fad'a dan dai ba'ajin tsoron Allah."
"Wallahi idan baki min shiru a nan ba ranki sai yayi mumunan b'aci manzon tsira SAW yana cewa fal yak'ul khairan aw liyasmut, to idan kisan ba alkairi zaki fad'a ba ki tashi ki bar min nan tunda dama ba gayato ki nayi ba, ko kunya ta bakiji a gabana kina ai batamin yarinya to nagaji dajin irin wad'an nan munanan kalaman naki kan y'ata kinan zargin ta akan abinda ke da kanki kin san ba gaskiya bane, ban san mi tayi maki ba kike mata haka."
Abbu ya k'arasa maganar ransa a matuk'ar b'ace sumi sumi Ufadi tata shi tana cewa "Ga gaskiya sai a hanani fad'ar ta" tashige d'akinta da sauri sabida tasan da Abbu ya zafi ba wasa.
Tana shiga d'akin kuma sai tace "Miyasa ma nake aibata yarinya can gaban yaron nan idan fa auren ta yakeson yi shikenan na b'ata auren, gaskiya da sake idan auren ta yazo nema kam zan san yanda zanyi na gyara maganar inaaaaaa mijin auren da nadad'e inason ta samu don taje ta bar min gidan in huta da jaraba kuma da rikon d'an da ba nawa ba, ai da sake koda ba neman auren ta ya zoba zan shiga in fita sai ya aureta tunda dai har ya kawo kansa gidan nan tun yaushe nake fatan Allah ya kawo man mafita na jefar da d'an mangoro in huta da k'uda ko kad'an banison ganin yarinyar nan a cikin gidan nan wallahi dole ma tayi aure ta bar min gida duk da cewa gidan ubanta ne amma yazama dole ta bar shi."
Ufadi ce ke ta wanan maganganu ita d'aya a d'aki."
B'angaren Abbu kuma Ufadi na tashi ya juyo kan Sadisu yace "To yaro bismillah ina jikan da mikazo dashi baya ga karb'ar sauran cikon kud'in ka."
Sai da ya d'an nisa tare da girgiza kai idonsa na kallon k'asa sannan yace "A gaskiya baba tun ranar da naga Arahamat ta kwanta min inason ta so kuma na aure ba na yaudara ba kuma ni ba malalaci ba ne baba idan kanaso ma kasa a yima bincike a kaina."
"To Alhamdulilah nayi farin cikin jin haka daga bakin ka dan daga nin kai yaron kirki ne, amma wanni hanzari ba gudu ba ni da na tambayi Arahamat ce man tayi babu komi a tsakani ku gashi kai kazomin da wani zance ya haka?"
"Et baba gaskiya ban fad'a mata cewa inason ta ba shiyasa kuma abinda yasa nayi haka dan kar tayi tunani sabida na taimaka mata ne yasa nace inason ta ko kuma ta fassara zancan da wata manufa, shiyasa na zabi har sai nazo maka da zancan tunkun na dalilin da yasa na mata wayo kan cewa ta nuna min gida su idan sai nazo na karb'i sauran canjin, a zahirin gaskiya ba karb'ar kud'in nazo ba ganika na kuma na fad'a maka manufata a kanta tunda nidai tun ranar dana bata kud'in nan manta dasu sabida ni gabad'aya na bata ba wai don ta mayar min da canji bane, dan Allah baba ina neman alfarma da a taimaka a bani auren Arahamat." Sadisu ya fad'a ba tare da ya d'ago da kansa ba.
Wani farin ciki ne ya mamaye Abbu sabida Allah kad'ai yasan yanda yake fatan Allah ya kawowa Arahamat miji na gari tayi aure ko dan ta futa da uk'uba Ufadi gashi da gani alamu wanan yaron mutuman kirki ne, sai dai Abbu bai nuna tsanani farin cikin da yake cikin sabida ma ka Sadisu yayi tunani ko an gaji da zaman ta a gidan ne alhali ba haka bane.
Abbu ya fad'ad'a murmushin yace "Gaskiya nayi farin ciki sosai da jin haka, amma miye sunan ka kai d'an waye kuma ina ne gidan ku a gari nan miye kuma sana'ar ka? kasan Yanada kyau nasan asalinka da halinka da abubuwan da baza'a rasaba na rayuwa tunda zancan aure fah babban abune ko ba gaskiya ba?"
"D'an murmushi yayi har kansa na duk'e yace "Hakane baba, da farko dai ni sunana Sadisu Asmane Sanga mahaifina cikaken d'an asalin garin Mali ne can ne garin su na iyaye da kakani dagin sa duka suna can, nima can aka haifeni ni da dangina baki d'aya mahaifiyata cikaka 'yar Niger ce haifafa garin zinder, yanzu ma a cikin garin Niamey muke da zama sakamakon rasuwar mahaifina muka tataro muka baro Mali kuma muka dawo Niger inada yaye mata biyu da namiji guda nine k'arami a cikin kuma nine banyi aure ba, kuma karatu ne ya kawo ni cikin garin amma nan da wata biyu zan k'arasa na koma garin mu, sanan kamin na baro gida ina d'an tab'a kasuwanci idan na koma gida kuma da k'asuwancin zanci gaba."
"Masha Allah Sadisu naji tak'aitacan labarin ka, da alamu bakayi kama da mutuman banza ba dan haka indai ni ke bada auren Arahamat to nabaka ita duniya da lahira kuma abisa amana kaga dai ita marainiya ce kada ka cutar da ita sabida amana na baka ita idan kaci amana ta Allah zai saka mata ko dan maraicin ta, kuma itama buzuwace gaba da baya kamar yanda ka lura mahaifiyar ta rasu wajan haihuwa k'anwata, kuma su uku ne ga mahaifiyar su har nima sune k'adai gare ni duk fad'i duniyar nan banida kamar su sedai shi baban wan nasu tunda gomnati ya turasa karatu a Canada har inda yau ke kwana ban gara sashi a idona ba yau kimanin shekara hud'u kenan, yana raye ko ya koma ka mahalicin shi Allah kad'e yasani ita kuma k'anwartata tana Arlit gun yar uwar mahaifiyar su, sedai wani hanzari ba gudu ba, kaje kasami ita Arahamat d'in kanemi soyayar idan ta amince da haka taji tana sonka alhamdulilah idan kuma bata amince sedai kayi hakuri sabida bazan mata doli ba duk abinda takeso to nima shi nakeso."
Wani sihirtacen murmushi Sadisu ya saki sannan yace "Alhamdulilah baba nagode da karamci da kauna da aka nuna min nayi farin ciki mara misiltuwa baba Allah kara lafiya da nisan kwana kuma insha Allah za'a ga wan su da ikon Allah ya na a raye bai mutu ba da yarda ubangiji, in Allah yaso ya yarda idan har Arahamat ta amince da aure na baza ka taba nadamar bani ita da kayi ba da ikon Allah."
Seda ya kara sunne kai san yace "Baba idan son samu ne ina neman alfarma har in ta amince nan da wata biyu a d'aura mana aure kamin na koma sai mu koma tare da ita sabida yanzu ina fita daga nan zan kira mahaifiya ta na sanar mata insha Allah."
Abbu yace "To Sadisu wata biyu baiyi kusa?"